DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 22-24
Kana da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
Jehobah ya kwatanta mutane da ɓaure
24:5
Yahudawa masu aminci da suke zaman bauta a Babila suna kama da ɓaure mai kyau
24:8
Sarki Zedekiya da kuma wasu da suka yi abubuwa marasa kyau suna kama da ɓaure marar kyau
Ta yaya zan kasance da “zuciya wadda za ta san” Jehobah?
24:7
Idan muna nazarin Kalmar Allah da kuma bin umurninsa, Jehobah zai ba mu “zuciya wadda za ta san” shi
Wajibi ne mu riƙa bincika zuciyarmu kuma mu daina duk wani halin da zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah