Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 11/15 pp. 3-7
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DAUDA YA ƊAUKAKA SUNAN JEHOBAH SOSAI
  • DAUDA YA DOGARA GA JEHOBAH
  • DAUDA YA SAN MA’ANAR ƘA’IDOJI
  • KA YI KOME BISA GA NUFIN ALLAH
  • ‘Yakin Na Jehobah Ne’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Bari Mu Ɗaukaka Sunan Jehobah Tare
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 11/15 pp. 3-7

‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’

“Ka koya mini in aika nufinka; gama kai ne Allahna.”—ZAB. 143:10.

MUHIMMAN DARUSSA

Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa Dauda ya yi la’akari da ra’ayin Jehobah?

Mene ne ya taimaka wa Dauda ya san nufin Allah?

Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah?

1, 2. Ta yaya za mu amfana idan muka san nufin Allah, yaya za mu amfana daga misalin Sarki Dauda?

A CE ka bi wata hanyar da ba ka taɓa bi ba dā. Sai ka kai wata mararraba, kuma ba ka san inda za ka bi ba. Mene ne za ka yi? Babu shakka, za ka tambayi wani da ya san wurin sosai don ya nuna maka hanyar. Hakazalika, idan muna son mu yanke shawara mai muhimmanci, ya kamata mu san ra’ayin Jehobah. Jehobah ya san kome, kuma neman taimakonsa zai sa mu yi tafiya a ‘hanyar’ da ta dace.—Isha. 30:21.

2 Dauda ya yi la’akari sosai da ra’ayin Jehobah a rayuwarsa. Hakan ya taimaka masa ya yi nufin Allah. Dauda mutum ne da yake bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa. Wannan talifin zai taimaka mana mu san abin da Dauda ya yi sa’ad da yake cikin mawuyacin yanayi.—1 Sar. 11:4.

DAUDA YA ƊAUKAKA SUNAN JEHOBAH SOSAI

3, 4. (a) Me ya ba Dauda gaba gaɗin yin yaƙi da Goliath? (b) Ta yaya Dauda ya ɗauki sunan Allah?

3 Sa’ad da Dauda yake matashi, akwai wani lokaci da ya je yaƙi da wani Bafilisti mai suna Goliath. Mene ne ya taimaki Dauda ya yi yaƙi da Goliath wanda tsayinsa kafa tara da rabi ne kuma yana ɗauke da makamai iri-iri? (1 Sam. 17:4) Dauda yana da gaba gaɗi da kuma imani ga Allah, amma ainihin abin da ya taimaka masa shi ne don yana daraja Jehobah da kuma sunansa mai girma. Dauda ya ce: “Wanene wannan Ba-philisti mara-kaciya fa da za ya zarge rundunan yaƙi na Allah mai-rai?”—1 Sam. 17:26.

4 Sa’ad da Dauda ya je gaban Goliath, sai ya ce: “Kai kana zuwa wurina da takobi, da māshi, da kunkeli: amma ni na zo wurinka cikin sunan Ubangiji mai-runduna, Allah na rundunan yaƙi na Isra’ila, wanda ka zarge.” (1 Sam. 17:45) Dauda ya dogara ga Jehobah. Sai ya kashe Goliath ta wajen ɗana masa dutse da majajjawarsa. Ba a wannan lokacin kaɗai ba ne Dauda ya dogara ga Jehobah kuma ya ɗaukaka sunansa, amma a rayuwarsa baki ɗaya. Kuma Dauda ya gaya wa Isra’ilawa su “yi fahariya” da sunan Jehobah.—Karanta 1 Labarbaru 16:8-10.

5. Ta yaya mutane a yau suke yin koyi da Goliath ta wajen raina sunan Allah?

5 Kana alfahari cewa Jehobah Allahnka ne? (Irm. 9:24) Wane mataki kake ɗauka sa’ad da maƙwabta ko abokan aiki da na makaranta ko danginka suka zagi Jehobah ko suka yi wa Shaidun Jehobah dariya? Shin kana kāre sunan Jehobah da kuma dogara da shi, kamar yadda Dauda ya yi sa’ad da Goliath ya zagi Jehobah? Gaskiya ne cewa akwai “lokacin shuru,” amma bai kamata mu ji kunyar zama Shaidun Jehobah da mabiyan Yesu ba. (M. Wa. 3:1, 7; Mar. 8:38) Sa’ad da muke tattauna da mutanen da ba sa daraja Jehobah ko saƙonmu, bai kamata mu yi musu baƙar magana ba. Amma, hakan ba ya nufin mu zama kamar Isra’ilawan da “suka yi fargaba, suka ji tsoro ƙwarai” sa’ad da suka ji abin da Goliath ya faɗa. (1 Sam. 17:11) Maimakon haka, ya kamata mu yi magana kai tsaye don mu kāre suna mai tsarki na Jehobah. Muradinmu shi ne mu taimaka wa mutane su san Jehobah. Shi ya sa muke yin amfani da Kalmar Allah don mu taimaki mutane su san dalilin da ya sa ya kamata su san Jehobah.—Yaƙ. 4:8.

6. Mene ne ainihin dalilin da ya sa Dauda ya yaƙe Goliath, me ya kamata ya fi muhimmanci a gare mu?

6 Akwai wani darasi kuma da za mu iya koya daga labarin Dauda da Goliath. Sa’ad da Dauda ya nufa wajen Goliath a guje, ya ce: “Me za a yi wa mutumin wanda ya kashe Ba-philistin nan, ya kawar da zargi daga wajen Isra’ila?” Sai mutanen suka faɗi abin da sarkin zai yi, suka ce: Duk “wanda ya kashe shi [Goliath], sarki za ya wadatar da shi da dukiya mai-yawa, shi ba shi ɗiyatasa.” (1 Sam. 17:25-27) Ba lada ba ce Dauda yake so, amma yana son ya ɗaukaka Allah na gaskiya. (Karanta 1 Sama’ila 17:46, 47.) Mene ne ya fi muhimmanci a gare mu? Shin mun fi ɗaukan kanmu da muhimmanci ko kuwa sunan Allah? Muna so ne mu zama masu wadata kuma mu zama sanannu a duniya? Ya kamata mu zama kamar Dauda wanda ya ce: “Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare.” (Zab. 34:3) Ya kamata mu dogara ga Allah, kuma mu fi ɗaukan sunansa da muhimmanci.—Mat. 6:9.

7. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da imani sosai a hidima ko da mutane ba sa son su saurare mu?

7 Domin Dauda ya yaƙi Goliath, yana bukatar ya kasance da imani ga Jehobah. Ya soma dogara ga Jehobah tun sa’ad da yake kiwo, kuma hakan ya ƙarfafa imaninsa. (1 Sam. 17:34-37) Mu ma muna bukatar gaba gaɗi don mu ci gaba da yin wa’azi, musamman idan mutane ba sa son su saurare mu. Za mu kasance da imani sosai, idan muna dogara ga Allah a dukan ayyukanmu na yau da kullum. Alal misali, sa’ad da muke cikin mota, za mu iya yi wa mutumin da ke zaune kusa da mu wa’azi. Kuma sa’ad da muke wa’azi gida-gida, ya kamata mu tattauna da mutanen da ke tafiya a kan titi.—A. M. 20:20, 21.

DAUDA YA DOGARA GA JEHOBAH

8, 9. Ta yaya Dauda ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah, sa’ad da Saul yake neman ya kashe shi?

8 Dauda ya nuna yana a shirye ya dogara ga Jehobah ta yadda ya bi da Sarki Saul. Kishi ya sa Saul ya jefa māshinsa har sau uku don ya kashe Dauda. Amma, Dauda ya kauce kuma bai rama ba. Daga baya, sai ya Dauda ya gudu. (1 Sam. 18:7-11; 19:10) Sai Saul ya ɗauki mazaje guda dubu uku zaɓaɓu daga cikin dukan Isra’ila, ya tafi neman Dauda a cikin jeji. (1 Sam. 24:2) Wata rana, sai Saul ya shiga cikin kwarin da Dauda da mazajensa suka ɓoye amma bai san cewa suna ciki ba. Mene ne Dauda zai yi? Shin zai kashe Saul wanda Allah ya riga ya ce Dauda zai zama sarki a madadinsa? (1 Sam. 16:1, 13) Mazajen Dauda sun ma shawarce shi ya kashe Saul. Amma, Dauda ya ce: “Ubangiji ya tsare ni in yi wa ubangijina wannan abu, shafaffe na Ubangiji ne kuwa, har da zan miƙa hannu a kansa, da shi ke shafaffe na Ubangiji ne shi.” (Karanta 1 Sama’ila 24:4-7.) Har lokacin, Saul sarki ne shafaffe. Jehobah bai tuɓe Saul ba tukun a matsayin sarki, saboda haka, Dauda ba ya son ya yi masa juyin mulki. Akasin haka, Dauda ya yanke shafin rigar Saul. Hakan ya nuna cewa Dauda bai so ya kashe Saul ba, ko da yake ya samu damar yin hakan.—1 Sam. 24:11.

9 A lokaci na ƙarshe da Dauda ya ga Saul, ya daraja shi tun da shafaffe ne. Dauda da Abishai sun je wurin da Saul yake, kuma sun tarar da shi yana barci. Abishai ya yi zato cewa Allah ne ya ba Dauda wannan zarafin don ya kashe Saul. Abishai ya ma so ya kashe Saul da māshi. Amma, Dauda bai yarda ba. (1 Sam. 26:8-11) Dauda bai kashe shafaffe na Allah ba, duk da abin da Abishai ya ce, domin ya dogara ga Jehobah.

10. Wane ƙalubale ne za mu iya fuskanta, kuma mene ne zai taimaka mana mu yi nufin Jehobah?

10 Hakazalika, za mu iya kasancewa a yanayin da mutane suke son mu yi nufinsu, maimakon na Jehobah. Ko kuma, za su so mu tsai da shawara kafin mu san ra’ayin Jehobah a kan batun. Abin da Abishai ya yi wa Dauda ke nan. Idan ba ma son mutane su rinjaye mu, muna bukatar mu san ra’ayin Jehobah kuma mu duƙufa cewa za mu yi nufinsa.

11. Wane darasi ne ka koya daga yadda Dauda ya sa yin nufin Allah kan gaba a rayuwarsa?

11 Dauda ya yi addu’a ga Jehobah, ya ce: “Ka koya mini in aika nufinka.” (Karanta Zabura 143:5, 8, 10.) Dauda bai dogara ga kansa ba, kuma bai yi abin da mutane suka ce ya yi ba. Maimakon haka, ya yi ɗokin Jehobah ya koyar da shi. Ya ce: “Ina tunani da dukan al’amuranka: ina bimbini a kan ayyukan hannuwanka.” Za mu iya yin koyi da Dauda ta wajen yin nazarin Nassosi da kuma yin bimbini a kan yadda Jehobah ya bi da mutane a zamanin dā.

DAUDA YA SAN MA’ANAR ƘA’IDOJI

12, 13. Me ya sa Dauda ya zubar da ruwan da sojojinsa uku suka ɗebo masa?

12 Dauda misali ne mai kyau na wanda ya bi ƙa’idodin da ke cikin kalmar Allah a rayuwarsa. Ga wani misali. Wata rana, Dauda ya ji ƙishirwa sosai kuma ya ce yana son ya sha ruwa “daga rijiyar Baitalahmi.” A lokacin, Filistiyawa ne suka mallaki wannan birnin. Sai sojojinsa uku suka shiga birnin a bakin ransu kuma suka ɗebo masa ruwa. Amma Dauda ya ƙi sha, kuma “ya tsiyaye shi a gaban Ubangiji.” Me ya sa? Dauda ya ce: “Allahna ya tsare ni da in yi wannan: zan sha jinin waɗannan mutane, da suka kasaidda ransu? gama da hatsarin ransu suka kawo shi.”—1 Laba. 11:15-19.

13 Dauda ya san cewa dokar Jehobah ta ce kada a ci jini, amma a zubar a ƙasa. Kuma ya fahimci abin da ya sa dokar ta ce a yi hakan. Dokar ta ce “ran nama yana cikin jini.” Amma fa, me ya sa Dauda ya ƙi sha tun da ruwa ne? Domin ya san ƙa’idar da ke tattare da dokar da aka bayar game da jini. Ya koyi cewa jini abu ne mai daraja a gaban Jehobah. Kuma ya san cewa waɗannan sojojin sun saka rayukansu cikin haɗari ne don su ɗebo ruwan. Saboda haka, Dauda ya zubar da ruwan a ƙasa.—Lev. 17:11; K. Sha 12:23, 24.

14. Mene ne ya taimaki Dauda ya tsai da shawara da suka faranta wa Jehobah rai?

14 Dauda ya ɗauki dokar Jehobah da muhimmanci sosai a rayuwarsa. Shi ya sa ya rera waƙa cewa: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, Hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” (Zab. 40:8) Dauda ya yi nazarin dokar Allah kuma ya yi bimbini a kanta. Ya amince cewa dokokin Jehobah suna ɗauke da hikima sosai. Hakan ne ya sa Dauda ya so ya bi Dokar da aka ba da ta hannun Musa da kuma ƙa’idodin dokar. Ya kamata mu ma mu yi bimbini bayan mun karanta Littafi Mai Tsarki. Ta hakan, za mu sa ƙa’idodin dokar su zama jikinmu, kuma za mu riƙa tsai da shawara da za su faranta wa Jehobah rai.

15. A wace hanya ce Sulemanu ya daina bin Dokokin Allah?

15 Jehobah ya albarkaci Sulemanu sosai. Amma, daga baya Sulemanu ya daina bin dokokin Allah. Ya ƙi bin dokar Jehobah da ta ce kada Sarkin Isra’ila “ya tara wa kansa mata.” (K. Sha 17:17) Sulemanu ya auri mata da yawa daga wasu ƙasashe. Sa’ad da ya tsufa, sai “matansa suka juyar da zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli.” Ko da wace hujja ce Sulemanu yake da shi, “ya yi abin da ke mugu a idanun Ubangiji, ba ya bi Ubangiji sosai ba, kamar yadda ubansa Dauda ya yi.” (1 Sar. 11:1-6) Yana da muhimmanci mu bi dokoki da kuma ƙa’idodin da muka koya daga Kalmar Allah. Alal misali, sa’ad da muke son mu yi aure.

16. Wane darasi za mu koya daga umurnin da Jehobah ya ba da cewa mu yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai?

16 Me ya kamata mu yi idan wani da ba ya bauta wa Jehobah ya ce yana sonmu? Za mu yi kamar Dauda ko kuwa Sulemanu? Jehobah ya ce bayinsa su yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Hakan yana nufin cewa idan Kirista da ya yi baftisma yana son ya yi aure, ya auri Kiristan da ta yi baftisma. Wannan ayar ta nuna cewa Jehobah ba ya son mu auri mutumin da bai yi baftisma ba, ko kuma mu fita zance da shi ko ita.

17. Mene ne zai taimaka mana mu ƙi kallon hotunan batsa?

17 Yadda Dauda ya nemi taimakon Jehobah da dukan zuciyarsa zai iya taimaka mana mu ƙi kallon hotunan batsa. Ka karanta ayoyin da ke gaba, ka yi la’akari da ƙa’idodin da ke cikinsu, kuma ka ga ko za ka iya fahimtar yadda Jehobah yake ji game da hotunan batsa. (Karanta Zabura 119:37; Matta 5:28, 29; Kolosiyawa 3:5.) Yin tunani a kan ƙa’idodin masu muhimmanci na Jehobah za su taimaka mana mu ƙi kallon batsa.

KA YI KOME BISA GA NUFIN ALLAH

18, 19. (a) Ko da Dauda ajizi ne, mene ne ya taimaka masa ya ci gaba da bauta wa Jehobah? (b) Mene ne ƙudurinka?

18 Duk da cewa Dauda ya kafa mana misalai masu kyau, ya yi zunubai masu tsanani da yawa. (2 Sam. 11:2-4, 14, 15, 22-27; 1 Laba. 21:1, 7) Amma, ya tuba daga dukan zunuban da ya yi. Dauda ya bauta wa Jehobah “cikin sahihancin zuciya.” (1 Sar. 9:4) Me ya sa muka ce haka? Domin Dauda ya yi ƙoƙari don ya yi nufin Jehobah.

19 Za mu iya ci gaba da bauta wa Jehobah duk da ajizancinmu. Ya kamata mu ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah da yin bimbini kuma mu aikata abin da muka koya. A sakamako, za mu zama kamar Dauda wanda ya kasance da tawali’u, kuma ya yi addu’a ga Jehobah. Ya ce: “Ka koya mini in aika nufinka.”

[Hoto a shafi na 5]

Mene ne ya sa Dauda bai kashe Saul ba, ko da yake ya samu zarafin yin hakan?

[Hoto a shafi na 6]

Mene ne za mu iya koya daga yadda Dauda ya ƙi shan ruwan da sojojinsa suka ɗebo masa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba