Allah Ya Fahimci Yanayinka
“Ya Ubangiji, kā bincike ni, kā kuwa san ni.”—ZABURA 139:1.
ABIN DA KE SA WASU SHAKKA: Mutane da yawa suna ganin kamar Allah yana ɗaukan ’yan Adam a matsayin masu zunubi kawai, wato mutane marasa tsarki da ba su cancanci ya lura da su ba. Wata mai suna Kendra, wadda take fama da ciwon baƙin ciki, ta ɗauka cewa tana da alhaki babba kuma saboda haka ba za ta iya bin ƙa’idodin Allah kamar yadda ya kamata ba. A sakamakon haka, ta ce, “Na daina yin addu’a.”
ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: Jehobah ba ya mai da hankali ga ajizancinka kawai, amma ya san ka ciki da waje. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ya san tabi’armu [‘abin da aka yi mu da shi,’ Littafi Mai Tsarki]; yakan tuna mu turɓaya ne.” Ƙari ga haka, ba ya biya mana “gwargwadon zunubanmu,” amma yakan gafarta mana da jin ƙai sosai idan muka tuba.—Zabura 103:10, 14.
Ka yi la’akari da misalin Dauda, sarkin Isra’ila da aka ambata a talifi na farko a wannan jerin talifofin. Sa’ad da Dauda yake addu’a ga Allah, ya ce: “Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu, . . . Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata.” (Zabura 139:16, 23) Babu shakka Dauda ya tabbata cewa ko da yake ya yi zunubi sosai, har masu tsanani, Jehobah yana ganin zuciyarsa kuma ya fahimci cewa ya tuba.
Jehobah ya fahimci yanayinka fiye da yadda duk wani ɗan Adam zai iya fahimta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum yana duban [‘kyan tsari,’ LMT], amma Ubangiji yana duban zuciya.” (1 Sama’ila 16:7) Allah ya san cewa gādo da yadda aka raine ka da mahallinka da kuma mutuntakarka ne suka sa ka kasance da halaye dabam-dabam da kake da su. Duk da cewa kakan yi kuskure, yana ganin ƙoƙarin da kake yi don ka zama mai halin kirki kuma yana yaba maka.
To, ta yaya Allah yake ƙarfafa ka tun da ya fahimci ‘ainihin mutumin da kake’?