Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/1 p. 10
  • Jehobah Ya Damu da Kai Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Damu da Kai Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • “Ya Ubangiji, . . . Ka San Ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Allah Yana So Ka Ƙulla Dangantaka da Shi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/1 p. 10

KA KUSACI ALLAH

Jehobah Ya Damu da Kai Kuwa?

Wata mata da ta ƙi yarda cewa Allah ya damu da ita ta ce: “Wani babban ƙalubale da nake ƙoƙarin shawo kansa domin in kusaci Allah shi ne ganin cewa ban da mutunci a gaban Allah.” Ka taɓa samun kanka a irin wannan yanayin? Idan haka ne, wataƙila ka taɓa yin tunani: ‘Shin, Jehobah ya damu da waɗanda suke bauta masa kuwa?’ Hakika! Akwai wani furucin da Yesu ya yi da ya tabbata mana cewa Allah ya damu da mu.—Ka karanta Yohanna 6:44.

Mun san cewa Yesu ya fi kowa sanin halin Jehobah, shin mene ne ya faɗa game da hakan? (Luka 10:22) Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” Ba za mu taɓa iya zama almajiran Yesu ko kuma bayin Jehobah ba idan Jehobah da kansa bai jawo mu ba. (2 Tasalonikawa 2:13) Idan muka fahimci abin da Yesu yake nufi, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya damu da mu sosai.

Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce Jehobah ne yake jawo mu? A yaren Hellanawa, ana amfani da wannan fi’ili “jawo,” wajen kwatanta yadda ake jan taru da ke cike da kifaye. (Yohanna 21:6, 11) Hakan yana nufin cewa Jehobah yana jawo mu kuma ya tilasta mana mu bauta masa ne? A’a. Jehobah ya ba mu ’yancin yin zaɓi, saboda haka, ba ya tilasta mana mu bauta masa. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Jehobah yana bincika biliyoyin zukatan mutane da ke cikin duniya don neman waɗanda suke da zuciyar kirki. (1 Labarbaru 28:9) Idan ya sami mai zuciyar kirki, sai ya yi wani abu mai ban sha’awa. Mene ne ke nan?

Jehobah yana jawo hankalin wanda yake da tawali’u, kamar ‘ƙaramin yaro.’ (Matta 18:3) Jehobah yana yin hakan a hanyoyi biyu, wato, ta saƙon bishara da ake wa’azinsa a faɗin duniya, da kuma ta ruhu mai tsarki. Idan Jehobah ya lura da zuciyar wani da ke son gaskiyar Littafi Mai Tsarki, sai ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya taimaka wa mutumin ya san gaskiya kuma ya soma amfani da ita a rayuwarsa. (1 Korintiyawa 2:11, 12) Idan ba da taimakon Allah ba, ba za mu taɓa iya zama ainihin almajiran Yesu ko kuma bayin Allah ba.

Jehobah ya ba mu ’yancin yin zaɓi, saboda haka, ba ya tilasta mana mu bauta masa

Shin, mene ne kalamin Yesu da ke Yohanna 6:44 yake koya mana game da Jehobah Allah? Jehobah yana jawo mutane wurinsa ne don ya ga cewa suna da zuciya mai kyau kuma don yana ƙaunar su. Sa’ad da matar da aka yi ƙaulinta a farkon wannan talifin ta fahimci hakan, ta sami ƙarfafa. Ta ce: “Babu gatan da ya kai zama mai bauta wa Jehobah. Kuma idan Jehobah ya zaɓe ni in zama baiwarsa, hakan ya nuna cewa ina da mutunci a gabansa.” Kai kuma fa? Ya kamata sanin cewa Jehobah ya damu da waɗanda suke bauta masa ya motsa ka kusace shi, ko ba haka ba?

Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Yuli

Ayyukan Manzanni 11-28

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba