Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jl darasi na 15
  • Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?
  • Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Aka Tsara Ikilisiya
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • “Ku Yi Kiwon Garken Allah Wanda Ke Wurinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Ku Girmama Waɗanda Suke Aiki Tuƙuru A Cikinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
jl darasi na 15

DARASI NA 15

Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?

Wani dattijo yana tattaunawa da wasu ’yan’uwa a ikilisiya

Finland

Wani dattijo yana koyarwa a ikilisiya

Koyarwa

Wasu dattawa suna ƙarfafa ’yan ikiliyarsu

Ziyarar ƙarfafawa

Wani dattijo ya fita yin wa’azi a sarari

Yin wa’azi

Ba mu da limaman da ake biya albashi a ƙungiyarmu. A maimakon haka, kamar yadda aka yi a dā sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, muna da dattawan da suka cancanta, waɗanda aka naɗa don su “yi kiwon ikilisiyar Allah.” (Ayyukan Manzanni 20:28) Waɗannan dattawan mutane ne da suke da dangantaka mai kyau da Allah, kuma suna yi wa ikilisiya ja-gora ‘ba da tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta ba.’ (1 Bitrus 5:1-3) Wane aiki ne suke yi a madadin mu?

Suna kula da mu kuma suna kāre mu. Dattawa suna amfani da nassi su yi mana ja-gora kuma suna taimaka wa ikilisiya ta ci gaba da kusantar Jehobah. Domin sun san cewa Allah ne ya ba su hakkin kula da mutanensa, dattawa ba sa juya mu yadda suka ga dama, a maimakon haka, suna kula da mu kuma suna sa mu farin ciki. (2 Korintiyawa 1:24) Kamar yadda makiyayi yake kula sosai da tumakinsa, dattawa suna ƙoƙartawa su san kowane mutumin da ke cikin ikilisiya.

Suna koya mana yadda za mu yi nufin Allah. A kowane mako, dattawa suna ja-gorantar taron da ake yi a ikilisiya don su ƙarfafa bangaskiyarmu. (Ayyukan Manzanni 15:32) Saboda ƙwazonsu, suna kan gaba wajen yin wa’azi, suna fita wa’azi tare da mu kuma suna nuna mana hanyoyi dabam-dabam da za mu bi mu yi wa’azi.

Suna ƙarfafa kowanenmu. Domin su taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, dattawan da ke ikilisiyarmu suna iya tattaunawa da mu a gidanmu ko a Majami’ar Mulki ta wajen yin amfani da Nassi.—Yaƙub 5:14, 15.

Ƙari ga hidimar da suke yi a cikin ikilisiya, yawancin dattawan nan suna da aikin da suke yi, kuma suna bukatar su kula da iyalinsu, hakan yana bukatar lokacinsu da kuma kulawarsu. ’Yan’uwan nan da suke hidima da ƙwazo sun cancanci mu daraja su.—1 Tasalonikawa 5:12, 13.

  • Wane aiki ne dattawa suke yi a cikin ikilisiya?

  • A waɗanne hanyoyi ne dattawa suke nuna cewa suna kula da kowannenmu?

KA ƘARA BINCIKE

Waye ne ya cancanta ya yi wannan hidimar? Kana iya karanta 1 Timotawus 3:1-10, 12 da kuma Titus 1:5-9 don ka san abin da ake bukata kafin mutum ya zama dattijo ko bawa mai hidima.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba