Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/15 pp. 8-12
  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SUNA BUKATAR SU BINCIKA ZUCIYARSU?
  • “ZUCIYA WADDA ZA TA SAN” JEHOBAH A YAU
  • SAMUN “ZUCIYA” DA KE SON TA SAN ALLAH DA KUMA CI GABA DA YIN HAKAN
  • Kana da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Kiyaye Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/15 pp. 8-12

Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?

“In ba su zuciya wadda za ta san ni, su sani ni ne Ubangiji; za su zama mutanena.”—IRM. 24:7.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Yahudawa da yawa a zamanin Irmiya suka zama ‘marasa-kāciya a zuci’?

  • Me ya sa yake da muhimmanci kowannenmu ya bincika zuciyarsa?

  • Ta yaya za mu kasance da “zuciya wadda za ta san” Jehobah?

1, 2. Me ya sa wasu mutane suke son ɓaure?

KA TAƁA cin ɓaure kuwa? ’Ya’yan itace ne da Isra’ilawa suke ci sosai a zamanin dā. (Nah. 3:12; Luk 13:6-9) A yau, ana shuka ɓaure a ƙasashe da yawa, kuma yana da sinadarai masu amfani a jiki. Wasu ma sun ce yana taimaka wa zuciya.

2 Jehobah ya taɓa kwatanta zuciya da ɓaure. Ba amfanin ɓaure a jiki yake bayyanawa ba, domin yana magana ne game da zuciya ta alama. Abin da ya faɗa zai amfane mu da kuma ’yan’uwanmu. Yayin da muke tattauna abin da ya faɗa, ka yi tunanin darussan za mu koya a matsayin Kiristoci.

3. Mene ne kwandunan ’ya’yan itacen ɓaure da aka kwatanta a Irmiya sura 24 suke wakilta?

3 Bari mu yi la’akari da wani abin da Allah ya faɗa a zamanin annabi Irmiya game da ɓaure. A shekara ta 617 kafin zamaninmu, Yahudawa suna yin abubuwan da Jehobah ya tsana. Allah ya nuna abin da zai faru nan gaba ta wurin wahayi. Ya kwatanta kwandunan ’ya’yan itacen ɓaure biyu waɗanda suke wakiltar rukuni biyu. ’Ya’yan itacen ɓaure da ke cikin kwando ɗaya suna da “kyau ƙwarai,” amma waɗanda suke cikin ɗayan kwandon ‘munana ne ƙwarai.’ (Karanta Irmiya 24:1-3.) Munanan ’ya’yan itacen ɓaure suna wakiltar Sarki Zadakiya da mutanen da Sarki Nebukadnezzar da rundunarsa suka kai wa hari. Ezekiel da Daniyel da abokansa guda uku, da kuma wasu Yahudawa da ba da daɗewa ba za a kai su Babila kuma fa? Sune suke wakiltar ’ya’yan itacen ɓaure masu kyau. Wasu cikinsu za su koma su sake gina Urushalima da kuma haikalinta. Kuma da shigewar lokaci, hakan ya faru.—Irm. 24:8-10; 25:11, 12; 29:10.

4. Me ya sa abin da Allah ya faɗa game da ’ya’yan ɓaure masu kyau yake da ban ƙarfafa?

4 Jehobah ya ce game da waɗanda ’ya’yan itacen ɓaure masu kyau suke wakilta: “In ba su zuciya wadda za ta san ni, su sani ni ne Ubangiji; za su zama mutanena.” (Irm. 24:7) Wannan yana da ban ƙarfafa domin yana nufin cewa Allah yana son mu kasance da ‘zuciya wadda za ta san shi,’ wato, mu zama mutane da suke son su san shi kuma mu kasance cikin mutanensa. Ta yaya za mu yi hakan? Ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma aikata abin da muka koya. Kuma mu tuba mu daina abubuwa marasa kyau da muke yi. Bayan hakan, sai mu keɓe ranmu ga Allah kuma mu yi baftisma cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai tsarki. (Mat. 28:19, 20; A. M. 3:19) Shin ka ɗauki waɗannan matakan? Ko kuwa kana halartan taron Shaidun Jehobah a kai a kai don ka yi hakan?

5. An rubuta littafin Irmiya musamman game da waɗanne mutane?

5 Ko idan mun riga mu ɗauki waɗannan matakan, dole ne mu ci gaba da kasancewa da halayen kirki. Me ya sa? Za mu san amsar sa’ad da muka tattauna abin da Irmiya ya rubuta game da zuciya. Wasu surori cikin littafin Irmiya sun yi magana game da al’ummai da suke kusa da Yahuda, amma littafin ya fi mai da hankali ga al’ummar Yahuda sa’ad da sarakunanta guda biyar suke sarauta. (Irm. 1:15, 16) Irmiya ya rubuta game da mutanen da sun riga sun keɓe kansu ga Jehobah. Kakaninsu sun yarda su zama masu bauta wa Jehobah. (Fit. 19:3-8) A zamanin Irmiya, mutanen sun ce: “Mun zo wurinka; gama kai ne Ubangiji Allahnmu.” (Irm. 3:22) Amma, mene ne yanayin zuciyarsu?

SUNA BUKATAR SU BINCIKA ZUCIYARSU?

6. Me ya sa za mu so sanin abin da Allah ya faɗa game da zuciya?

6 Likitoci suna iya yin amfani da na’urori don su duba cikin jikinmu kuma su bincika ko zuciyarmu tana aiki da kyau. Amma, Jehobah zai iya sanin zuciyarmu ko kuma ainihin halinmu. Ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta? Ni Ubangiji mai-bimbinin zuciya ne . . . domin in sāka ma kowanne mutum bisa ga ayyukansa, bisa ga ’ya’yan aikinsa.” (Irm. 17:9, 10) Allah ya san bukatunmu da tunaninmu da yadda muke ji. Ya kuma san halinmu da abin da muke son mu yi da rayuwarmu. Allah yana iya bincika zuciyarka, amma kai ma kana bukatar ka yi ƙoƙari ka bincika abin da ke cikin zuciyarka.

7. Ta yaya Irmiya ya kwatanta zuciyar yawancin Yahudawa na zamaninsa?

7 Don mu bincika zuciyarmu, ya kamata mu yi tunanin yadda Jehobah ya ga zuciyar Yahudawa na zamanin Irmiya. Ga amsar da Irmiya ya ba da: ‘Dukan gidan Isra’ila kuma marasa-kāciya ne a zuci.’ Wannan ba ya nufin kaciya da Yahudawa maza suke yi, domin ya ce: ‘Ga shi, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, inda zan hori dukan masu-kāciya cikin rashin kāciyarsu.’ Hakan ya nuna cewa Yahudawa maza masu kaciya su ma “marasa-kāciya ne a zuci.” (Irm. 9:25, 26) To, mene ne wannan kalamin yake nufi?

8, 9. Mene ne yawancin Yahudawa suke bukatar su yi da zuciyarsu?

8 Allah ya gaya wa Yahudawa abin da suke bukatar su yi, kuma wannan ya taimaka mana mu fahimci abin da wannan kalami ‘marasa-kāciya a zuci’ yake nufi. Ya gaya musu: ‘Ku kawasda lobar zuciyarku, ku mazajen Yahuda, da ku mazaunan Urushalima: domin kada fushina ya fito . . . sabili da muguntar ayyukanku.’ Sun yi wa Jehobah rashin biyayya domin muguntar zuciyarsu. (Karanta Markus 7:20-23.) Sun yi tawaye kuma sun ƙi su tuba. Zuciyarsu, har da muradinsu da ra’ayinsu, sun ɓata wa Jehobah rai. (Karanta Irmiya 5:23, 24; 7:24-26.) Allah ya gaya musu cewa: “Ku kaciye kanku ga Ubangiji, ku kawar da lobar zuciyarku.”—Irm. 4:4; 18:11, 12.

9 A alamance, Yahudawa da ke zamanin Irmiya suna bukatar a yi wa zuciyarsu fiɗa. Isra’ilawa da ke zamanin Musa suna da irin wannan matsala. (K. Sha 10:16; 30:6) Ta yaya Yahudawa za su ‘kawar da lobar zuciyarsu’? Za su yi hakan ta wajen kawar da tunani da sha’awoyi ko kuma muradi da ke sa su ƙi yin biyayya ga dokokin Jehobah.—A. M. 7:51.

“ZUCIYA WADDA ZA TA SAN” JEHOBAH A YAU

10. Ta yaya Dauda ya bincika zuciyarsa ta alama, kuma ta yaya za mu yi koyi da misalinsa?

10 Ya kamata mu yi godiya cewa Allah yana taimaka mana mu fahimci zuciya ta alama. A matsayin bayin Jehobah, shin ya dace mu riƙa damuwa game da zuciyarmu ne? A cikin ikilisiyoyi da yawa, yawancin mutane suna bauta wa Jehobah da aminci kuma suna da halin kirki. Su ba munanan ’ya’yan itacen ɓaure ba ne, amma ya kamata mu tuna cewa Dauda ma ya ce: ‘Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina.’—Zab. 17:3; 139:23, 24.

11, 12. (a) Me ya sa kowannenmu yake bukatar ya bincika zuciyarsa? (b)  Mene ne Allah ba zai yi ba?

11 Jehobah yana son kowannenmu ya san shi, wato, ya amince da mu kuma mu ci gaba da yin hakan. Irmiya ya ce Jehobah yana bincika masu adalci kuma yana ganin “ciki da zuciya.” (Irm. 20:12) Tun da dai Jehobah ma yana bincika zuciyar masu adalci, ya kamata mu ma mu bincika abin da ke cikin zuciyarmu. (Karanta Zabura 11:5.) Idan muka yi haka, za mu iya ganin wasu halaye ko nufe-nufe marasa kyau a cikin zuciyarmu da suke sa mu yi rashin biyayya. Mai yiwuwa, ba ma saurin yi wa Jehobah biyayya. Muna bukatar mu bincika zuciyarmu domin mu iya kawar da ayyuka marasa kyau. Waɗanne halaye marasa kyau ne za su iya kasancewa cikin zuciyarmu? Kuma ta yaya za mu iya yin canje-canjen da ake bukata?—Irm. 4:4.

12 Jehobah ya ce zai ba Isra’ilawa masu kama da ’ya’yan ɓaure masu-kyau “zuciya wadda za ta san” shi. Amma, bai ce zai tilasta musu su canja zuciyarsu ba. Hakan nan ma ba zai tilasta mana mu canja halayenmu ba. Su ma suna bukatar su san Jehobah, kuma ya kamata mu ma mu yi hakan.

13, 14. Ta yaya abin da ke cikin zuciyar mutum zai iya za ma masa illa?

13 Yesu ya ce: “Daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha.” (Mat. 15:19) Alal misali, idan mutum yana sha’awoyi marasa kyau a cikin zuciyarsa, zai iya yin zina ko fasikanci. Idan kuma ya ƙi tuba, zai rasa tagomashin Allah har abada. Amma, ko idan bai yi zunubi mai tsanani ba, sha’awoyi marasa kyau suna iya yin jijiya a cikin zuciyarsa. (Karanta Matta 5:27, 28.) Yana da muhimmanci mu tabbata cewa babu sha’awoyi marasa kyau a cikin zuciyarmu. Kana sha’awar wani ko wata a hanyar da da ba ta dace ba? Shin kana bukatar ka kawar da abin da ke cikin zuciyarka?

14 Haka nan ma, ɗan’uwa yana iya riƙe wani ɗan’uwa a zuciya, har ma ya fara tsanan sa. (Lev. 19:17) Hakika, yana bukata ya kawar da irin wannan tunanin daga cikin zuciyarsa.—Mat. 5:21, 22.

15, 16. (a) Ka ba da misalin yadda Kirista zai iya zama ‘marar-kāciya a zuci.’ (b) Me kake ganin ya sa Jehobah ba ya son mu kasance ‘marasa-kāciya a zuci’?

15 Yawancin Kiristoci ba su da irin waɗannan sha’awoyin a zuciyarsu. Duk da haka, Yesu ya yi magana game da “miyagun tunani.” Alal misali, za mu iya yin tunani cewa kasancewa da aminci ga iyalinmu ya fi kome muhimmanci. Hakika, ya dace Kiristoci su ƙaunaci danginsu maimakon su zama kamar mutanen duniya “marasa-ƙauna irin na tabi’a.” (2 Tim. 3:1, 3) Amma, muna iya ƙaunar iyalinmu a hanyar da ba ta dace ba. Mutane da yawa suna jin cewa “ɗan’uwa rabin jiki” ne. Sa’ad da aka ɓata wa danginsu rai, sukan goyi bayansu, kuma su yi kamar su ne aka yi wa laifi. ’Yan’uwan Dinah sun yi fushi sosai domin an yi lalata da ita. Sabili da haka, suka karkashe mutane da yawa. (Far. 34:13, 25-30) Mugun tunani ne ya sa Absalom ya kashe ɗan’uwansa Amnon. (2 Sam. 13:1-30) Hakika, “miyagun tunani” za su iya za ma mana lahani.

16 Kiristoci na gaskiya ba sa kisan kai. Amma, wasu sukan yi fushi sosai sa’ad da aka wulakanta wani a cikin iyalinsu ko kuma suna ganin cewa an yi hakan. To, yaya suke bi da wanda suke tunanin cewa ya yi musu laifi? Suna iya ƙin cuɗanya da shi, ko kuma su ƙi gayyatarsa gidansu. (Ibran. 13:1, 2) Amma, bai kamata Kiristoci masu ƙaunar ’yan’uwansu su yi haka ba. Jehobah ya san zuciyarmu. Idan ya ga cewa muna mugun tunani, zai ce mu ‘marasa-kāciya a zuci’ ne. (Irm. 9:25, 26) Amma, Jehobah ya ce: “Ku kawar da lobar zuciyarku.”—Irm. 4:4.

SAMUN “ZUCIYA” DA KE SON TA SAN ALLAH DA KUMA CI GABA DA YIN HAKAN

17. Ta yaya jin tsoron Jehobah zai taimaka mana mu yi canje-canje a zuciyarmu?

17 Sa’ad da ka bincika zuciyarka, za ka iya ganin cewa ba ka saurin biyayya ga umurnin Jehobah kamar yadda ya dace. Mai yiwuwa, za ka iya zama ‘marar-kāciya a zuci.’ Wataƙila kana jin tsoron irin tunanin da mutane za su yi game da kai. Ko kuma kana son ka zama sananne ko mai kuɗi sosai. Wasu lokatai za ka iya yi taurin kai, ka ce kana son ka yi duk abin ka ga dama. Wasu ma sun ji hakan. (Irm. 7:24; 11:8) Irmiya ya rubuta cewa Yahudawa marasa aminci na zamaninsa, suna da “zuciyar ƙiyayya, da son tayarwa.” Ya daɗa cewa: “Ba su kuwa cewa cikin zuciyarsu, bari dai mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, shi da ke bada ruwa.” (Irm. 5:23, 24) Idan muna tsoron Jehobah, wato, muna daraja shi, hakan zai sa mu kawar da mugunta daga cikin zuciyarmu. Zai yi mana sauƙi mu yi canje-canje a zuciyarmu kuma mu yi duk abin da Jehobah ya ce mu yi.

18. Mene ne Jehobah ya ce zai yi wa waɗanda ke cikin sabon alkawari?

18 Idan muka ci gaba da ƙoƙartawa, Jehobah zai ba mu “zuciya wadda za ta san” shi. Ya ce zai yi hakan ga Kiristoci shafaffu da ke cikin sabon alkawari: “Zan sa shari’ata a cikinsu, zan rubuta ta a cikin zuciyarsu, in zama Allahnsu, su zama mutanena.” Ya daɗa cewa: “Ba kuwa za su ƙara koya wa juna, mutum da maƙwabcinsa, ɗan’uwa da ɗan’uwansa, su ce, ku san Ubangiji; gama dukansu za su san ni, tun daga ƙaraminsu har zuwa babba . . . gama zan gafarta muguntarsu, ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.”—Irm. 31:31-34.a

19. Wane bege ne Kiristoci na gaskiya suke da shi??

19 Muna ɗokin ganin cikawar alkawuran da Allah ya yi mana. Ya kamata dukanmu mu so mu san Jehobah kuma mu kasance cikin mutanensa. Za mu iya sanin Jehobah har abada idan ya gafarta mana zunubanmu bisa hadayar Kristi. Tun da mun san cewa za a gafarta mana zunubanmu, ya kamata mu ma mu so gafartawa wasu nasu, ko da yin hakan yana da wuya. Ya kamata mu yi ƙoƙari mu kawar da fushi ko kuma ƙiyayya. Hakan zai taimaka mana mu nuna cewa muna son mu bauta wa Jehobah kuma muna son mu san shi sosai. Za mu zama kamar waɗanda Jehobah ya ce game da su: “Za ku neme ni, ku same ni kuma, lokacin da ku ke nemana da zuciya ɗaya, zan samu gareku.”—Irm. 29:13, 14.

a An bayyana wannan sabon alkawari a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2012 shafuffuka na 26-30.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba