Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
“Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah.”—2 TIMOTHAWUS 2:15.
1. Waɗanne canje-canje ne ke kawo gwaji ga lafiyarmu ta ruhaniya?
DUNIYA da take kewaye da mu tana canjawa kullum. Mun burge da ganin ci gaban kimiyya da fasaha da kuma suƙuƙucewar darajar ɗabi’a. Yadda muka bincika a talifi na baya, dole ne Kiristoci su yi tsayayya wa ruhun da ba na Allah ba, na wannan duniyar. Yadda duniya take canjawa, mu ma muna canjawa a hanyoyi dabam dabam. Mun yi girma daga jariri zuwa mutum. Muna iya samun kuma mu yi hasarar arziki, rashin lafiyar jiki, da kuma waɗanda muke ƙaunarsu. Ba ma iya sarrafa canje-canje da yawa ba, kuma waɗannan sukan jawo sababbin ƙalubale masu wuya ƙwarai ga lafiyarmu ta ruhaniya.
2. Waɗanne canje-canje Dauda ya fuskanta a rayuwarsa?
2 Mutane kalilan ne suke shaida canje-canje na musamman a rayuwarsu, yadda ya faru da Dauda, ɗan Jesse. Dauda ya canja daga marar farin jini, ɗan kiwo zuwa shahararre a al’umma. Daga baya ya zama ɗan gudun hijira, wanda sarki mai kishi yake nemansa kamar dabba. Bayan haka, Dauda ya zama sarki kuma mai nasara. Ya jimre wa mugun sakamakon zunubi mai tsanani. Ya sha bala’i da kuma tsatsaguwa cikin iyalinsa. Ya sami arziki, ya tsufa, kuma ya yi ciwon tsufa. Amma duk da yawan canje-canje a rayuwarsa, Dauda ya nuna tabbaci da dogara a duk rayuwarsa ga Jehovah da kuma ruhunsa. Ya yi iyakacin ƙoƙarinsa ya miƙa kansa “yardaje ga Allah,” kuma Allah ya albarkace shi. (2 Timothawus 2:15) Ko da yanayinmu ya bambanta da na Dauda, za mu iya koya daga yadda ya bi da al’amura a rayuwarsa. Misalinsa zai iya taimakonmu mu fahimci yadda za mu ci gaba da samun taimakon ruhun Allah sa’ad da muke fuskantar canje-canje a rayuwarmu.
Tawali’un Dauda—Misali Mai Kyau
3, 4. Ta yaya Dauda ya bar matsayin ɗan kiwo zuwa shahararre a al’umma?
3 Da yake yaro, Dauda ba sananne ba ne ko a iyalinsa ma. Lokacin da annabi Sama’ila ya zo Bai’talahmi, uban Dauda ya kawo masa yaransa maza takwas. An bar Dauda, ƙaramin cikinsu, yana kiwon tumaki. Amma, Dauda ne Jehovah ya zaɓa ya zama sarkin Isra’ila. Aka kira Dauda daga wurin kiwo. Labarin Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa: “Sama’ila ya ɗauki ƙahon mai, ya shafe shi a tsakiyar ’yan’uwansa: ruhun Ubangiji kuma ya jiɗo ma Dawuda da iko ƙwarai daga ran nan zuwa gaba.” (1 Samu’ila 16:12, 13) Dauda ya dogara ga ruhun nan a duk rayuwarsa.
4 Ba da daɗewa ba wannan ɗan kiwo zai zama sananne a al’ummar. Aka kira shi ya zo ya yi wa sarki hidima kuma ya rera masa waƙa. Ya kashe mayaƙi Goliath, ƙato wanda sojojin da suka ƙware a Isra’ila ma sun ji tsoronsa. Da aka naɗa shi shugaban mayaƙa, Dauda ya yi nasara da Filistiyawan. Mutane suka so shi. Suka rera masa waƙar yabo. Da farko, mashawarcin Sarki Saul ya kwatanta Dauda yaro, da cewa ba kawai “gwanin kiɗi” a molo ba amma kuma “jarumi ne, mutumin yaƙi, mai-iya magana, kyakkyawan mutum.”—1 Samu’ila 16:18; 17:23, 24, 45-51; 18:5-7.
5. Da me zai sa Dauda kumburi, kuma ta yaya muka sani cewa bai yi hakan ba?
5 Dauda ya zama sananne, kyakkyawa, matashi, mai iya magana, gwanin kiɗi, jarumi, mai tagomashin Allah—kamar dai yana da kome. Da waɗannan halaye sun sa shi kumburi, amma babu wani cikinsu da ya sa shi kumburi. Ka lura da abin da Dauda ya ce wa Sarki Saul sa’ad da ya ba wa Dauda ’yarsa ya aura. Da cikakkiyar tawali’u, Dauda ya ce: “Wane ni, me ke gareni kuma, me ne gidan ubana kuma cikin Isra’ila da zan zama surukin sarki?” (1 Samu’ila 18:18) Da yake magana game da wannan ayar, wani masani ya rubuta: “Abin da Dauda yake nufi shi ne, cewa ba shi da inganci, a matsayinsa na zaman jama’a, ba ma daga iyalinsa ba, da zai iya ganin ya cancanci zama surukin sarkin.”
6. Me ya sa ya kamata mu koyi tawali’u?
6 Fahimtar cewa Jehovah ya fi mutane ajizai a kowane fasalin rayuwa ya sa Dauda ya kasance da tawali’u. Dauda ya yi mamaki ma cewa Allah yana lura da mutane. (Zabura 144:3) Dauda ya sani cewa kowacce girma da ya samu kawai domin tawali’un Jehovah ne, da ya ƙasƙantar da kansa ya kiyaye, ya kāre, kuma ya kula da shi. (Zabura 18:35) Lallai darasi ne mai kyau kuwa dominmu! Kada iyawarmu, abin da muka cim ma, da kuma gatarmu su sa mu kumburi. “Me ke gareka da ba ka karɓa kuwa?” in ji manzo Bulus. “Idan fa karɓa ne ka yi, don me ka ke fahariya, sai ka ce ba karɓa ka yi ba?” (1 Korinthiyawa 4:7) Don mu sami ruhu mai tsarki na Allah kuma mu mori tagomashinsa, dole ne mu koyi kuma adana tawali’u.—Yaƙub 4:6.
“Kada Ku Ɗauka ma Kanku Fansa”
7. Wane zarafi Dauda ya samu da zai iya kashe Sarki Saul?
7 Ko da yake farin jinin Dauda bai sa shi fahariya ba, ya jawo kishi daga wurin Sarki Saul, wanda ruhun Allah ya riga ya bar shi. Ko da yake Dauda bai yi wani laifi ba, dole ya gudu domin ransa kuma ya fara zama a daji. A wani lokaci, da suke neman Dauda, Sarki Saul ya shiga wani kogo ba su san cewa Dauda da abokansa suna ɓoye ciki ba. Mazan Dauda suka aririce shi ya yi amfani da zarafin da suke ganin cewa Allah ne ya ba su sa’a su kashe Saul. Muna iya ƙaga ganinsu cikin duhu, suna feɗuwa wa Dauda cewa: “Ga shi, rana ke nan da Ubangiji ya ce maka, Duba, zan bada maƙiyinka ga hannunka, domin ka yi masa abin da ka ga dama.”—1 Samu’ila 24:2-6.
8. Me ya sa Dauda ya kame kansa daga yin ramako?
8 Dauda ya ƙi ya taɓa Saul. Ya nuna bangaskiya da haƙuri, ya gamsu ya bar wa Jehovah al’amura. Bayan da sarkin ya fita daga kogon, Dauda ya yi masa kira ya ce: “Ubangiji shi hukumta tsakanina da kai, Ubangiji kuma shi rama mini wurinka: amma hannuna ba za ya taɓa ka ba.” (1 Samu’ila 24:12) Ko da yake ya sani cewa Saul ne mai laifin, Dauda bai yi ramako ba; kuma bai zargi Saul ba. A wasu lokatai da yawa kuma, Dauda ya kame kansa daga yin ramako. Maimako, ya dogara ga Jehovah ne ya daidaita abubuwa.—1 Samu’ila 25:32-34; 26:10, 11.
9. Me ya sa bai kamata mu yi ramako ba idan muka fuskanci hamayya ko tsanani?
9 Kana iya iske kanka a yanayi mai wuya kamar Dauda. Wataƙila abokan makaranta, abokan aiki, waɗanda suke cikin iyali, ko kuma wasu da ba sa bin imaninka suna tsananta maka. Kada ka yi ramako. Ka jira Jehovah, ka biɗi ruhunsa mai tsarki ya taimake ka. Mai yiwuwa waɗanda ba masu bi ba, nagarin halinka yana iya burge su kuma su zama masu bi. (1 Bitrus 3:1) Ko me ya faru, ka tabbata cewa Jehovah yana ganin yanayinka kuma zai yi wani abu game da shi a lokacinsa. Manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.”—Romawa 12:19.
“Ku Ji Koyarwa”
10. Ta yaya ne Dauda ya fāɗi cikin zunubi, yaya ya yi ƙoƙarin rufe shi?
10 Shekaru suka shige. Dauda ya zama sarki ƙaunatacce, shahararre. Tafarkin rayuwarsa ta aminci, tare da zabura masu daɗi da ya rubuta a yabon Jehovah zai iya sa mutum ya ji kamar wannan mutum ne da bai taɓa fāɗi cikin zunubi mai tsanani ba. Amma kuwa, ya yi haka. Wata rana, daga benensa sarkin yana kallon wata kyakkyawan mace tana wanka. Ya yi tambaya ko wacece. Da ya ji cewa Bath-sheba ce, kuma mijinta Uriah yana dagar yaƙi, Dauda ya aika a kira ta kuma ya kwana da ita. Daga baya, ya gano ta yi ciki. Lallai idan aka san wannan zai zama abin kunya! Zina cikin Dokar Musa, babban laifi ne. Sarkin yana tsammanin zai iya ɓoye zunubin. Saboda haka, ya aika saƙo wa sojoji, cewa Uriah ya dawo Urushalima. Dauda yana tsammanin Uriah zai je wajen Bath-sheba ya kwana da ita, amma ba haka ba. Yanzu da ya damu ƙwarai, Dauda ya aiki Uriah ya koma yaƙi da wasiƙa zuwa wajen Joab, shugaban sojojin. Wasiƙar tana cewa a sa Uriah a gaban yaƙi mai tsanani domin ya mutu. Haka Joab ya yi, aka kashe Uriah. Bayan Bath-sheba ta gama makoki, Dauda ya ɗauko ta ta zama matarsa.—2 Samu’ila 11:1-27.
11. Wane labari Natan ya ba wa Dauda, kuma me ya yi?
11 Kamar ƙullin ta yiwu, ko da yake ya kamata Dauda ya san cewa dukan al’amarin a buɗe yake a gaban Jehovah. (Ibraniyawa 4:13) Watanni suka wuce kuma aka haifi ɗan. Sai kuma ta wurin ja-gorar Allah, annabi Natan ya je wajen Dauda. Annabin ya gaya wa sarkin wani labari na mai arziki da yake da tumaki da yawa ya karɓa na mutumi matsiyaci da yake da guda ya yanka. Labarin ya ta da hankalin Dauda ƙwarai game da yin gaskiya amma bai yi tsammanin kome ba. Nan da nan Dauda ya shar’anta mai arzikin. Cike da fushi, ya ce wa Natan: “Mutumin da ya yi wannan ya isa mutuwa.”—2 Samu’ila 12:1-6.
12. Wane hukunci Jehovah ya yi wa Dauda?
12 Annabin ya ce: “Kai ne mutumin nan.” Dauda ya shar’anta kansa. Hakika, nan da nan fushin Dauda ya zama na kunya mai yawa da kuma baƙin ciki. Bai iya magana ba, sai ya saurara sa’ad da Natan yake furta masa hukuncin Jehovah da ba a kauce masa. Ba zancen ta’aziyya ba. Dauda ya rena maganar Jehovah ta wurin yin mugunta. Ba ya kashe Uriah da takobin magabci ba? Takobi ba zai bar gidan Dauda ba. Ba ya ɗauki matar Uriah a ɓoye ba? Za a yi masa haka nan, ba a ɓoye ba amma a fili.—2 Samu’ila 12:7-12.
13. Me Dauda ya yi game da horon Jehovah?
13 Abin kirki game da Dauda shi ne bai ɓoye zunubinsa ba. Bai yi fushi ba a kan annabi Natan. Bai ga laifin wasu ko kuma ya nemi hujjar abin da ya yi ba. Da aka nuna masa zunubinsa, Dauda ya yarda kuma ya ce: “Na yi ma Ubangiji zunubi.” (2 Samu’ila 12:13) Zabura ta 51 ta nuna baƙin cikin da ya ji kuma zurfin tubarsa. Ya roƙi Jehovah: “Kada ka yashe ni daga gabanka; kada kuma ka ɗauke mini ruhunka mai-tsarki.” Ya tabbata cewa Jehovah cikin jinƙansa, ba zai yashe “karyayyar zuciya mai-tuba” game da zunubi ba. (Zabura 51:11, 17) Dauda ya ci gaba da dogara ga ruhun Allah. Ko da yake Jehovah bai kāre Dauda daga mugun sakamakon zunubinsa ba, ya gafarta masa.
14. Yaya ya kamata mu ji game da horon Jehovah?
14 Dukanmu ajizai ne kuma dukanmu na zunubi. (Romawa 3:23) A wasu lokatai mukan yi zunubi mai tsanani, yadda ya faru da Dauda. Kamar yadda uba mai ƙauna yake horon yaransa, haka Jehovah yake gyaran waɗanda suke biɗan su bauta masa. Ko da yake horo yana da amfani, bai da sauƙi a yi na’am da shi. Hakika, a wasu lokatai ma yana da “ban ciwo.” (Ibraniyawa 12:6, 11) Duk da haka, idan muka “ji koyarwa,” za mu sulhuntu ga Jehovah. (Misalai 8:33) Don mu ci gaba da moran ruhun Jehovah dole ne mu yarda da gyara kuma mu yi abin da Allah za ya amince da mu.
Kada Ka Sa Bege a Kan Wadata Marar-Tsayawa
15. (a) A waɗanne hanyoyi wasu mutane suke amfani da arzikinsu? (b) Yaya Dauda ya so ya yi amfani da arzikinsa?
15 Babu wani tabbacin cewa Dauda ya fito daga sanannen iyali, ko kuma wadda take da arziki. Amma, a lokacin sarautarsa, Dauda ya sami arziki. Kamar yadda ka sani, mutane da yawa suna maƙo da arzikinsu, suna ƙoƙarin su daɗa samu, ko kuma su yi son kai da shi. Wasu kuma suna amfani da kuɗinsu su ɗaukaka kansu. (Matta 6:2) Dauda ya yi amfani da kuɗinsa a wata hanya dabam. Ya so ƙwarai ya ɗaukaka Jehovah. Dauda ya furta wa Natan burinsa ya gina haikali wa Jehovah don a ajiye sunduƙin alkawari a ciki, wanda a lokacin yana Urushalima a “makarai na zane.” Jehovah ya yi farin ciki da burin Dauda amma ya gaya masa ta bakin Natan cewa Ɗan Dauda ne, Sulemanu zai yi ginin.—2 Samu’ila 7:1, 2, 12, 13.
16. Wane shiri ne Dauda ya yi domin gina haikalin?
16 Dauda ya tattara kayan da za a yi amfani da su a babban aikin ginin nan. Dauda ya ce wa Sulemanu: “Na shirya talanti zambar ɗari na zinariya, talanti zambar dubu na azurfa; na jan ƙarfe da baƙin ƙarfe gaba da aunuwa; gama suna dayawa da gaske; domin gidan Ubangiji: itace da dutse kuma na shirya; in ka so fa sai ka ƙara.” Daga cikin arzikinsa, ya ba da talanti 3,000 na zinariya da kuma talanti 7,000 na azurfa.a (1 Labarbaru 22:14; 29:3, 4) Karimcin Dauda ba don ya yi fahariyar bayarwa ba ne amma bayyanuwar bangaskiya da kuma ibada ce ga Jehovah Allah. Domin ya san Tushen arzikinsa, ya ce wa Jehovah: “Dukan abu daga gareka ya ke, daga cikin naka kuma muka bayar a gareka.” (1 Labarbaru 29:14) Zuciyar Dauda na karimci ce ta motsa shi ya yi iyakacin ƙoƙarinsa domin tsarkakkiyar bauta.
17. Ta yaya gargaɗin da ke a 1 Timothawus 6:17-19 yake domin mawadata duk da matalauta?
17 Haka nan ma, bari mu yi amfani da dukiyarmu a yin nagarta. Maimakon mu biɗi abubuwan duniya, zai fi kyau mu biɗi amincewar Allah—hanyar hikima da farin ciki ta gaskiya. Manzo Bulus ya rubuta: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu; su yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyyar babbayarwa, masu-son zumunta; suna ajiye wa kansu tushe mai-kyau domin wokaci mai-zuwa, da za su ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.” (1 Timothawus 6:17-19) Ko yaya yanayin tattalin arzikinmu yake, bari mu dogara ga ruhun Allah mu kuma biɗi tafarkin rayuwa da zai sa mu kasance ‘mawadaci ga Allah.’ (Luka 12:21) Babu abin da ya fi daraja da samun tagomashi wajen Ubanmu mai ƙauna na samaniya.
Ka Miƙa Kanka Yardaje ga Allah
18. A waɗanne hanyoyi Dauda ya bar misali mai kyau wa Kiristoci?
18 Duk cikin rayuwarsa, Dauda ya nemi tagomashin Jehovah. A cikin waƙa, ya rera: “Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai; gama raina yana fake a wurinka.” (Zabura 57:1) Dogararsa cikin Jehovah ba a banza ba ne. Dauda ya tsufa, “ya jima da gaske.” (1 Labarbaru 23:1) Ko da yake Dauda ya yi kuskure mai tsanani, ana tuna da shi ɗaya cikin shaidu da yawa na Allah da ya nuna bangaskiya na musamman.—Ibraniyawa 11:32.
19. Ta yaya za mu iya miƙa kanmu yardaje ga Allah?
19 Yayin da kake fuskantar canji a rayuwa, ka tuna cewa kamar yadda Jehovah ya kiyaye, ƙarfafa, kuma ya yi wa Dauda gyara, Zai iya yi maka hakan. Manzo Bulus ma kamar Dauda ya shaida canji da yawa a rayuwa. Duk da haka, shi ma ya dogara ga ruhun Allah. Ya rubuta: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.” (Filibbiyawa 4:12, 13) Idan muka dogara ga Jehovah, zai taimake mu mu yi nasara. Yana son mu yi nasara. Idan muka saurare shi kuma muka matsa kusa da shi, zai ba mu ƙarfi mu yi nufinsa. Kuma idan muka ci gaba da dogara ga ruhun Allah, za mu iya ‘miƙa kanmu yardaje ga Allah’ a yanzu har zuwa dawwama.—2 Timothawus 2:15.
[Hasiya]
a Yawan bayarwa da Dauda ya yi idan aka gwada da yau, ya kai fiye da dalla 1,200,000,000.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za mu tsare kanmu daga fahariya?
• Me ya sa ba za mu yi ramako ba?
• Wane irin ra’ayi ya kamata muke da shi game da horo?
• Me ya sa ya kamata mu dogara ga Allah ba ga arziki ba?
[Hoto a shafi na 24]
Dauda ya dogara ga ruhun Allah kuma ya biɗi amincewarsa. Kai ma kana yin haka?
[Hoto a shafi na 26]
“Dukan abu daga gareka ya ke, daga cikin naka kuma muka bayar a gareka”