Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 3/1 pp. 22-26
  • Bari Mu Ɗaukaka Sunan Jehobah Tare

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Mu Ɗaukaka Sunan Jehobah Tare
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dauda Ya Guji Saul
  • Ya Sake Tsira Daga Mutuwa
  • Abin da Ka Sa a Gaba Ya Yi Daidai da na Dauda?
  • Taro na Ƙarfafa Bangaskiyarmu
  • Ka Yi Godiya Domin Taimakon Mala’iku
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Isra’ilawa Sun Ce a Naɗa Musu Sarki
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 3/1 pp. 22-26

Bari Mu Ɗaukaka Sunan Jehobah Tare

“Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare.”—ZABURA 34: 3.

1. Wane misali mai kyau ne Yesu ya kafa a lokacin hidimarsa a duniya?

ADAREN 14 ga Nisan, a shekara ta 33 A.Z., Yesu da manzaninsa sun yi waƙar yabo ga Jehobah a wani ɗakin bene a Urushalima. (Matta 26:30) Wannan shi ne lokaci na ƙarshe da Yesu ya yi hakan da manzaninsa. Yana da kyau da ya kammala taronsa da su a wannan hanyar. Tun daga farkon hidimarsa a duniya zuwa ƙarshenta, Yesu ya yaba wa Ubansa kuma ya sanar da sunansa da himma. (Matta 4:10; 6:9; 22:37, 38; Yohanna 12:28; 17:6) Ta haka, ya maimaita gayyatar mai zabura: “Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare.” (Zabura 34:3) Wannan misali ne mai kyau da ya kamata mu bi!

2, 3. (a) Ta yaya muka san cewa Zabura ta 34 tana da ma’ana na annabci? (b) Menene za mu tattauna a cikin wannan talifin da kuma na gaba?

2 Sa’o’i kaɗan bayan ya yi waƙar yabo tare da Yesu, manzo Yohanna ya shaida wata aukuwa dabam. Ya ga yadda aka kashe Ubangijinsa da kuma masu laifi biyu a kan gungumen azaba. Sojojin Roma sun karya ƙafafuwan masu laifin biyu don su hanzarta mutuwarsu. Kuma Yohanna ya ba da rahoto cewa ba su karya ƙafafun Yesu ba. Yesu ya riga ya mutu sa’ad da sojojin suka zo wurinsa. A cikin Linjilarsa, Yohanna ya bayyana cewa wannan cikar wani sashen Zabura ta 34 ce: “Ko ɗaya cikinsu [ƙasusuwansa] ba ya karye ba.”— Yohanna 19:32-36; Zabura 34:20.

3 Zabura ta 34 tana ƙunshe da batutuwa masu muhimmanci ga Kiristoci. Saboda haka, a cikin wannan talifin da na gaba, za mu duba yanayin da ya sa Dauda ya rubuta wannan zaburar, sa’an nan za mu tattauna abubuwa masu ban ƙarfafa da suke ƙunshe a cikin zaburar.

Dauda Ya Guji Saul

4. (a) Me ya sa aka naɗa Dauda sarkin Isra’ila na nan gaba? (b) Me ya sa Saul “ya ƙaunace” Dauda ƙwarai?

4 Sa’ad da Dauda yake matashi, Saul ne sarkin Isra’ila. Amma, Saul ya yi rashin biyayya kuma ya rasa tagomashin Jehobah. Saboda wannan dalilin, annabi Sama’ila ya gaya masa: “Yau Ubangiji ya tsage maka sarautar Isra’ila, ya bayas ga maƙwabcinka wanda ya fi ka nagarta.” (1 Samuila 15:28) Bayan haka, Jehobah ya umurci Sama’ila ya naɗa Dauda, wanda shi ne autan Yesse, don ya zama sarkin Isra’ila na gaba. Domin ya yi rashin ruhun Allah, Sarki Saul ya cika da baƙin ciki. Da yake Dauda ya iya waƙa, an kawo shi daga Gibeyon don ya yi wa sarki hidima, kuma waƙar Dauda tana sa Saul ya ji daɗi, wanda “ya kuwa ƙaunace shi ƙwarai.”—1 Samuila 16:11, 13, 21, 23.

5. Me ya sa Saul ya canja halinsa ga Dauda, kuma menene Dauda ya yi domin haka?

5 Da shigewar lokaci, Jehobah ya ci gaba da kasancewa da Dauda. Jehobah ya taimaki Dauda ya kashe katon nan ɗan Filistiya, Goliyat, kuma ya taimake shi sa’ad da mutanen Isra’ila suka yaba masa domin jarumtakarsa. Amma, albarkar da Jehobah yake yi wa Dauda ta sa Saul kishi, kuma ya soma jin haushin Dauda. Sa’ad da Dauda yake kaɗa garayarsa a gaban Saul, sarkin ya jefe shi da mashi sau biyu. A waɗannan lokatai, ya kauce wa mashin. Sa’ad da Saul ya yi ƙoƙarin ya kashe shi kuma, sarkin Isra’ila na nan gaba ya fahimci cewa yana bukatar ya gudu domin ransa. Domin Saul yana ta ƙoƙarin ya kama shi ya kashe, Dauda ya yanke shawarar samun mafaka a yankin da ba na Isra’ila ba.—1 Samuila 18:11; 19:9, 10.

6. Me ya sa Saul ya ba da umurnin cewa a kashe duka mazaunan Nob?

6 A kan hanyarsa ta zuwa iyakar ƙasar Isra’ila, Dauda ya tsaya a birnin Nob, inda mazaunin Jehobah yake. Babu shakka, akwai matasan da suke tare da Dauda, kuma Dauda ya nemi abin da shi da su za su ci. An gaya wa Saul cewa babban firist ya ba Dauda da mutanensa abinci da kuma takobin da Dauda ya ɗauke daga Goliyat. Cikin fushi, Saul ya sa aka kashe dukan mazauna birnin tare da firistoci 85.—1 Samuila 21:1, 2; 22:12, 13, 18, 19; Matta 12:3, 4.

Ya Sake Tsira Daga Mutuwa

7. Me ya sa ba Gat ba ce mafakar da ta dace ga Dauda?

7 Daga Nob, Dauda ya yi tafiyar kilomita 40 zuwa yammacin yankin Filistiya, kuma ya nemi mafaka wurin Akish Sarkin Gat a garinsu Goliyat. Wataƙila, Dauda ya yi tunanin cewa Saul ba zai zo nemansa ba a Gat. Ba da daɗewa ba, bayin sarkin Gat suka gane Dauda. Sa’ad da Dauda ya ji cewa sun gane shi, “ya kuwa ji tsoron Achish sarkin Gath ƙwarai.”—1 Samuila 21:10-12.

8. (a) Menene Zabura ta 56 ta gaya mana game da abin da Dauda ya shaida a Gat? (b) Ta yaya Dauda ya sha da kyar daga mutuwa?

8 Sai Filistiyawan suka kama Dauda. Wataƙila a wannan lokacin ne Dauda ya rubuta wannan zaburar inda ya roƙi Jehobah: “Ka sa hawayena cikin goranka.” (Zabura 56:8) Da haka, ya furta tabbacinsa cewa Jehobah ba zai mance kukansa ba, amma zai kula da shi cikin ƙauna kuma zai kāre shi. Dauda ya yi tunanin wayon da zai yi ya ruɗi sarkin Filistiya. Ya yi kamar ya haukace. Da ganin haka, Sarki Akish ya yi wa bayinsa faɗa domin sun kawo masa “mahaukaci.” Babu shakka, Jehobah ya albarkaci dabarar da Dauda ya yi. An kori Dauda daga birnin, ya sake sha da kyar daga mutuwa.—1 Samuila 21:13-15.

9, 10. Don wane dalili ne Dauda ya rubuta Zabura ta 34, kuma su waye ne ƙila ke zuciyar Dauda sa’ad da ya rubuta wannan zaburar?

9 Littafi Mai Tsarki bai faɗi ba ko magoya bayan Dauda sun bi shi zuwa cikin Gat, ko kuwa sun tsaya yi masa tsaro a ƙauyukan da ke kusa da Isra’ila ba. Ko yaya, sun sake haɗuwa cikin farin ciki sa’ad da Dauda ya gaya musu yadda Jehobah ya sake cetonsa. Wannan shi ne tushen Zabura ta 34. A sura ta ɗaya zuwa ta bakwai na zaburar, Dauda ya yaba wa Allah domin ya cece shi kuma ya gayyaci magoya bayansa su ɗaukaka Jehobah tare a matsayin Mai Ceto Mai Girma na mutanensa.—Zabura 34:3, 4, 7.

10 Dauda da mutanensa sun sami mafaka a cikin kogon Adullam a kan tsaunukan Isra’ila, kusan kilomita 15 daga gabashin Gat. A nan ne Isra’ilawa da ba sa jin daɗin sarautar Sarki Saul suka zo suka same shi. (1 Samuila 22:1, 2) Wataƙila Dauda yana tunanin irin waɗannan mutanen ne sa’ad da ya rubuta kalaman da ke Zabura 34:8-22. Tunasarwar da ke cikin waɗannan surori suna da muhimmanci a gare mu a yau, kuma za mu amfana sosai ta wajen tattauna wannan zabura mai kyau.

Abin da Ka Sa a Gaba Ya Yi Daidai da na Dauda?

11, 12. Waɗanne dalilai ne muke da su na yaba wa Jehobah a kowane lokaci?

11 “Zan albarkaci Ubangiji a kowane loto: Yabonsa kuwa za ya zauna a bakina tuttur.” (Zabura 34:1) Domin ya zama yasashe, Dauda ya damu game da abin duniya, amma kamar yadda waɗannan kalaman suka nuna, bai ƙyale damuwarsa na yau da kullum ya sha kan ƙudurinsa na yaba wa Jehobah ba. Wannan misali ne mai kyau a gare mu sa’ad da muka fuskanci matsala! Ko muna makaranta, wurin aiki, muna tare da ’yan’uwa Kiristoci, ko kuma muna hidima, ya kamata muradinmu na musamman ya kasance na yabon Jehobah. Ka yi tunanin dalilai marar iyaka da muke da su na yin haka! Alal misali, abubuwan da za mu iya gani da kuma more a cikin ayyukan Jehobah masu ban mamaki ba su da iyaka. Kuma ka yi tunanin abubuwan da ya cim ma ta sashen ƙungiyarsa ta duniya! Jehobah yana amfani da mutane masu aminci a hanyoyi masu yawa a wannan zamanin duk da cewa su ajizai ne. Za a iya kamanta ayyukan Allah da na mutanen da ake ɗaukakawa a duniya a yau? Ba ka yarda ba da Dauda wanda ya rubuta: “Babu kamarka a wurin alloli; Ba kuwa kamar ayukanka”?—Zabura 86:8.

12 Kamar Dauda, mun motsu mu yaba wa Jehobah a kullayaumi domin ayyukansa wanda babu na biyunsa. Bugu da ƙari, mun yi farin cikin sanin cewa a yanzu Mulkin Allah yana hannun Zuriyar Dauda na dindindin, Yesu Kristi. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Wannan na nufin cewa ƙarshen wannan zamanin ya kusa. Rai na dindindin na mutane fiye da biliyan shida na cikin haɗari. Muna da aiki mai yawa na gaya wa mutane game da Mulkin Allah da abin da zai yi musu nan ba da daɗewa ba, da kuma taimaka musu su yaba wa Jehobah tare da mu. Babu shakka, abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu shi ne mu yi amfani da kowane dama mu ƙarfafa mutane su karɓi “wannan bishara” kafin lokaci ya ƙure.—Matta 24:14.

13. (a) A cikin waye ne Dauda ya yi fahariya, kuma waɗanne irin mutane ne suka yi na’am? (b) Ta yaya ne ake jawo mutane masu tawali’u zuwa cikin ikilisiyar Kirista a yau?

13 “Raina za shi yi fahariya a cikin Ubangiji: Mai-tawali’u za ya ji, ya yi murna kuma.” (Zabura 34:2) Ba wai Dauda yana fahariya ba ne domin abubuwan da ya cim ma. Alal misali, bai yi fahariya ba game da yadda ya ruɗi sarkin Gat. Ya fahimci cewa Jehobah ne ya kāre shi sa’ad da yake Gat kuma ya tsira ne domin taimakon Jehobah. (Misalai 21:1) Saboda haka, Dauda bai yi fahariya ba domin kansa, amma a cikin Jehobah. Saboda haka, masu tawali’u sun kusanci Jehobah. Yesu da kansa ya ɗaukaka sunan Jehobah, kuma hakan ya jawo mutane masu tawali’u waɗanda suke son su yi koyi zuwa wurinsa. A yau, ana jawo mutane masu tawali’u daga dukan al’ummai zuwa ikilisiyar shafaffun Kiristoci na dukan duniya, wanda Yesu ne Shugabanta. (Kolossiyawa 1:18) An motsa zuciyar waɗannan mutane masu tawali’u sa’ad da suka ji yadda bayin Allah masu tawali’u suka ɗaukaka sunansa, da kuma sa’ad da suka ji saƙon Littafi Mai Tsarki, wanda ruhun Allah ya taimake su su fahimta.—Yohanna 6:44; Ayukan Manzanni 16:14.

Taro na Ƙarfafa Bangaskiyarmu

14. (a) Dauda ya gamsu da yaba wa Jehobah a ɓoye ne kawai? (b) Wane misali ne Yesu ya kafa game da taro don bauta?

14 “Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare.” (Zabura 34:3) Dauda ba ya son ya yaba wa Jehobah a ɓoye. Ya gayyaci abokansa su zo su ɗaukaka sunan Allah tare. Hakazalika, Yesu Kristi, Dauda Babba, ya yi farin cikin yaba wa Jehobah a fili, a majami’a, a bukukuwan da ake yi a haikalin Allah a Urushalima, da kuma sa’ad da yake tare da mabiyansa. (Luka 2:49; 4:16-19; 10:21; Yohanna 18:20) Gata ne mai girma mu bi misalin Yesu ta wajen yaba wa Jehobah a duk lokacin da muke tare da ’yan’uwa masu bi, musamman yanzu da muke “ganin ranan nan tana gusowa.”—Ibraniyawa 10:24, 25.

15. (a) Ta yaya ne abin da Dauda ya fuskanta ya shafi mutanensa? (b) Ta yaya ne muke amfana sa’ad da muka halarci taronmu?

15 “Na biɗi Ubangiji, ya amsa mini, ya kuma tsamarda ni daga dukan yawan tsorona.” (Zabura 34:4) Wannan abin da Dauda ya faɗa yana da muhimmanci sosai a gare shi. Shi ya sa ya ci gaba da cewa: “Wannan talaka ya yi kuka, Ubangiji kuma ya ji shi, Ya cece shi daga dukan wahalansa.” (Zabura 34:6) Sa’ad da muke tare da ’yan’uwa masu bi, muna da dama mai yawa na faɗin labarai masu ƙarfafawa game da yadda Jehobah ya taimaka mana mu jimre wasu yanayi masu wuya. Wannan yana ƙarfafa bangaskiyar ’yan’uwanmu masu bi, kamar yadda kalaman Dauda suka ƙarfafa bangaskiyar magoya bayansa. Game da Dauda kuwa, abokansa sun “duba [Jehobah], suka haskaka; Fuskokinsu kuma ba za su kumyata ba daɗai.” (Zabura 34:5) Ko da yake suna guduwa ne daga Sarki Saul, ba su ji kunya ba. Suna da tabbacin cewa Allah yana goyon bayan Dauda kuma fuskokinsu sun cika da haske. Hakazalika, mutane masu son gaskiya da kuma waɗanda suka zama Kiristoci na gaskiya tun da daɗewa sun dangana ne ga Jehobah don taimako. Tun da yake sun shaida taimakonsa, fuskokinsu da ke haske sun nuna ƙudurinsu na kasancewa da aminci.

Ka Yi Godiya Domin Taimakon Mala’iku

16. Ta yaya ne Jehobah ya yi amfani da mala’ikunsa su kāre mu?

16 “Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” (Zabura 34:7) Dauda bai ɗauki cetonsa daga Jehobah kamar abin da shi kaɗai zai iya samu ba. Hakika, Dauda shi ne sarkin Isra’ila na nan gaba da Jehobah ya naɗa; amma ya san cewa Jehobah yana amfani da mala’ikunsa su kula da masu bauta masa da aminci, ko da suna da arziki ko babu. A zamaninmu, masu bauta ta gaskiya sun shaida kāriyar da Jehobah yake bayarwa. A Nazi na Jamus, da kuma Angola, Malawi, Mazambik, da kuma ƙasashe masu yawa, masu mulki sun yi ƙoƙarin su kashe duka Shaidun Jehobah. Amma hakan bai yiwu ba. Maimakon haka, mutanen Jehobah a waɗannan ƙasashe sun ci gaba da jin daɗi yayin da suke ɗaukaka sunan Allah tare. Me ya sa? Domin Jehobah yana amfani da mala’ikunsa su kāre mutanensa.—Ibraniyawa 1:14.

17. Ta waɗanne hanyoyi ne mala’ikun Allah suke taimaka mana?

17 Ƙari ga haka, mala’ikun Jehobah suna iya juya al’amura don a cire mutumin da zai sa wasu a cikin mutanen Allah su yi tuntuɓe. (Matta 13:41; 18:6, 10) Ko da yake mai yiwuwa a wannan lokacin ba ma lura, mala’iku suna cire abin da zai hana mu yin hidimar Allah, kuma suna kāre mu daga abubuwan da za su shafi dangantakarmu da Jehobah. Mafi muhimmanci, suna yi mana ja-gora a aikinmu na sanar da “bishara ta har abada” ga duka ’yan adam, har da inda ake aikin wa’azi a cikin yanayi mai haɗari. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) An sha faɗin taimakon da mala’iku suke yi a littattafai na Littafi Mai Tsarki waɗanda Shaidun Jehobah suka wallafa.a Irin waɗannan labaran suna da yawa sosai fiye da yadda za a ce tsautsayi ne kawai.

18. (a) Menene muke bukatar mu yi idan muna son mu sami taimakon mala’iku? (b) Menene za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Domin mu ci gaba da amfana daga taimakon mala’iku da ja-gorarsu, dole ne mu ci gaba da ɗaukaka sunan Jehobah har ma a lokacin hamayya. Ka tuna cewa, mala’ikan Allah ‘yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa [Jehobah]’ ne kawai. Menene hakan ke nufi? Menene tsoron Allah, kuma ta yaya za mu iya nuna ta? Me ya sa Allah mai ƙauna zai so mu ji tsoronsa? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafi na 550; 2005 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafofi 53-54; Hasumiyar Tsaro, 1 ga Maris, 2000, shafofi 5-6; 1 ga Janairu, 1991, shafi na 27; da kuma 15 ga Fabrairu , 1991, shafi na 26.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne gwaji ne Dauda ya jimre sa’ad da yake matashi?

• Kamar Dauda, menene ainihin damuwarmu?

• Ta yaya ne muka ɗauki taron Kirista?

• Ta yaya ne Jehobah yake yin amfani da mala’ikunsa su taimake mu?

[Taswira a shafi na 23]

Ramah

Gat

Ziklag

Gibeyon

Nob

Urushalima

Baitalami

Adullam

Keilah

Hebron

Ziph

Horesh

Karmel

Maon

En-gedi

Tekun Gishiri

[Inda aka Dauko]

Taswira: Based on maps copyrighted by Pictorial Archive (Near Eastern History) Est. and Survey of Israel

[Hoto a shafi na 23]

Duk da cewa shi ɗan gudun hijira ne, Dauda ya ɗaukaka sunan Jehobah

[Hoto a shafi na 25]

Bangaskiyarmu na ƙarfafa sa’ad da muka saurari labaran da ake faɗa a taronmu na Kirista

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba