“Ku Girmama Waɗanda Suke Aiki Tuƙuru A Cikinku”
“Ku girmama waɗanda suke aiki tuƙuru a cikinku, kuma suke shugabanci a gareku cikin Ubangiji, suna kuma yi muku gargaɗi.” —1 TAS. 5:12, NW.
1, 2. (a) Mene ne yanayin ikilisiyar Tasalonika sa’ad da Bulus ya rubuta musu wasiƙarsa ta farko? (b) Mene ne Bulus ya ƙarfafa Tasalonikawa su yi?
KA YI tunani cewa kana cikin ikilisiyar Tasalonika a ƙarni na farko, ɗaya cikin ikilisiyar da aka fara kafawa a ƙasar Turai. Manzo Bulus ya ba da lokaci sosai yana ƙarfafa ’yan’uwan da suke wurin. Wataƙila ya naɗa dattawa su yi ja-gora, kamar yadda ya yi a sauran ikilisiyoyin. (A. M. 14:23) Amma bayan an kafa ikilisiyar, Yahudawa suka kwaso ’yan tawaye don su kori Bulus da Sila daga birnin. Wataƙila Kiristoci da suka rage sun ji kamar an yasar da su kuma sun ji tsoro.
2 Babu shakka, bayan da Bulus ya bar Tasalonika ya damu ƙwarai da sabuwar ikilisiyar. Ya yi ƙoƙari ya koma, amma “Shaitan ya hana” shi. Sai ya aike Timotawus ya je ya ƙarfafa ikilisiyar. (1 Tas. 2:18; 3:2) Sa’ad da Timotawus ya dawo da rahoto mai kyau, hakan ya sa Bulus ya rubuta wa Tasalonikawa wasiƙa. Ɗaya cikin abubuwan da Bulus ya ƙarfafa su su yi shi ne su riƙa ‘girmama waɗanda suke shugabanci a gare su.’—Karanta 1 Tasalonikawa 5:12, 13.
3. Waɗanne dalilai ne Kiristoci a Tasalonika suke da su na daraja dattawan sosai?
3 ’Yan’uwan da suke wa Kiristoci da ke Tasalonika ja-gora ba su ƙware ba kamar Bulus da kuma abokan wa’azinsa, kuma ba su manyanta ba kamar dattawan da ke Urushalima. Ballantana ma, bai kai shekara guda ba tun da aka kafa ikilisiyar! Duk da haka, waɗanda suke cikin ikilisiya suna da dalilin yin farin ciki don dattawa da suke “aiki tuƙuru” da “shugabanci” a ikilisiyar kuma suke wa ’yan’uwan “gargaɗi.” Hakika, suna da dalili mai kyau na “daraja dattawan sosai cikin ƙauna.” Wannan kashedi na su “kasance da salama da juna” ya biyo bayan roƙon da Bulus ya yi. Da a ce kana Tasalonika, da ka nuna godiya sosai ga ayyukan dattawan? Yaya kake ɗaukan “kyautai ga mutane” waɗanda Allah ya yi wa ikilisiya tanadinsu ta hanyar Kristi.—Afis. 4:8.
“Aiki Tuƙuru”
4, 5. Me ya sa aiki ne mai wuya ga dattawan zamanin Bulus su koyar da ikilisiyar, kuma me ya sa haka yake a yau?
4 Ta yaya dattawan Tasalonika suke “aiki tuƙuru,” bayan an aika Bulus da Sila zuwa birnin Biriya? Babu shakka, sun yi koyi da Bulus ta wajen yin amfani da Nassosi don su koyar da ikilisiyar. Za ka yi mamaki, ‘Shin Kiristoci da ke Tasalonika sun nuna godiya don Kalmar Allah?’ Ballantana ma, Littafi Mai Tsarki ya ce mutanen Biriya sun “fi mutanen Tasalonika darajar hali, . . . suna bin cikin littattafai kowacce rana.” (A. M. 17:11) An yi kwatancin ga dukan Tasalonikawa da Yahudawa ne ba ga Kiristoci ba. Waɗanda suka yi imani sun ‘karɓe maganar ba kamar ta mutane ba, amma kamar maganar Allah.’ (1 Tas. 2:13) Babu shakka, dattawan sun yi aiki tuƙuru don su kula da su a ruhaniya.
5 A yau, rukunin bawan nan mai aminci, mai hikima yana yi wa garken Allah tanadin “abincinsu a lotonsa?” (Mat. 24:45) Bisa ga ja-gorancin rukunin bawan, dattawan ikilisiyoyi suna aiki tuƙuru don su kula da ’yan’uwansu a ruhaniya. Waɗanda suke cikin ikilisiya suna iya samun littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da yawa, kuma akwai tanadi kamar su Watch Tower Publications Index da Watchtower Library a FAIFAN CD-ROM a wasu harsuna. Dattawa suna ɗaukan sa’o’i da yawa suna shirya jawabai don su amfani ’yan’uwan kuma su gamsar da bukatu na ruhaniya na ikilisiyar. Ka taɓa yin tunani a kan sa’o’in da dattawa suke yi don shirya jawabai na tarurrukan ikilisiya da manyan tarurruka da kuma taron gunduma?
6, 7. (a) Wanne misali ne dattawan Tasalonika suka koya daga Bulus? (b) Me ya sa zai iya kasancewa da ƙalubale ga dattawa su yi koyi da Bulus a yau?
6 Dattawan Tasalonika sun tuna da misali mai kyau da Bulus ya kafa wajen kula da garken. Sun yi hakan cikin ƙauna ba don an tilasta musu ba. Kamar yadda aka tattauna a talifin da ya gabata, Bulus ya “nuna taushin hali . . . , kamar yadda mai goyo ke kula da goyonta.” (Karanta 1 Tasalonikawa 2:7, 8; “Littafi Mai Tsarki.”) Ya ma kasance a shirye ‘ya ba da ransa’! Dattawa suna bukatar su kasance kamar shi, sa’ad da suke ziyarar ƙarfafawa.
7 Makiyaya Kirista a yau suna bukatar su yi koyi da Bulus ta wajen daraja garken. Wasu tumaki za su iya kasance marasa kirki da kuma fara’a. Duk da haka, dattawa suna ƙoƙari su nuna basira kuma su “sami nagarta” a cikinsu. (Mis. 16:20) Da yake dattawa ajizai ne, za su iya ƙoƙarta don ganin halaye masu kyau na kowane mutum. Duk da haka, yayin da yake ƙoƙari ya kasance da basira ga kowa, yana da kyau a yaba masa don ƙoƙarin da yake yi ya zama makiyayi mai kyau a ƙarƙashin Kristi.
8, 9. A waɗanne hanyoyi ne dattawa a yau suke “yin tsaro sabili da rayukan[mu]”?
8 Dukan mu muna da dalili na ‘sarayar da kai’ ga dattawa. Kamar yadda Bulus ya rubuta, “suna yin tsaro sabili da rayukan[mu].” (Ibran. 13:17) Wannan furucin ya tuna mana da makiyayi na zahiri da yake ƙin yin barci don ya kāre tumakinsa. Hakazalika, dattawa a yau suna sadaukar da barcinsu don su kula da waɗanda suke rashin lafiya na zahiri da na motsin rai da kuma na ruhaniya. Alal misali, ’yan’uwan da ke Kwamitin Hulɗa da Asibitoci suna tashi da dare a wasu lokatai don su kula da wani da ke ciwo. Duk da haka, muna godiya ga hidimarsu sa’ad da muke fuskantar irin wannan yanayin!
9 Dattawan da ke Kwamitin Gine-Gine na Yankin da kuma waɗanda ke kwamitin ba da kayan agaji suna aiki tuƙuru don taimaka wa ’yan’uwan. Ya kamata mu goyi bayansu sosai! Ka yi la’akari da kayan agaji da aka ba da bayan babban hadari mai ɓarna sosai mai suna Nargis da ya auko wa ƙasar Myanmar a shekara ta 2008. Don su isa ikilisiyar Bothingone da ke yankin Irrawaddy Delta inda hadarin ya yi tsanani sosai, rukunin ba da kayan agajin suka bi ta wuraren da gawawwaki suke ko’ina. Sa’ad da ’yan’uwa da ke yankin suka ga cewa mai kula da da’irarsu a dā yana cikin rukunin masu ba da kayan agaji da suka fara isa ƙauyen Bothingone, sai suka yi kuka suna cewa: “Duba! Mai kula da da’irarmu ne! Jehobah ya cece mu!” Shin kana nuna godiya don aiki tuƙuru da dattawa suke yi dare da rana? An naɗa wasu dattawa su yi hidima a matsayin kwamiti na musamman da suke kula da shari’a mai wuya. Waɗannan dattawa ba sa fahariya game da abin da suka cim ma, duk da haka waɗanda suke amfana daga hidimar suna godiya sosai.—Mat. 6:2-4.
10. Wanne aiki ne da dattawa suke yi ba a yawan lura da shi?
10 Dattawa da yawa kuma a yau suna da rubuce-rubucen da za su yi. Alal misali, mai tsara ayyukan rukunin dattawa yana shirya tsarin ayyuka na taro duk mako. Sakatare na ikilisiya yana harhaɗa rahotannin hidimar fage duk wata da kuma duk shekara. Mai kula da makaranta yana tunani sosai a kan tsarin ayyuka na makarantar. A kowanne watanni ana lissafa kuɗaɗen ikilisiya. Dattawa suna karanta wasiƙu daga ofishin reshe kuma suna amfani da umurnin da ke ciki don “ɗayantuwar ruhu” ta kasance. (Afis. 4:3, 13) Ƙoƙarce-ƙoƙarcen waɗannan dattawan yana sa “a yi abu duka da hankali bisa ga ƙa’ida kuma.”—1 Kor. 14:40.
‘Shugabanni a Gareku’
11, 12. Wane ne ke ja-gora a cikin ikilisiya, kuma mene ne yin hakan ya ƙunsa?
11 Bulus ya kwatanta dattawan Tasalonika masu aiki tuƙuru cewa su ‘shugabanni ne’ ga ikilisiyar. Kalmar nan a yare na asali tana nufin “tsaya a gaba” kuma za a iya fassara ta “yin ja-gora ko yin jagabanci.” (1 Tas. 5:12) Bulus ya ce waɗannan dattawan suna “aiki tuƙuru.” Yana magana ne game da dukan dattawan ikilisiya. A yau, yawancin dattawa suna tsayawa a gaba kuma su gudanar da tarurruka a cikin ikilisiya. Gyaran da aka yi kwanan nan na “mai tsara ayyukan rukunin dattawa” ya taimaka mana mu ɗauki dukan dattawa a matsayin rukuni ɗaya.
12 Yin “shugabanci” a cikin ikilisiya ba ya nufin koyarwa kawai. An yi amfani da irin wannan furucin a 1 Timotawus 3:4. Bulus ya ce ya kamata dattijo ya zama mutum da ke “mulkin nasa gida da kyau, ’ya’yansa suna cikin biyayya da hankali shimfiɗe sarai.” Furucin nan “mulki” ba ya nufin koyar da yaransa kaɗai ba amma yin ja-gora a cikin iyali kuma yaransa su kasance da “biyayya.” Hakika, dattawa suna yin ja-gora a cikin ikilisiya, kuma suna taimaka wa kowa ya yi biyayya ga Jehobah.—1 Tim. 3:5.
13. Me ya sa zai iya ɗaukan lokaci kafin a yanka shawara a taron dattawa?
13 Don su shugabanci garken da kyau, dattawa suna tattauna hanyar da ta dace na kula da ikilisiyar. Zai iya fi kasancewa da kyau idan dattijo ɗaya ya tsai da shawarar. Amma, bisa ga misalin hukumar mulki na ƙarni na farko, rukunin dattawa na zamanin mu suna tattauna batutuwa a sake, suna neman ja-gora daga Nassosi. Maƙasudinsu shi ne yin amfani da ƙa’idodin Nassosi wajen taimaka wa ikilisiyar. Hakan yana kasancewa da amfani idan kowane dattijo ya shirya don taronsu, yana bincika Nassosi da kuma umurnin da rukunin bawan nan mai aminci mai hikima ya bayar. Hakika, hakan yana ɗaukan lokaci sosai. Idan akwai ra’ayi dabam kamar yadda ya faru sa’ad da hukumar mulki na ƙarni na farko take tattauna batun kaciya, za a bukaci ƙarin lokaci da bincike don samun ra’ayi guda da ya jitu da Nassosi.—A. M. 15:2, 6, 7, 12-14, 28.
14. Kana godiya cewa rukunin dattawa suna aiki a matsayin rukuni ɗaya? Me ya sa kake jin hakan?
14 Mene ne zai iya faruwa idan wani dattijo ya nace cewa lallai sai an bi nasa ra’ayin ko kuma yana ƙoƙari ya ɗaukaka nasa ra’ayi? Ko kuma shin idan wani, kamar Diyoturifis na ƙarni na farko, yana jawo rigima? (3 Yoh. 9, 10) Babu shakka ikilisiyar gabaki ɗaya za ta sha wuya. Idan Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya saka rigima a ikilisiya ta ƙarni na farko, za mu iya tabbata cewa zai so ya saka rigima cikin ikilisiya a yau. Zai iya yin amfani da halin son kai na ’yan Adam, kamar ra’ayin zaman sanannu. Saboda haka, dattawa suna bukatar su kasance da tawali’u kuma su yi aiki tare cikin haɗin kai. Muna godiya sosai ga halin tawali’u na dattawa da suke da haɗin kai a matsayin rukuni ɗaya!
“Yi Muku Gargaɗi”
15. Mene ne muradin dattawa sa’ad da suke yi wa ɗan’uwa ko ’yar’uwa gargaɗi?
15 Bulus ya nanata wani aikin dattawa mai wuya amma mai muhimmanci: yi wa garken gargaɗi. Bulus ne kaɗai ya yi amfani da kalmar Helas da aka fassara “gargaɗi,” a Nassosin Helenanci na Kirista. Yana iya nufin ja wa mutum kunne sosai amma ban da yin magana da fushi. (A. M. 20:31; 2 Tas. 3:15) Alal misali, Bulus ya rubuta wa Korintiyawa: “Ina rubutun wannan ba domin in kunyatar da ku ba, amma domin in gargaɗar da ku, ku da ku ke ’ya’yana ƙaunatattu.” (1 Kor. 4:14) Ƙauna da kulawa ne ya sa ya ba da wannan gargaɗin.
16. Me ya kamata dattawa su tuna sa’ad da suke wa mutane gargaɗi?
16 Dattawa suna yin la’akari da yadda suke wa mutane gargaɗi. Suna ƙoƙari su yi koyi da Bulus ta kasancewa da kirki da ƙauna da kuma taimako. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:11, 12.) Hakika, dattawa suna ‘riƙe da amintaciyar magana, har da za su iya yin gargaɗi da sahihiyar koyarwa.’—Tit. 1:5-9.
17, 18. Me ya kamata ka tuna idan dattijo ya yi maka gargaɗi?
17 A bayyane yake cewa dattawa ba kamiltattu ba ne kuma za su iya faɗin wani abu da za su yi nadama a kai. (1 Sar. 8:46; Yaƙ. 3:8) Kuma dattawa sun san cewa gargaɗi ba ‘abin faranta zuciya ba ne, amma abin ban ciwo ne’ ga ’yan’uwa masu ruhaniya. (Ibran. 12:11) Saboda haka idan dattijo ya gargaɗi wani, wataƙila ya yi hakan ne bayan ya yi tunani da addu’a sosai a kan batun. Idan dattijo ya gargaɗe ka, kana godiya ga kulawarsa kuwa?
18 A ce kana da wani ciwo da ba a gano ainihin irinsa ba. Sai wani likita ya gano ciwon, amma ba ka yarda ba cewa kana da irin wannan ciwon. Shin za ka yi fushi da likitan? A’a! Ko da ya ce za a yi maka fiɗa, wataƙila za ka amince da hakan, tun da ka san cewa kai ne za ka amfana. Yadda likitan ya sanar maka da matsalar zai iya shafan tunanin ka sosai, amma shin za ka ƙyale hakan ya shafi shawarar da za ka tsai da? A’a. Hakazalika, kada ka ƙyale yadda aka ba ka gargaɗi ya hana ka sauraron waɗanda ƙila Jehobah da Yesu suke amfani da su don ka san yadda za ka iya samun ci gaba ko kāre kanka a ruhaniya.
Ka Nuna Godiya ga Tanadin Dattawa da Jehobah Ya Yi
19, 20. Ta yaya za ka iya nuna godiya don “kyautai ga mutane”?
19 Mene ne za ka yi idan ka karɓi kyauta da aka yi musamman domin ka? Shin za ka nuna godiyarka ta yin amfani da shi? “Kyautai ga mutane” tanadin da Jehobah ya yi maka ne ta Yesu Kristi. Hanya ɗaya da za ka nuna godiyarka ga wannan kyautai ita ce ta sauraron jawabai da dattawa suke ba da wa da kuma yin ƙoƙari ka yi amfani da bayanai da suka faɗa. Za ka kuma iya nuna godiya ta ba da kalamai masu ƙarfafawa a tarurruka. Ka goyi bayan aiki da dattawa suke ja-gora, kamar hidimar fage. Idan shawarar da wani dattijo ya ba ka ta amfane ka, zai yi kyau ka faɗa masa hakan. Ƙari ga hakan, zai yi kyau ka nuna godiya ga iyalin dattijon. Ka tuna cewa, iyalin dattijon tana sadaukar da lokacin da ya kamata ta kasance tare da shi don dattijon ya yi aiki tuƙuru a cikin ikilisiya.
20 Hakika, muna da dalilai da yawa na nuna godiya ga dattawa, waɗanda suke aiki tuƙuru a tsakaninmu, suna mana ja-gora da kuma gargaɗi. Waɗannan “kyautai ga mutane” tanadi mai kyau ne sosai daga Jehobah!
Ka Tuna?
• Waɗanne dalilai ne Kiristoci a Tasalonika suke da su na nuna godiya ga waɗanda suke shugabanci tsakaninsu?
• Ta yaya dattawa a cikin ikilisiyarku suke aiki tuƙuru domin ku?
• Ta yaya kake amfana daga dattawa da suke shugabanci a gare ka?
• Ya kamata ka tuna da me, sa’ad da dattijo ya gargaɗe ka?
[Hoto a shafi na 27]
Kana godiya ga hanyoyi da yawa da dattawa suke kiwo a cikin ikilisiya?