Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
“Ya Allah, ka yi hamzari zuwa gareni: Kai ne taimakona da mai-cetona.”—ZAB. 70:5.
1, 2. (a) A wane lokaci ne masu bauta wa Jehobah suke yin addu’a don ya taimake su? (b) Wace tambaya ce ya kamata mu yi, kuma a ina ne za mu sami amsar?
SA’AD da wasu ma’aurata suka yi tafiya, sun ji cewa ’yarsu mai shekara ashirin da uku da ta yi aure ta ɓace. Suna tsammanin an sace ta ne. Nan da nan sai suka tattara kayansu suka koma gida, suna roƙon Allah ya taimake su. An gaya wa wani Mashaidi mai shekara 20 cewa yana da wata cuta da ta shanye masa jiki gaba ɗaya. Nan da nan sai ya yi addu’a ga Jehobah. Wata mata da take ta famar neman aiki, kuma ba ta da isashen kuɗin sayan abinci da za su ci da ita da ’yarta mai shekara 12. Ta yi addu’a ga Jehobah. Hakika, idan suna fuskantar jarabobbi masu tsanani ko kuma matsaloli, bayin Allah suna roƙonsa ya taimake su. Ka taɓa roƙon Jehobah ya taimake ka a lokacin da kake da bukata mai tsanani?
2 Wata tambaya mai muhimmanci, ita ce: Ya kamata mu sa rai cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu kuwa? Za a samu amsa mai ƙarfafa bangaskiya a Zabura sura 70. Dauda mutum mai bauta wa Jehobah da aminci wanda ya fuskanci jarabobbi da ƙalubale a rayuwarsa ne ya rubuta zabura. Wannan mai zabura da aka hure ya ce game da Jehobah: “Ya Allah, . . . Kai ne taimakona da mai-cetona.” (Zab. 70:5) Bincika Zabura sura 70 zai iya taimakonmu mu ga cewa mu ma za mu iya yin addu’a ga Jehobah a lokacin da muke cikin matsala kuma mu tabbata cewa zai kasance ‘mai-cetonmu.’
“Kai Ne . . . Mai Ceto”
3. (a) Wane roƙo na neman taimako ne ke cikin Zabura sura 70? (b) Wane tabbaci ne Dauda ya nuna a Zabura sura 70?
3 Zabura sura 70 ta soma kuma ta ƙare da roƙon Allah ya taimaka. (Ka karanta Zabura 70:1-5.) Dauda ya roƙi Jehobah ya yi “hamzari” don ya cece shi. A tsakanin aya 2 zuwa 4, Dauda ya yi roƙo sau biyar, guda uku na farko game da waɗanda suke so su kashe shi ne. Dauda ya roƙi Jehobah ya halaka waɗannan miyagun kuma ya kunyatar da su don muguntarsu. Roƙo guda biyun da ke aya ta 4 game da mutanen Allah ne. Dauda ya yi addu’a cewa waɗanda suke biɗan Jehobah su yi murna kuma su ɗaukaka shi. A ƙarshen addu’ar sa, Dauda ya ce wa Jehobah: “Kai ne taimakona da mai-cetona.” Ka lura, Dauda bai ce “bari ka kasance” ba, kamar yana wani roƙo ne. Amma ya ce, “Kai ne,” hakan ya nuna tabbacinsa. Dauda ya gaskata cewa zai sami taimako daga Allah.
4, 5. Menene muka koya game da Dauda a cikin Zabura sura 70, kuma wane tabbaci ne ya kamata mu kasance da shi?
4 Menene Zabura sura 70 ta nuna game da Dauda? Sa’ad da miyagu suke son su kashe shi, Dauda bai sasanta al’amuran da kansa ba. Maimakon haka, ya tabbata cewa Jehobah zai ba ’yan hamayya sakamakonsu yadda yake so kuma a daidai lokacinsa. (1 Sam. 26:10) Dauda ya ci gaba da tabbata cewa Jehobah zai taimaki kuma ya cece waɗanda suke roƙonsa. (Ibran. 11:6) Dauda ya gaskata cewa irin waɗannan masu bauta na gaskiya suna da dalilin yin farin ciki kuma su girmama Jehobah ta wajen gaya wa mutane game da girmansa.—Zab. 5:11; 35:27.
5 Kamar Dauda, za mu iya tabbata cewa Jehobah mai Taimakonmu ne kuma ‘mai-cetonmu.’ Saboda haka, sa’ad da muke fuskantar jarrabobi masu tsanani ko kuma muna bukatar taimako, yana da kyau mu roƙi Jehobah ya taimake mu da hanzari. (Zab. 71:12) Yaya ne Jehobah zai amsa addu’o’inmu na neman taimako? Kafin mu tattauna yadda Jehobah zai taimake mu, bari mu bincika hanyoyi uku da ya ceci Dauda, kuma ya taimake shi a lokacin bukata sosai.
Ceto Daga Masu Hamayya
6. Menene ya taimaki Dauda ya san cewa Jehobah yana ceton masu aminci?
6 Daga sashen Littafi Mai Tsarki da yake da shi a lokacin, Dauda ya san cewa masu aminci za su iya dogara ga Jehobah ya taimake su. Sa’ad da Jehobah ya kawo rigyawa bisa duniya marar ibada, ya ceci Nuhu da iyalinsa masu tsoron Allah. (Far. 7:23) Sa’ad da Jehobah ya aiko da wuta da kibritu bisa miyagu da ke Saduma da Gwamrata, ya taimaki Lutu mai aminci da ’ya’yansa mata biyu su tsira da ransu. (Far. 19:12-26) Sa’ad da Jehobah ya halaka Fir’auna mai fahariya da sojojinsa a Jan Teku, ya ceci mutanensa daga halaka. (Fit. 14:19-28) Shi ya sa Dauda ya ɗaukaka Jehobah a wata aya cikin zabura a matsayin “Allah mai-yawan ceto.”—Zab. 68:20.
7-9. (a) Wane dalili ne ya sa Dauda ya dogara da ikon Allah na ceto? (b) Wanene Dauda ya ce ya cece shi?
7 Dauda kuma yana da wani dalili da ya sa ya tabbata cewa Jehobah zai cece shi. Dauda da kansa ya ga yadda ‘madawaman hannuwan’ Jehobah suke ceton waɗanda suke bauta masa. (K. Sha 33:27) Sau da yawa, Jehobah ya ceci Dauda daga wurin “maƙiya.” (Zab. 18:17-19, 48) Ka yi la’akari da wannan misali.
8 Sa’ad da matan Isra’ila suke yabon Dauda don nasararsa a yaƙi, Sarki Saul ya soma kishin Dauda har ya jefi Dauda sau biyu da kibiyarsa. (1 Sam. 18:6-9) Dauda ya kauce wa kibiyar sau biyu. Dauda ya tsira don shi ƙwararren mai yaƙi ne? A’a. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa “Ubangiji . . . yana tare da shi.” (Ka karanta 1 Samuila 18:11-14.) Daga baya, sa’ad da ƙullin da Saul ya yi don Filibiyawa su kashe Dauda bai yiwu ba, “Saul . . . ya lura ya sani Ubangiji yana tare da Dauda.”—1 Sam. 18:17-28.
9 Dauda ya ce wani ne ya cece shi. To, wanene ya cece shi? Rubutu na sama a cikin Littafi Mai Tsarki na Ibrananci na ainihi a Zabura 18 ya ce Dauda ya yi “magana da Jehobah a kalaman wannan waƙar a ranar da Jehobah ya cece shi . . . daga hannun Saul.” Dauda ya nuna yadda yake ji a waƙa, yana cewa: “Ubangiji pana ne, da kagarata, mai-cetona kuma; Allahna, pana mai-ƙarfi, a cikinsa zan dogara.” (Zab. 18:2) Yana ƙarfafa bangaskiyarmu mu sani cewa Jehobah yana iya ceton mutanensa.—Zab. 35:10.
Taimako a Lokacin Ciwo
10, 11. Menene zai taimake mu mu san lokacin da Dauda ya yi rashin lafiya da aka ambata a Zabura sura 41?
10 Sarki Dauda ya taɓa yin ciwo mai tsanani, da aka ambata a Zabura sura 41. Dauda ya yi rashin lafiya sosai yana kwance a bisa gado, har abokan gabansa suna tsammanin cewa ba zai “sake tashi ba.” (Ayoyi 7, 8) Yaushe ne Dauda ya yi rashin lafiya mai tsanani? Wataƙila hakan ya faru ne lokacin da ɗansa Absalom yake ƙoƙarin ya karɓe mulkin.—2 Sam. 15:6, 13, 14.
11 Ko kuwa Dauda yana maganar wani aboki ne mai aminci, wanda yake cin gurasa tare da shi, cewa shi ne ya ci amanarsa. (Aya 9) Wannan ya tuna mana da wani abu da ya faru a rayuwar Dauda. A lokacin da Absalom ya yi tawaye, Ahithophel mai ba wa Dauda shawara ya ci amanarsa kuma ya haɗa hannu da Absalom don su sha kan sarkin. (2 Sam. 15:31; 16:15) Ka yi la’akari da sarkin a bisa gadonsa ba ƙarfin tashiwa, kuma yana sane cewa yana kewaye da abokan gaban da suke so su kashe shi don su ci gaba da ƙullinsu.—Aya 5.
12, 13. (a) Wane tabbaci ne Dauda yake da shi? (b) Ta yaya ne Allah ya ƙarfafa Dauda?
12 Dauda ya dogara ga “mai-ceto.” Game da wani mai bauta wa Jehobah da yake rashin lafiya, Dauda ya ce: “Ubangiji za ya cece shi cikin baƙar ranar. Ubangiji za ya toƙara shi a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya: kana gyarta masa shimfiɗa cikin cutarsa.” (Zab. 41:1, 3) A nan kuma Dauda ya nuna tabbacinsa, kamar yadda ya ambata sa’ad da ya ce “Ubangiji za ya” yi. Dauda ya tabbata cewa Jehobah zai cece shi. Ta yaya?
13 Dauda ba ya nufin Jehobah ya yi mu’ujiza ya cire cutar. Amma, Dauda ya tabbata cewa Jehobah za ya “toƙara shi” wato, zai taimake shi kuma ya ƙarfafa shi sa’ad da yake kwance a gadon ba lafiya. Hakika, Dauda yana bukatar taimako. Ban da cuta da ta hana shi tashiwa, yana kewaye da abokan gaba da suke maganganun banza a kansa. (Ayoyi 5, 6) Wataƙila Jehobah ya ƙarfafa Dauda ta wurin sa ya tuna da kalamai masu ƙarfafawa. Dauda ya ce: “Kana riƙe da ni cikin kamalata.” (Aya 12) Wataƙila Dauda ya sami ƙarfi sa’ad da ya tuna cewa ko da yake ba shi da lafiya kuma abokan gabansa suna mugun maganganu, Jehobah ya ɗauke shi a matsayin mutum mai aminci. Daga baya Dauda ya warke daga rashin lafiyar da ya yi. Abin ƙarfafa ne a san cewa Jehobah yana taimakon waɗanda suke rashin lafiya.—2 Kor. 1:3.
Abinci da Sutura
14, 15. Yaushe ne Dauda da mutanensa suka samu kansu a cikin bukata, kuma wane taimako ne suka samu?
14 Sa’ad da ya zama sarki a Isra’ila, Dauda yana cin abinci da abin sha mafi kyau har ya gayyaci wasu mutane su ci abinci da shi. (2 Sam. 9:10) Dauda ma ya taɓa rashin abin ci da abin sha. Sa’ad da ɗansa Absalom ya yi tawaye kuma ya yi ƙoƙari ya karɓe mulkin, Dauda tare da wasu da suke yi masa biyayya sun bar Urushalima. Sun gudu zuwa ƙasar Gilead, da ke gabashin Kogin Urdun. (2 Sam. 17:22, 24) Saboda sun yi gudun hijira, ba da daɗewa ba Dauda da mutanensa sun soma bukatar abin ci da abin sha da kuma wurin hutawa. A ina ne za su sami abin da suke bukata a cikin jeji?
15 A ƙarshe, Dauda da mutanensa suka kai birnin Mahanaim. A nan ne suka haɗu da maza masu gaba gaɗi, wato, Shobi, Machir da kuma Barzillai. Suna a shirye su ba da ransu don su taimaki sarkin da Allah ya naɗa, domin idan Absalom ya karɓi mulkin, babu shakka zai hukunta dukan waɗanda suka goyi bayan Dauda. Sa’ad da suka ga matsalar da Dauda da mutanensa suke ciki, waɗannan mutane masu aminci sun kawo musu abin biyan bukata, har da shimfiɗa, alkama, sha’ir, gasashen hatsi, wake, lentils, zuma, mai, da kuma tumaki. (Ka karanta 2 Samuila 17:27-29.) Dauda ya yi godiya sosai da irin aminci da halin karɓan baƙi da waɗannan mutane uku suka nuna. Dauda ba zai taɓa manta da abin da suka yi masa ba.
16. Wanene yake da hakkin yi wa Dauda da mutanensa tanadin abin biyan bukata?
16 Wanene yake da hakkin yi wa Dauda da mutanensa tanadin abin biyan bukata? Dauda ya tabbata cewa Jehobah ne yake kula da mutanensa. Hakika Jehobah zai iya motsa wasu bayinsa su taimaki wani ɗan’uwa da ke neman taimako. Sa’ad da yake tunanin abin da ya faru a ƙasar Gilead, Dauda ya tabbata cewa alherin waɗannan mutane uku ya nuna ƙaunar Jehobah. A ƙarshen rayuwarsa, Dauda ya rubuta: “Dā yaro ni ke, yanzu kuwa na tsufa: amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” (Zab. 37:25) Abin farin ciki ne a san cewa Jehobah zai yi wa bayinsa tanadin abin biyan bukata.—Mis. 10:3.
“Ubangiji Ya San Yadda Zai Ceci” Mutane
17. Menene Jehobah ya ci gaba da nunawa?
17 Dauda yana ɗaya daga cikin masu bauta da yawa da Jehobah ya cece su a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Bayan zamanin Dauda, Allah ya ci gaba da nuna gaskiyar abin da manzo Bitrus ya ce: “Ubangiji ya san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” (2 Bit. 2:9) Ka yi la’akari da misalai biyu.
18. Yaya ne Jehobah ya yi tanadin tsira a zamanin Hezekiya?
18 Sa’ad da rundunar sojojin Assuriya masu ƙarfi suka shigo Yahuda kuma suka yi wa Urushalima barazana a ƙarni na takwas K.Z., Sarki Hezekiya ya yi addu’a: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu . . . domin dukan mulkokin duniya su sani kai ne Ubangiji kai kaɗai.” (Isha. 37:20) Ainihin abin da ya dami Hezekiya shi ne a girmama sunan Jehobah. Jehobah ya amsa addu’ar da ya yi. A cikin dare ɗaya, mala’ika guda ya kashe Assuriyawa guda 185,000, don ya ceci amintattun bayin Jehobah.—Isha. 37:32, 36.
19. Ta wurin bin wane umurni ne Kiristoci na ƙarni na farko suka tsira daga halaka?
19 Kwanaki kaɗan kafin mutuwarsa, Yesu ya ba da gargaɗi a annabce don almajiransa a Yahuda su amfana. (Ka karanta Luka 21:20-22.) Shekaru goma bayan haka, a shekara ta 66 A.Z., Yahudawa da suka yi tawaye suka kawo sojojin Romawa zuwa Urushalima. Sojojin da suke ƙarƙashin Cestius Gallus sun yi nasara sa’ad da suka rushe bangon haikalin; sai nan da nan suka janye. Fahimtar abin da ya faru ya ba wa amintattun Kiristoci zarafin tsira daga halaka zuwa dutse kamar yadda Yesu ya annabta. Sojojin Romawa sun dawo a shekara ta 70 A.Z. Wannan lokacin ba su ja da baya ba, sai da aka halaka Urushalima gaba ɗaya. Kiristoci da suka bi umurnin Yesu sun tsira daga wannan halakar.—Luka 19:41-44.
20. Me ya sa ya kamata mu dogara ga Jehobah ‘mai cetonmu’?
20 Za mu ƙarfafa bangaskiyarmu idan muka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimaki mutanensa a dā. Abin da ya yi a dā zai sa mu dogara gare shi. Ko da wane irin ƙalubale ne muke fuskanta a yanzu ko kuma za mu fuskanta a nan gaba, ya kamata mu ma mu dogara da Jehobah ‘mai cetonmu.’ Ta yaya ne Jehobah zai cece mu? Mutanen da aka ambata a farkon wannan talifin kuma fa? Yaya abubuwa suka juya musu? Bari mu gani a talifi na gaba.
Ka Tuna?
• Zabura sura 70 ta ba mu wane dalili ne na kasancewa da tabbaci?
• Ta yaya ne Dauda ya sami taimako sa’ad da yake ciwo?
• Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Jehobah zai iya ceton mutanensa daga ’yan hamayya?