Ka Kusaci Allah
“Ya Ubangiji, . . . Ka San Ni”
“BABU baƙin cikin da ya fi sanin cewa babu wanda ya damu da kai ko kuma ya fahimce ka.”a Hakan ya taɓa faruwa da kai? Ka taɓa jin cewa babu wanda ya fahimci yanayin da kake ciki balle ma yadda kake ji? Idan haka ne, wannan batun zai iya ƙarfafa ka: Jehobah yana kula sosai da masu bauta masa kuma yana lura da dukan abubuwan da ke faruwa da su yayin da suke hidimominsu na yau da kullum. Kalmomin Dauda a littafin Zabura 139 sun tabbatar da wannan gaskiyar.
Domin yana da gaba gaɗin cewa Allah yana ƙaunarsa, Dauda ya ce: “Ya Ubangiji, kā bincike ni, kā kuwa san ni.” (Aya ta 1) Dauda ya yi amfani da kyakkyawan kwatanci a nan. Aikatau na Ibrananci da aka fassara “bincike” yana iya nufin haƙar ma’adanai (Ayuba 28:3), bincika ƙasa (Alƙalawa 18:2), ko kuma bincika shaidun da aka gabatar a shari’a (Kubawar shari’a 13:14). Hakika, Jehobah ya san mu ciki da waje kamar yana bincika duk wani fasalin rayuwarmu. Ta wajen yin amfani da wakilin sunan nan “ni,” Dauda ya koya mana cewa Jehobah yana kula da kowanne cikin bayinsa. Yana bincika su ciki da waje har ya san kowannen su.
Dauda ya ƙara bayyana zurfin binciken da Allah yake yi, ya ce: “Zamana da tashina ka sani, ka fahimci tunanina tun daga nesa.” (Aya ta 2) Wato, Jehobah yana “nesa,” yana zaune a sama. Duk da haka, ya san sa’ad da muka zauna, mai yiwuwa bayan mun yini muna aiki da kuma sa’ad da muka tashi da safe muka fita hidimominmu na yau da kullum. Ya kuma san tunaninmu da sha’awarmu da kuma manufofinmu. Shin, Dauda ya ji kamar ransa na cikin haɗari ne domin Jehobah yana yi masa irin wannan bincike? Akasin haka, ya yi farin cikin cewa ana yi masa irin wannan binciken. (Ayoyi 23, 24) Me ya sa?
Dauda ya san cewa Jehobah yana da manufa mai kyau na bincika masu bauta masa. Dauda ya yi nuni ga wannan manufa sa’ad da ya rubuta: “Kā bincike tafarkina da kwanciyata, kā san dukan al’amurana.” (Aya ta 3) A kowace rana, Jehobah yana ganin ‘dukan al’amuranmu,’ wato, kurakuranmu da ayyukanmu masu kyau. Yana mai da hankali ne ga ayyukanmu marar kyau ko kuma masu kyau? Kalmar Ibrananci da aka fassara “bincike” za ta iya kasance a “rairaye” ko kuma “sheƙa,” kamar yadda manomi yake sheƙa ƙaiƙayi daga tsaba. Kalmar Ibrananci da aka fassara “fahimci” tana nufin “a ƙaunace.” Sa’ad da yake bincika ayyuka da kuma abubuwan da ke fita daga bakin masu bauta masa a kowace rana, Jehobah yana ɗaukan masu kyaun da tamani. Me ya sa? Yana ɗaukan ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na faranta masa rai da tamani.
Zabura 139 ta koya mana cewa Jehobah yana kula sosai da masu bauta masa. Yana bincika su kuma yana kula da su yayin da suke yin hidimominsu na yau da kullum. Ya san matsalolin da suke fuskanta, kuma ya fahimci baƙin cikin da suke ji a sakamakon waɗannan wahaloli. Za ka so ka bauta wa wannan Allahn mai nuna ƙauna? Idan amsar ka e ce, ka san cewa: Jehobah ba zai taɓa ‘manta da aikinka da ƙauna wadda ka nuna ga sunansa’ ba.—Ibraniyawa 6:10.
[Hasiya]
a An yi wannan ƙaulin ne daga kalmomin mawallafi Arthur H. Stainback