‘Ƙirarmu Abin Al’ajabi Ne’
“Ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce.”—ZABURA 139:14.
1. Me ya sa yawancin mutane masu tunani suka yaba wa Allah domin abubuwa masu ban al’ajabi da ke duniya?
WANNAN duniyar tana cike da halittu masu ban al’ajabi. Ta yaya suka wanzu? Wasu sun gaskata cewa za a iya samun amsar ba tare da an ambaci Mahalicci mai hikima ba. Wasu kuma sun gaskata cewa rashin ambatar Mahalicci zai rage yadda za mu fahimci halitta. Sun gaskata cewa halittun duniya suna da wuyar fahimta, sun bambanta, kuma suna da ban al’ajabi fiye da yadda za a ce wai sun wanzu ne kawai haka nan. Ga yawancin mutane, har da wasu ’yan kimiyya, alamu sun nuna cewa sararin samaniya yana da Mahalicci mai hikima, iko, da rahama.a
2. Menene ya motsa Dauda ya yaba wa Jehobah?
2 Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya gaskata cewa Mahalicci ya cancanci yabo domin halittunsa masu ban al’ajabi. Ko da yake Dauda ya rayu ne kafin wannan zamani na kimiyya, ya lura cewa halittun Allah masu ban al’ajabi sun kewaye shi. Dauda ya duba yadda aka ƙera jikinsa wanda hakan ya ba shi mamaki game da yadda Allah ya yi halitta. “Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa,” ya rubuta. “Ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.”—Zabura 139:14.
3, 4. Me ya sa yake da muhimmanci kowanenmu ya yi bimbini sosai game da ayyukan Jehobah?
3 Dauda ya gaskata da hakan ne ta wajen yin bimbini sosai. A yau, darussan da ake koyarwa a makaranta da kuma kafofin labarai suna cike da hasashen da ke lalata bangaskiya game da tushen mutum. Idan muna son mu kasance da bangaskiya kamar Dauda, muna bukatar mu yi bimbini sosai. Yana da haɗari mu tsai da shawara bisa tunanin da wasu suke yi, musamman a batutuwa masu muhimmanci kamar wanzuwa da kuma matsayin Mahalicci.
4 Bugu da ƙari, yin bimbini a kan ayyukan Jehobah zai ƙarfafa ƙauna da godiyar da muke yi masa, kuma zai sa mu gaskata da alkawuransa na nan gaba. Hakan zai motsa mu mu san Jehobah sosai kuma mu bauta masa. Bari mu tattauna yadda ’yan kimiyya na zamani suka tabbatar da abin da Dauda ya kammala cewa ‘ƙirarmu abin al’ajabi ce.’
Yadda Muke Girma Yana da Ban Al’ajabi
5, 6. (a) Ta yaya ne mu duka muka soma rayuwa? (b) Wane matsayi ne ƙoda take cikawa?
5 “Gama kai ka sifanta kayan cikina [ƙoda]: Ka harhaɗa ni cikin cikin uwata.” (Zabura 139:13) Rayuwarmu ta soma ne da ƙwayar rai guda a cikin mahaifiyarmu da ba ta kai ɗigon da ke ƙarshen wannan jimlar ba. Wannan ƙaramar ƙwayar tana da wuyar fahimta, domin mahaɗa ce ta sinadarai! Tana girma da sauri. An riga an ƙera muhimman ɓangarorin jikinka bayan ka yi watanni biyu a cikin mahaifa. A cikinsu kuwa da ƙoda. A lokacin da aka haife ka, ƙodojinka suna shirye su tace jininka, su cire abubuwa marasa amfani da kuma ruwan da ba zai amfane jikinka ba, kuma su bar abubuwa masu amfani a jikinka. Ƙodojinka biyu, idan suna lafiya, suna tace ruwan da ke cikin jininka, kusan lita 5 a jikin babban mutum bayan kowane minti 45!
6 Ƙodojinka suna taimaka wa wajen bi da sinadarai da ke cikin jininka da kuma hawan jini. Wani aiki mai muhimmanci da ƙoda take yi shi ne, tana mai da Bitamin D zuwa wani irin bitamin da ke sa ɓargo ya bayar da jajayen ƙwayoyin jini. Babu shakka, shi ya sa mutane suke mamaki ƙwarai saboda irin aikin da ƙodoji suke yi!.”b
7, 8. (a) Ka kwatanta yadda jaririn da ba a haifa ba yake soma girma. (b) Ta wace hanya ce jaririn da ke girma ‘ake sifanta shi da gwaninta daga cikin zurfafan duniya’?
7 “Yanayina ba a ɓoye ya ke a gareka ba, Sa’anda aka yi ni a fakaice, Sa’anda aka sifanta ni da gwaninta daga cikin zurfafan duniya.” (Zabura 139:15) Ainihin ƙwayar halittar za ta rabu, kuma sababbin ƙwayoyin halittun suna ci gaba da rabuwa. Bayan haka ƙwayoyin halittun za su soma rarrabuwa su zama jijiyoyi, tsoka, fata, da sauransu. Waɗannan ƙwayoyin halittu iri ɗaya suna haɗuwa su zama tsoka daga baya kuma su zama ɓangarori na jiki. Alal misali, bayan makonni uku da aka ɗauki cikinka, ka soma zama ƙwarangwal. A lokacin da ka kai sati bakwai a ciki, kana da tsawon kusan inci ɗaya, dukan ƙasusuwa 206 da za su kasance a jikinka sa’ad da ka girma za su bayyana ko da yake ba su da ƙwari.
8 Wannan tsarin na girma mai ban al’ajabi yana faruwa ne a cikin cikin mahaifiyarka da mutane ba za su iya gani ba, wanda kamar an ɓoye ne a cikin zurfafan duniya. Hakika, har yanzu mutane sun kasa sanin yawancin batutuwa game da yadda muke girma. Alal misali, menene ke sa wasu ƙwayoyin hali da ke cikin ƙwayar halitta suke rarrabuwa zuwa sashe dabam dabam na jiki? Wataƙila ’yan kimiyya za su san dalilin a nan gaba, amma kamar yadda Dauda ya ce, Mahaliccinmu, Jehobah, ya san dukan dalilan.
9, 10. Ta yaya ne duka bayanai game da tayi suke ‘rubuce’ a cikin ‘littafin’ Allah?
9 “Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu, waɗanda a ke sifantarsu yau da gobe, tun ba ko ɗaya a cikinsu ba.” (Zabura 139:16) Ƙwayar halittarka ta farko tana ƙunshe da dukan siffar jikinka. Wannan siffar ce take bi da yadda kake girma a cikin mahaifa har wata tara kafin a haife ka zuwa fiye da shekara ashirin sa’ad da ka girma ka zama mutum. A wannan lokacin, jikinka ya shaida yanayi dabam dabam a ƙarƙashin ja-gorancin bayanin da aka tsara a cikin wannan ƙwayar halitta ta ainihi.
10 Dauda bai da ilimin ƙwayoyin halitta da na halaye, domin ba shi da madubi mai ƙara girman abubuwa. Amma ya fahimci cewa yadda aka yi jikinsa ya nuna cewa an tsara shi ne. Ƙila Dauda yana da ɗan ilimi game da yadda tayi ke girma, shi ya sa ya ce kowane mataki zai faru ne kamar yadda aka tsara shi kuma a daidai lokacinsa. A cikin waƙa, ya kwatanta cewa wannan tsarin yana a ‘rubuce’ a cikin ‘littafin’ Allah.
11. Ta yaya kamaninmu ya kasance yadda yake?
11 A yau an sani cewa dukan abubuwan da ka gāda daga iyayenka da kuma kakanninka, kamar tsayi, kamanni, idanu da kalar gashi, da kuma halaye, duk sun yiwu ne domin ƙwayar halinka. Kowace ƙwayar halitta tana ƙunshe da dubban ƙwayoyin hali, kuma kowace ƙwayar hali ta ƙunshi sinadarai da ke ɗauke da kamanin mutum da ake kira DNA. An rubuta umurnin yadda jikinka zai girma a cikin DNA ɗinka. A duk lokacin da ƙwayar halittarka ta rabu don ta ƙera sababbin ƙwayoyin halitta ko ta sauya tsofaffin ƙwayoyin halitta, DNA ɗinka za ta ba da waɗannan umurnin, wanda hakan zai sa ka kasance a raye kuma kamaninka ya kasance yadda yake. Wannan fitaccen misali ne na iko da hikimar Mahaliccinmu da ke sama!
Hankalinmu Mai Ban Al’ajabi
12. Menene musamman ya bambanta mutane daga dabbobi?
12 “Ina misalin darajar tunaninka zuwa gareni, ya Allah! Ina misalin yawan jimlassu! Idan zan ƙididdige su, sun fi yashi yawa.” (Zabura 139:17, 18a) An halicci dabbobi a hanya mai ban al’ajabi, kuma wasu a cikinsu suna da iyawa da suka ɗara na mutane. Amma Allah ya ba mutane tunani da ya ɗara na dabbobi. “Ko da yake mun yi kama da sauran halittu, mun fita dabam a cikin dukan halittun duniya wajen iyawarmu na yin magana da tunani,” in ji wani littafi na ’yan kimiyya. “Kuma mun fita dabam ta wajen ɗokin da muke yi game da kanmu: Ta yaya ne aka tsara mu a zahiri?” Wannan ita ce tambayar da Dauda ya yi tunani a kai.
13. (a) Ta yaya ne Dauda ya yi bimbini a kan tunanin Allah? (b) Ta yaya ne za mu iya bin misalin Dauda?
13 Mafi muhimmanci, akasin dabbobi, muna iya yin bimbini game da al’amuran Allah.c Wannan kyauta ta musamman tana ɗaya daga cikin hanyoyin da aka halicce mu a “cikin surar Allah.” (Farawa 1:27) Dauda ya yi amfani da wannan kyautar sosai. Ya yi bimbini a kan alamun wanzuwar Allah da kuma halayensa masu kyau da suka bayyana a duniyar da take kewaye da shi. Dauda kuma yana da littattafai na farko na Nassosi Masu Tsarki, waɗanda suke ɗauke da abubuwan da Allah ya faɗa game da kansa da kuma ayyukansa. Waɗannan hurarrun rubutu sun taimaka wa Dauda ya fahimci tunanin Allah, halinsa, da kuma nufinsa. Yin bimbini a kan Nassosi, halitta, da kuma abubuwan da Allah ya yi ma shi ya motsa Dauda ya yaba wa Mahaliccinsa.
Abin da Bangaskiya ta Ƙunsa
14. Me ya sa ba ma bukatar mu san duka abubuwa game da Allah don mu ba da gaskiya a gare shi?
14 Yayin da Dauda yake tunani a kan halitta da Nassosi, ya kuma ƙara fahimtar cewa sanin Allah da iyawarsa sun fi ƙarfinsa. (Zabura 139:6) Mu ma haka. Ba za mu taɓa fahimtar dukan ayyukan halittun Allah ba. (Mai-Wa’azi 3:11; 8:17) Allah ya ‘bayyana’ isashen sani ta hanyar Nassosi da kuma halitta wanda zai sa masu biɗar gaskiya a kowane lokaci su yi imani bisa abin da aka bayyana.—Romawa 1:19, 20; Ibraniyawa 11:1, 3.
15. Ka kwatanta yadda aka haɗa bangaskiya da dangantakarmu da Allah.
15 Bangaskiya ta wuce gaskata cewa rai da kuma duniya sun fito ne daga Tushe mai hikima. Ta ƙunshi amincewa da Jehobah Allah, wanda yake son mu san shi kuma mu kasance da dangantaka mai kyau da shi. (Yaƙub 4:8) Muna iya kwatanta haka da yadda mutum yake amincewa da ubansa mai ƙauna. Idan wani mai sūka ya nuna shakka cewa babanka ba zai taimaka maka ba a lokacin wahala, wataƙila ba za ka iya tabbatar masa cewa ubanka zai taimaka ba. Amma idan ka riga ka shaida halayen babanka masu kyau, za ka kasance da tabbaci cewa ubanka ba zai taɓa yin watsi da kai ba. Hakazalika, sanin Jehobah ta wajen yin nazarin Nassosi, yin tunani a kan halittu, da kuma shaida taimakonsa ta wajen amsa addu’o’inmu, na motsa mu mu amince da shi. Hakan kuma yana sa mu so mu daɗa koyo game da shi kuma mu ɗaukaka shi har abada cikin ƙauna da ibada. Wannan shi ne manufa mafi muhimmanci da kowane mutum zai iya biɗa.—Afisawa 5:1, 2.
Ka Nemi Ja-gorar Mahaliccinmu!
16. Menene za mu iya koya daga dangantakar Dauda na kud da kud da Jehobah?
16 “Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina, ka bishe ni cikin tafarki na har abada.” (Zabura 139:23, 24) Dauda ya san cewa Jehobah ya riga ya san shi sosai, Mahaliccinsa ya san dukan tunaninsa, abin da ya ce, da abin da ya yi. (Zabura 139:1-12; Ibraniyawa 4:13) Irin wannan sanin da Allah yake da shi ya sa Dauda ya sami kwanciyar rai, kamar yadda ɗan ƙaramin yaro yake samun kwanciyar rai sa’ad da iyayensa masu ƙauna suka ɗauke shi. Dauda ya ɗauki dangantakarsa da Jehobah da tamani kuma ya yi iya ƙoƙarinsa ya manne mata ta wajen yin bimbini sosai a kan ayyukan Jehobah da kuma yi masa addu’a. Hakika, yawancin zaburar Dauda, har da Zabura ta 139 addu’o’i ne da aka yi cikin waƙa. Yin bimbini da kuma addu’a za su iya taimaka mana mu kusanci Jehobah.
17. (a) Me ya sa Dauda yake son Jehobah ya bincika zuciyarsa? (b) Ta yaya ne yadda muke amfani da ikon yin zaɓi zai shafi rayuwarmu?
17 Muna da ikon yin zaɓi domin an halicce mu a cikin surar Allah. Muna iya zaɓan yin abin da ke da kyau ko marar kyau. Wannan ’yancin na tare da ba da lissafi. Dauda ba ya son ya kasance da mugu. (Zabura 139:19-22) Yana son ya guje wa yin mugun kuskure. Saboda haka, sa’ad da ya yi tunani a kan yawan sanin Jehobah, cikin tawali’u Dauda ya roƙi Allah ya bincika tunaninsa kuma ya yi masa ja-gora zuwa hanyar rai. Mizanan Allah na ɗabi’a sun shafi kowa; saboda haka muna bukatar mu yi zaɓi mai kyau. Jehobah ya umurci dukanmu mu yi masa biyayya. Yin haka na sa mu sami tagomashinsa da kuma amfani mai yawa. (Yohanna 12:50; 1 Timothawus 4:8) Bin Jehobah a kowace rana yana taimaka mana mu sami kwanciyar rai, har ma a lokacin matsaloli.—Filibbiyawa 4:6, 7.
Mu bi Mahaliccinmu Mai Ban Al’ajabi!
18. Menene Dauda ya kammala daga tunaninsa na halitta?
18 Sa’ad da yake matashi, a yawancin lokaci Dauda yana waje yana kiwon dabbobi. A lokacin da dabbobin ke sunkuyar da kansu suna cin ciyawa, Dauda yana ɗaga kansa ya kalli sama. Sa’ad da dare ya yi, Dauda yana yin bimbini a kan girman sararin samaniya. “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa,” Dauda ya rubuta. “Yini yana magana da yini, kuma dare yana gwada ma dare sani.” (Zabura 19:1, 2) Dauda ya fahimci cewa yana bukatar ya biɗi kuma ya bi Wanda ya yi duka abubuwa masu ban al’ajabi. Mu ma muna bukatar mu yi haka.
19. Waɗanne darussa ne tsofaffi da matasa za su iya koya daga ‘ƙirarmu mai ban al’ajabi’?
19 Dauda ya zama misalin shawarar da ɗansa Sulemanu ya ba matasa: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma kwanakin ƙuruciyarka, . . . ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.” (Mai-Wa’azi 12:1, 13) Sa’ad da yake matashi, Dauda ya fahimci cewa ‘ƙirarsa abin al’ajabi ne.’ Yin rayuwa da ta jitu da wannan sanin ya sa ya sami amfani mai yawa a duka rayuwarsa. Idan dukanmu, tsofaffi da matasa muka yaba wa Mahaliccinmu kuma muka bauta masa, za mu ji daɗin rayuwarmu ta yanzu da ta gaba. Game da waɗanda suka kusanci Jehobah kuma suka bi hanyoyinsa na aminci, Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai: Za su kasance cike da romo da ɗanyantaka: Domin a bayana Ubangiji mai-yi daidai ne.” (Zabura 92:14, 15) Kuma za mu kasance da begen morar ayyuka masu ban al’ajabi na Mahaliccinmu har abada.
[Hasiya]
a Ka duba Awake! na 22 ga Yuni, 2004, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Ka duba “Your Kidneys—A Filter for Life,” da ke cikin Awake! 8 ga Agusta, 1997.
c Kalaman Dauda da ke Zabura 139:18b kamar suna nufin cewa idan ya zauna tun da safe har ya yi barci daddare yana ƙirga batutuwan Jehobah, idan ya tashi da safe, zai ga cewa yana da saura da yawa da zai ƙirga.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya ne yadda tayi ke girma ya nuna cewa ‘ƙirarmu abin al’ajabi ne’?
• Me ya sa ya kamata mu yi bimbini a kan batutuwan Jehobah?
• Ta yaya ne aka haɗa bangaskiya da dangantakarmu da Jehobah?
[Hotuna a shafi na 15]
Girman jariri a cikin ciki yana bin wani tsari ne da aka kafa
DNA
[Inda aka Dauko]
Tayi: Lennart Nilsson
[Hoto a shafi na 16]
Kamar yaran da suka amince da ubansa mai ƙauna, muna da tabbaci a Jehobah
[Hoto a shafi na 17]
Yin bimbini a kan ayyukan Jehobah ya motsa Dauda ya yaba masa