Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 pp. 9-13
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ɓoyayyen Mutum na Zuciya”
  • Ku “Ƙallafa Zuciyarku” ga Kalmar Allah
  • ‘Ka Kafa Zuciyarka ga Biɗar Kalmar Allah’
  • ‘Ka Yi Ƙaunar Jehovah da Dukan Zuciyarka’
  • Ka Kiyaye Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 pp. 9-13

Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So

“Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina.”—ZABURA 51:10.

1, 2. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga zuciyarmu?

DOGO ne kuma mai kyan gani. Da ganinsa, ya burge annabi Sama’ila sosai har ya kai ga kammala cewa wannan ɗan farin Jesse ne Allah ya zaɓa ya zama sarki bayan Saul. Amma Jehovah ya ce: “Kada ka dubi fuskar [ɗan nan], ko kuwa tsawon jikinsa: gama na ƙi shi. . . . Gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zuciya.” Jehovah ya zaɓi autan Jesse, Dauda—“mutum gwargwadon zuciyarsa.”—1 Samu’ila 13:14; 16:7.

2 Allah zai iya sanin zuciyar mutum, yadda ya nuna daga baya: “Ni Ubangiji mai-bimbinin zuciya ne, ina gwada ciki, domin in sāka ma kowanne mutum bisa ga ayyukansa, bisa ga ’ya’yan aikinsa.” (Irmiya 17:10) Hakika, “Ubangiji yana auna zukata.” (Misalai 17:3) To, mecece zuciya da ke cikin mutum da Jehovah yake aunawa? Menene za mu yi don mu samu zuciya da yake so?

“Ɓoyayyen Mutum na Zuciya”

3, 4. A wace hanya ce musamman aka yi amfani da kalmar nan “zuciya” cikin Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misalai.

3 Kalmar nan “zuciya” ta bayyana kusan sau dubu a cikin Nassosi Masu Tsarki. Yawancin lokatai an yi amfani da ita a hanya ce ta alama. Alal misali, Jehovah ya gaya wa annabi Musa: “Ka yi magana da ’ya’yan Isra’ila, su ɗauki hadaya su kawo mini: za ka karɓi hadayata daga hannun kowane mutum wanda zuciyatasa ta nufe shi.” Kuma waɗanda suke ba da kyauta ‘dukan waɗanda zuciyarsu ta zuga su, suka zo.’ (Fitowa 25:2; 35:21) A bayyane, fanni ɗaya na zuciya ta alama motsawa ce—iko na ciki da ke motsa mu mu aikata abu. Zuciyarmu ta alama tana nuna yadda muke ji, sha’awarmu da kuma soyayya. Zuciya da za ta iya cika da fushi ko ta cika da tsoro, ta yi baƙin ciki sosai ko ta yi farin ciki. (Zabura 27:3; 39:3; Yohanna 16:22; Romawa 9:2) Za ta iya fahariya ko kuma tawali’u, ta yi ƙauna ko ƙiyayya.—Misalai 16:5; Matta 11:29; 1 Bitrus 1:22.

4 Saboda haka, sau da yawa ana haɗa “zuciya” da motsawa kuma da sosuwar zuciya, yayin nan kuma “azanci” game da tunani ne musamman. Haka za a fahimci waɗannan kalmomi yayin da sun bayyana cikin mahalli ɗaya cikin Nassosi. (Matta 22:37; Filibbiyawa 4:7) Amma zuciya da azanci ba sa jituwa. Alal misali, Musa ya aririce Isra’ila: “Ka ajiye a cikin zuciyarka, [ko “dole ka tuna cikin azancinka,” hasiya ta NW ] Ubangiji shi ne Allah.” (Kubawar Shari’a 4:39) Ga marubuta da suke ƙulli game da shi, Yesu ya ce: “Don me ku ke tunanin mugunta a cikin zukatanku?” (Matta 9:4) ‘Fahimi,’ “ilimi,” da kuma “tunani” za a iya haɗa su da zuciya. (1 Sarakuna 3:12; Misalai 15:14; Markus 2:6) Saboda haka, zuciya ta alama, za ta iya haɗawa da azanci—tunaninmu ko kuma fahiminmu.

5. Mecece zuciya ta alama ta ke nufi?

5 Bisa wani aikin bincike, zuciya ta zahiri tana nufin, “sashe na musamman a galibi, na ciki, saboda haka zuciya ta alama tana nufin mutum na ciki yana nuna kansa a ayyukansa dabam dabam, a sha’awarsa, soyayya, sosuwar zuciyarsa, ƙyashi, nufe-nufe, tunaninsa, fahiminsa, ƙagan zuci, hikimarsa, ilimi, gwaninta, imaninsa, da kuma amfani da dalilai, iya tunawa da kuma iya sanin abu.” Yana nuna abin da muke da gaske a ciki, “ɓoyayyen mutum na zuciya.” (1 Bitrus 3:4) Abin da Jehovah yake gani ke nan kuma ke aunawa. Saboda haka, Dauda ya yi addu’a: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitaccen ruhu daga cikina.” (Zabura 51:10) Yaya za mu samu zuciya mai tsabta?

Ku “Ƙallafa Zuciyarku” ga Kalmar Allah

6. Wane gargaɗi Musa ya ba Isra’ila yayin da suke zango a Filayen Mowab?

6 Yayin da yake yi wa ’ya’yan Isra’ila da suka taru a filayen Mowab kafin su shiga Ƙasar Alkawari gargaɗi, Musa ya ce: “Ku ƙallafa zuciyarku a kan dukan zantattukan da na shaida muku yau; da za ku umurci ’ya’yanku, su tsare dukan zantattukan wannan shari’a domin su aikata.” (Kubawar Shari’a 32:46) Isra’ilawa suna bukatar su “yi biyayya sosai.” (Knox) Sai dai sun saba sosai da umurnan Allah za su iya saka su cikin ’ya’yansu.—Kubawar Shari’a 6:6-8.

7. Menene ‘ƙallafa zuciyarmu’ ga Kalmar Allah ta ƙunsa?

7 Farilla ta musamman a samun zuciya mai tsabta, samun cikakken sani na nufin Allah ne da kuma nufe-nufensa. Da akwai tushe ɗaya ne kawai a samun wannan sani, hurariyar Kalmar Allah. (2 Timothawus 3:16, 17) Amma, ilimin kai kawai, ba zai taimaka mana mu samu zuciya da ke faranta wa Jehovah rai ba. Domin sani ya shafi abin da muke a ciki da gaske, dole mu ‘ƙallafa zuciyarmu,’ ko kuma “mu sa a zuci,” abin da muke koya. (Kubawar Shari’a 32:46, An American Translation) Yaya ake haka? Mai Zabura Dauda ya yi bayani: “Ina tuna da kwanakin dā; ina tunani da dukan al’amuranka: ina bimbini a kan ayyukan hannuwanka.”—Zabura 143:5.

8. Waɗanne tambayoyi za mu iya bimbini a kansu yayin da muke nazari?

8 A nuna godiya, mu ma ya kamata mu yi bimbini a kan ayyukan Jehovah. Yayin da muke karanta Littafi Mai Tsarki ko littattafan Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu yi bimbini a kan tambayoyi kamar su: ‘Menene wannan ya koya mini game da Jehovah? Waɗanne halayen Jehovah na gani aka nuna a nan? Menene wannan labarin ya koya mini game da abin da Jehovah yake so da abin da ba ya so? Menene sakamakon bin tafarki da Jehovah yake so in an gwada da bin wanda ba ya so? Ta yaya wannan labarin yake da dangantaka da abin da na sani?’

9. Ta yaya yin nazari da kanmu da yin bimbini suke da amfani?

9 Lisa ’yar shekara 32a ta yi bayani game da yadda ta soma ganin amfanin nazari mai ma’ana da yin bimbini: “Bayan na yi baftisma a shekara ta 1994, ina da ƙwazo cikin gaskiya na misalin shekaru biyu. Ina halarta dukan taron Kirista, ina ba da awoyi 30 zuwa 40 kowanne wata a hidimar fage, kuma ina tarayya da ’yan’uwa Kiristoci. Sai na soma janyewa. Na yi nisa sosai har na taka dokar Allah. Amma na komo kuma na shawarta na tsabtacce rayuwata. Na yi farin ciki cewa Jehovah ya amince da tuba ta kuma ya karɓe ni! Sau da yawa ina yin bimbini: ‘Me ya sa na janye?’ Amsar da ke zuwa zuciyata ita ce, domin na ƙyale nazari mai ma’ana da yin bimbini. Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba ta shiga zuciyata ba. Daga nan zuwa gaba, nazari da kaina da yin bimbini koyaushe suka zama sashe na musamman a rayuwa ta.” Yayin da muka ƙaru a saninmu na Jehovah, da Ɗansa, da kuma Kalmarsa, yana da muhimmanci mu ba da lokaci don yin bimbini mai ma’ana!

10. Me ya sa take da gaggawa mu keɓe lokaci don nazari da kanmu da kuma yin bimbini?

10 A cikin wannan duniya da muka taƙura, samun lokaci don nazari da yin bimbini abu ne mai wuya. Amma, Kiristoci a yau suna tsaye a bakin Ƙasar Alkawari mai ban al’ajabi—sabuwar duniya ta adalci ta Allah. (2 Bitrus 3:13) Aukuwa ta ban mamaki, kamar su halaka “Babila Babba” da farmaki daga “Gog, na ƙasar Magog” a kan mutanen Jehovah, na nan gaba. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2, 5, 15-17; Ezekiel 38:1-4, 14-16; 39:2) Abin da ke gaba zai iya gwada ƙaunarmu ga Jehovah. Da gaggawa yanzu mu rifta zarafi kuma mu ƙallafa zukatanmu ga Kalmar Allah!—Afisawa 5:15, 16.

‘Ka Kafa Zuciyarka ga Biɗar Kalmar Allah’

11. Ta yaya za a kamanta zuciyarmu da ƙasa?

11 Za a iya kamanta zuciya ta alama da ƙasa da za a iya shuka irin gaskiya. (Matta 13:18-23) Ana nome ƙasa ta zahiri don a tabbata cewa tsiron ya yi girma da kyau. Hakanan ma, ya kamata mu shirya zuciyarmu, don ta ƙara sauraron Kalmar Allah. Ezra firist “ya kafa zuciyatasa ga biɗar shari’ar Ubangiji, shi aikata.” (Ezra 7:10) Yaya za mu iya shirya zuciyarmu?

12. Me zai taimaka a shirya zuciya don yin nazari?

12 Shiri mafi kyau na zuciya in muna son mu bincika Kalmar Allah shi ne addu’a. Ana buɗe taron Kirista na masu bauta ta gaskiya da addu’a, kuma a rufe ta da addu’a. Ya dace mu soma kowanne sashe na nazarin Littafi Mai Tsarki da kanmu da addu’a kuma mu riƙe halin ibada lokacin da muke nazari!

13. Don mu samu zuciya da Jehovah yake so, menene dole za mu yi?

13 Dole a shirya zuciya ta alama ta kawar da nace wa ra’ayin da ake da shi dā. Shugabannan addinai na zamanin Yesu ba su so su yi haka ba. (Matta 13:15) A wata sassa, uwar Yesu Maryamu, ta tsai da abu “cikin zuciyarta” bisa gaskiya da ta ji. (Luka 2:19, 51) Ta zama almajira mai aminci ta Yesu. Lidiya ta Thyatira ta saurari Bulus, “Ubangiji kuma ya buɗe zuciyarta, da za ta lura.” Ita ma ta zama mai bi. (Ayukan Manzanni 16:14, 15) Kada mu ƙi ƙememe a kan namu ra’ayoyi ko kuma na koyarwan da muka daraja na addini. Maimako, bari mu kasance da yardan rai “Allah ya zama mai-gaskiya, ko da kowane mutum maƙaryaci ne.”—Romawa 3:4.

14. Yaya za mu shirya zuciyarmu mu saurara a taron Kirista?

14 Shirya zuciya don ta saurara a taron Kirista yana da muhimmanci. Abubuwa na raba hankali za su iya juya hankalinmu daga abin da ake faɗa. Abubuwa da aka faɗa za su kasance da iko kaɗan ne kawai a kanmu idan mun shagala a abubuwa da suka faru a ranar ko kuma mun damu game da abin da ke jiranmu gobe. Muna bukatar mu ƙuduri niyyar saurara kuma mu koya idan za mu amfana daga abin da aka faɗa. Za mu amfana sosai idan muka ƙudura niyyar mu fahimci nassosi da ake bayani a kansu da kuma ake fitowa da ma’ana da ke ciki!—Nehemiah 8:5-8, 12.

15. Ta yaya tawali’u yake taimaka mana mu iya koyo?

15 Yadda daɗa abubuwa da suka dace zai kyautata ƙasa ta zahiri, haka ne koyar tawali’u, yunwa ta ruhaniya, dogara, tsoron ibada, da ƙauna ga Allah za su ƙara kyautata zuciyarmu ta alama. Tawali’u na sa zuciya ta yi taushi, yana taimakonmu mu iya koyo. Jehovah ya ce wa Josiah Sarkin Yahudiya: “Tun da shi ke zuciyarka tana da taushi, ka kuwa ƙasƙantadda kanka gaban Ubangiji, sa’anda ka ji maganar da na faɗi . . . ka yi kuka a gabana kuma; ni na ji ka.” (2 Sarakuna 22:19) Josiah na da zuciya mai tawali’u kuma ta saurarawa. Tawali’u ya taimaki almajiran Yesu ‘marasa-karatu, talakawa’ su fahimci kuma su yi amfani da gaskiya ta ruhaniya da “masu-hikima da masu-fahimi” ba su fahimta ba. (Ayukan Manzanni 4:13; Luka 10:21) Bari mu “ƙasƙantadda kanmu a gaban Allahnmu” yayin da muke ƙoƙari mu samu zuciya da Jehovah yake so.—Ezra 8:21.

16. Me ya sa ake bukatar a gina marmari don abinci na ruhaniya?

16 Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-ladabi a ruhu.” (Matta 5:3) Ko da an ba mu iyawa ta ruhaniya, matsi daga wannan muguwar duniya ko kuma hali kamar ragonci zai iya rage sanin bukatarmu. (Matta 4:4) Dole mu gina marmari mai kyau na abinci na ruhaniya. Ko idan ma da farko ba ma jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki da nazari na kanmu, ta nacewa za mu iske cewa ilimi ‘zai yi daɗi ga ranmu,’ don mu iya ɗokin lokatan nazari.—Misalai 2:10, 11.

17. (a) Me ya sa Jehovah ya cancanci cikakkiyar dogararmu? (b) Ta yaya za mu koyi dogara ga Allah?

17 Sarki Sulemanu ya yi gargaɗi: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.” (Misalai 3:5) Zuciya da take dogara da Jehovah ta sani cewa ko menene Yake biɗa ko umurta ta wurin Kalmarsa koyaushe daidai ne. (Ishaya 48:17) Babu shakka Jehovah ya cancanci cikakkiyar dogararmu. Yana iya cika duk abubuwa da ya ƙudurta. (Ishaya 40:26, 29) Shi ya sa, sunansa a zahiri na nufin “Yakan Sa Ya Kasance,” wanda ke gina aminci a iyawarsa na cika abin da ya yi alkawarinsa! Shi “mai-adalci ne cikin dukan tasarrufinsa, mai-alheri ne cikin dukan ayyukansa.” (Zabura 145:17) Amma, don mu koyi dogara gare shi, muna bukatar mu ‘ɗanɗana, mu duba cewa Jehovah nagari ne’ ta yin amfani da abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu ta yin bimbini a kan amfani mai kyau da wannan yake kawowa.—Zabura 34:8.

18. Ta yaya tsoron Allah yake taimaka mana mu saurari ja-gorar Allah?

18 A nuna wani hali kuma da zai sa zuciyarmu ta saurari ja-gora ta Allah, Sulemanu ya ce: “Ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da mugunta.” (Misalai 3:7) Jehovah ya faɗi game da Isra’ila ta dā: “Da ma da wannan irin zuciya a cikinsu da za su ji tsorona, su kiyaye dukan dokokina kullum, domin su zauna lafiya, duk da ’ya’yansu har abada!” (Kubawar Shari’a 5:29) Hakika, waɗanda suke tsoron Allah suna biyayya da shi. Jehovah yana da iyawa na “ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi” kuma ya hori waɗanda suke masa rashin biyayya. (2 Labarbaru 16:9) Bari tsoron ɓata wa Allah rai ya sarrafa dukan ayyukanmu, tunaninmu, da kuma jiye-jiye.

‘Ka Yi Ƙaunar Jehovah da Dukan Zuciyarka’

19. Wane matsayi ƙauna take da shi a sa zuciyarmu ta saurari ja-gorar Jehovah?

19 Fiye da dukan sauran inganci, ƙauna da gaske tana sa zuciyarmu ta saurari ja-gorar Jehovah. Zuciya da take cike da ƙaunar Allah tana sa mutum ya so ya koyi abin da ke faranta wa Allah rai da abin da ke ɓata masa rai. (1 Yohanna 5:3) Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Bari mu zurfafa ƙaunarmu ga Allah ta sa ya zama halinmu mu yi bimbini a kan nagartansa, ta yin magana da shi kullum shi abokinmu ne na kud da kud, da kuma ta yin ɗokiyar gaya wa wasu game da shi.

20. Ta yaya za mu samu zuciya da Jehovah yake so?

20 A maimaitawa: Samun zuciya da Jehovah yake so ya ƙunshi yarda da cewa Kalmar Allah ta shafi abin da muke a ciki, ɓoyayyen mutum na zuciya. Nazari mai ma’ana na Nassosi da kanmu da yin bimbini mai kyau dole ne. Hanya mafi kyau na cim ma wannan shi ne, shirya zuciya—zuciya da ba ta riƙe ra’ayin da ake da shi dā, wadda take cike da halaye da za su iya sa mu iya koyarwa! Hakika, da taimakon Jehovah, za a samu zuciya mai kyau. Amma waɗanne matakai za mu iya ɗauka don mu tsare zuciyarmu?

[Hasiya]

a An sake sunan.

Yaya Za Ka Amsa?

• Mecece zuciya ta alama da Jehovah yake aunawa?

• Ta yaya za mu ‘ƙallafa zukatanmu’ ga Kalmar Allah?

• Ta yaya ya kamata mu shirya zuciyarmu mu biɗi Kalmar Allah?

• Bayan ka yi nazarin wannan talifin, menene ka motsa za ka yi?

[Hoto a shafi na 9]

Dauda cikin godiya ya yi bimbini a kan abubuwa ta ruhaniya. Kana yin haka?

[Hotuna a shafi na 10]

Ka shirya zuciyarka kafin ka yi nazarin Kalmar Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba