Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 5/15 pp. 28-32
  • Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da ‘Mutane da Yawa Suka Tasam Mana’
  • ‘Jehobah Zai Amsa!’
  • “Ceto ga Ubangiji Ya Ke”
  • Dauda Ya Sake Nuna Dogara ga Allah
  • Ka Ci Gaba da Yin Cikakkiyar Dogara ga Allah
  • Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Darussa Daga Littafin Sama’ila na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 5/15 pp. 28-32

Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi

“Ubangiji za ya ji lokacin da na yi kira gareshi.”—ZAB. 4:3.

1, 2. (a) Waɗanne yanayi masu wuya ne Dauda ya fuskanta? (b) Waɗanne zabura ne za mu tattauna?

SARKI DAUDA ya ɗan daɗe yana sarautar ƙasar Isra’ila, amma yanzu yana fuskantar yanayi mai wuya. Ɗansa Absalom mai ƙulle-ƙulle ya sanar cewa shi ne sarki, kuma ya tilasta wa Dauda ya yi gudun hijira zuwa Urushalima. Amininsa ya kuma ci amanarsa, yanzu kuma, wasu aminansa da suka rage suna tafiya tare da shi yayin da yake tafe ƙafa wofi yana kuka a kan Dutsen Zaitun. Kuma daga baya Shimei, wanda yake cikin iyalin Sarki Saul, yana jifansa da duwatsu kuma yana yayyafa wa Dauda ƙura yayin da yake zaginsa.—2 Sam. 15:30, 31; 16:5-14.

2 Shin wannan yanayin zai sa Dauda ya mutu saboda baƙin ciki da kunya? A’a, domin ya dogara ga Jehobah. Mun san da hakan daga Zabura ta uku, da Dauda ya rubuta game da gudun da ya yi. Ya kuma rubuta Zabura ta huɗu. Dukan waɗannan rubuce-rubucen sun nuna tabbaci cewa Allah yana sauraro kuma yana amsa addu’o’i. (Zab. 3:4; 4:3) Wannan zaburar ta nuna cewa Jehobah yana kasancewa tare da amintattunsa dare da rana, kuma yana albarkace su da kāriya da salama da kuma lumana. (Zab. 3:5; 4:8) Bari mu tattauna waɗannan zaburar kuma mu ga yadda suke sa mu gaba gaɗi kuma suke sa mu dogara ga Allah.

Sa’ad da ‘Mutane da Yawa Suka Tasam Mana’

3. Mene ne yanayin Dauda bisa ga abin da ke Zabura 3:1, 2?

3 Wani manzo ya ce: “Zuciyar Isra’ilawa sun koma wajen Absalom.” (2 Sam. 15:13) Da yake mamaki game da yadda mutane da yawa suka goyi bayan Absalom, Dauda ya yi tambaya: “Ya Ubangiji, me ya sa maƙiyana sun ƙaru ba misali? Waɗanda sun tasa mani da yawa su ke. Da yawa ne masu-ce da raina, ba shi da wani taimako wurin Allah.” (Zab. 3:1, 2) Isra’ilawa da yawa suna ji cewa Jehobah ba zai ceci Dauda daga masifa a hannun Absalom da magoyan bayansa ba.

4, 5. (a) Wane tabbaci ne Dauda yake da shi? (b) Mene ne ma’anar kalmomin nan “mai-ɗaukaka kaina”?

4 Amma Dauda yana da gaba gaɗi domin ya dogara gabaki ɗaya ga Allah. Ya rera: “Ya Ubangiji, kai garkuwa ne gareni; Darajata, da mai-ɗaukaka kaina kuma.” (Zab. 3:3) Dauda ya tabbata cewa Jehobah zai kāre shi kamar yadda garkuwa take kāre soja. Hakika, sarkin tsoho yana gudu cike da kunya. Amma Maɗaukaki Duka zai canja yanayin Dauda zuwa na ɗaukaka. Jehobah zai sa ya yiwu ya sake samun gaba gaɗi kuma ya kawar da kunya da yake ji. Dauda ya yi kira ga Allah da sanin cewa zai amsa masa. Kana dogara ga Jehobah haka kuwa?

5 Ta kalaman nan “mai-ɗaukaka kaina,” Dauda ya nuna cewa taimakon da zai samu zai taho ne daga wurin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, kana ba ni nasara. Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.” Game da kalmar nan “mai-ɗaukaka kaina,” wani bincike da aka yi ya ce: “Sa’ad da Allah ya ɗaukaka ‘kan’ wani, Yana sa mutum ya samu bege da gaba gaɗi.” Dauda yana da dalilin yin baƙin ciki, tun da an kore shi daga sarautarsa. Amma dai, ‘ɗaukaka kansa’ zai sa ya sake samun gaba gaɗi da ƙarfin zuciya da kuma cikakkiyar dogara ga Allah.

‘Jehobah Zai Amsa!’

6. Me ya sa Dauda ya ce Jehobah ya amsa addu’arsa daga dutsensa mai-tsarki?

6 Da yake yana dogara ga Jehobah kuma yana cike da gaba gaɗi, Dauda ya ci gaba da cewa: “Da muryata ni kan yi kuka ga Ubangiji, Ya kan amsa mani daga cikin dutsensa mai-tsarki kuma.” (Zab. 3:4) An kai sunduƙi, wanda ke wakiltar kasancewar Allah, zuwa Dutsen Sihiyona bisa ga umurnin Dauda. (Karanta 2 Sama’ila 15:23-25.) Shi ya sa Dauda ya ce Jehobah ya amsa addu’arsa daga dutsensa mai-tsarki.

7. Me ya sa Dauda bai yi fargaba ba?

7 Dauda bai yi fargaba ba tun da ya san cewa Allah ba zai yi watsi da addu’arsa ba. Maimakon haka, ya rera waƙa: “Na kwanta, na yi barci; na falka; gama Ubangiji yana kiwona.” (Zab. 3:5) Dauda bai ji tsoron yin barci da dare ba sa’ad da ake fi kai wa mutum hari farat ɗaya. Abin da ya faru masa a dā ya tabbatar masa cewa zai farka, kuma lallai Allah zai tallafa masa. Hakan ma zai iya faru da mu idan mun “kiyaye tafarkun Ubangiji” kuma ba mu bar shi ba.—Karanta 2 Sama’ila 22:21, 22.

8. Ta yaya Zabura 27:1-4 ta nuna cewa Dauda ya dogara ga Allah?

8 Wata zabura da Dauda ya kuma rubuta wadda ke ɗauke da waɗannan hurarrun kalmomi sun tabbatar mana cewa Dauda yana da gaba gaɗi da cikakkiyar dogara ga Allah: “Ubangiji ne haskena da cetona kuma; tsoron wa zan ji? Ubangiji shi ne ƙarfin raina; zan ji tsoron wanene? . . . Ko rundunar yaƙi za ta kafa mani sansani, zuciyata ba za ta ji tsoro ba. . . . Abu guda ɗaya na yi roƙo ga Ubangiji, shi zan nema; in zauna cikin gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, domin in dubi jamalin Ubangiji, in yi ta tunani cikin haikalinsa.” (Zab. 27:1-4) Idan kai ma ka yi irin wannan ƙudurin kuma idan da hali, za ka riƙa halartar tarurruka tare da ’yan’uwanka masu bauta wa Jehobah a kai a kai.—Ibran. 10:23-25.

9, 10. Duk da kalaman Zabura 3:6, 7, me ya sa za mu ce Dauda bai da baƙar zuciya?

9 Ko da yake Dauda yana fuskantar cin amana na Absalom da kuma rashin amincin mutane da yawa, ya rera waƙa: “Ba zan ji tsoron ɗimbin mutane ba, waɗanda sun kewaye ni da gāba. Tashi, ya Ubangiji; ka cece ni, ya Allahna: Gama ka buga dukan maƙiyana a kumatu; Ka kakaryi haƙoran masu-mugunta.”—Zab. 3:6, 7.

10 Dauda bai da baƙar zuciya. Idan za a ‘buga maƙiyansa a kumatu,’ Allah ne zai yi hakan. Sarki Dauda ya rubuta Dokar da kansa kuma ya san cewa a ciki Jehobah ya ce: “Ramawa gareni ta ke, da sakamako kuma.” (K. Sha 17:14, 15, 18; 32:35) Allah ne kuma zai “kakaryi haƙoran masu-mugunta.” Kakaryi haƙoransu yana nufin cewa za a naƙasa su har ba za su iya yin la’ani ba. Jehobah ya san miyagu domin “yana duban zuciya.” (1 Sam. 16:7) Muna farin ciki cewa Allah yana ba mu bangaskiya da ƙarfi mu tsayayya wa sarkin mugunta, Shaiɗan, wanda ba da daɗewa ba za a ɗaure shi kamar zaki mai ruri wanda bai da haƙora, kuma ya dace a halaka shi!—1 Bit. 5:8, 9; R. Yoh. 20:1, 2, 7-10.

“Ceto ga Ubangiji Ya Ke”

11. Me ya sa ya dace mu saka ’yan’uwanmu masu bi a addu’armu?

11 Dauda ya san cewa Jehobah ne kaɗai zai ba shi ceton da yake bukata. Amma marubucin zabura bai yi tunanin kansa ba kawai. Dukan bayin Jehobah amintattu kuma fa? Ya dace da Dauda ya kammala hurarrun zaburarsa da kalmomin nan: “Ceto ga Ubangiji ya ke: albarkarka ta zauna bisa mutanenka.” (Zab. 3:8) A gaskiya, Dauda yana da matsaloli da yawa, amma yana tunawa da mutanen Jehobah gabaki ɗaya kuma yana da gaba gaɗi cewa Allah zai albarkace su. Ya dace mu ma mu riƙa tunawa da ’yan’uwanmu. Bari mu tuna da su a addu’o’inmu, mu roƙi Jehobah ya ba su ruhunsa mai tsarki don su samu gaba gaɗi kuma su yi shelar bishara da ƙarfin zuciya.—Afis. 6:17-20.

12, 13. Mene ne ya faru wa Absalom, kuma yaya Dauda ya aikata?

12 Absalom ya mutu a hanya marar kyau, kuma hakan gargaɗi ne ga dukan waɗanda suke wulakanta wasu, musamman shafaffun Allah, kamar Dauda. (Karanta Misalai 3:31-35.) An yi yaƙi, kuma rundunar Absalom sun ci kāshi. Absalom da kansa yana tafiya a kan alfadarinsa sai reshen wani babban itace ya kama sumar kansa. Yana a rataye a wurin babu mai cetonsa, sai Yowab ya kashe shi ta wurin soke māshi guda uku a zuciyarsa.—2 Sam. 18:6-17.

13 Shin Dauda ya yi farin ciki sa’ad da ya ji abin da ya faru wa ɗansa? A’a. Maimakon haka, ya yi kuka yana kai da kawowa, yana cewa: “Ya ɗana Absalom, ya ɗana, ɗana Absalom! Da ma Allah ya yarda na mutu dominka, ya Absalom, ya ɗana, ɗana!” (2 Sam. 18:24-33) Kalaman Yowab ne kaɗai suka ƙarfafa Dauda. Absalom wanda kwaɗayinsa ya motsa shi ya tasam ma mahaifinsa, wanda shafaffe ne, kuma ya jawo wa kansa la’ani ya mutu a mummunar hanya!—2 Sam. 19:1-8; Mis. 12:21; 24:21, 22.

Dauda Ya Sake Nuna Dogara ga Allah

14. Mene ne za a iya cewa game da rubutun Zabura ta huɗu?

14 Kamar Zabura ta uku, Zabura ta huɗu tana ɗauke da addu’a da Dauda ya yi da dukan zuciyarsa da ta nuna cewa ya dogara ga Jehobah gabaki ɗaya. (Zab. 3:4; 4:3) Wataƙila Dauda ya rubuta wannan zaburar don ya nuna kwanciyar ransa da kuma godiya ga Allah bayan da juyin mulkin da Absalom ya shirya bai yi nasara ba. Ko kuma ya rubuta ne don Lawiyawa mawaƙa. Ko da mene ne ya motsa shi ya rubuta ta, yin bimbini a kai zai iya ƙarfafa dogararmu ga Jehobah.

15. Me ya sa za mu iya yin addu’a ga Jehobah da gaba gaɗi ta hanyar Ɗansa?

15 Dauda ya kuma nuna cikakkiyar dogara ga Allah kuma ya kasance da gaba gaɗi cewa Allah yana amsa addu’arsa. Ya rera waƙa: “Ya Allah na adalcina, ka amsa mani lokacin da na yi kira; lokacin da ina cikin ƙunci kā yalwata ni: ka yi mani jinƙai, ka ji addu’ata.” (Zab. 4:1) Mu ma za mu iya samun irin wannan gaba gaɗin idan mun kasance da aminci. Sanin cewa Jehobah, ‘Allah na adalci,’ yana yi wa amintattunsa albarka, zai iya motsa mu mu yi addu’a gare shi da gaba gaɗi ta wurin Ɗansa da imani ga fansar hadaya ta Yesu. (Yoh. 3:16, 36) Yin hakan na sa mu kwanciyar rai sosai!

16. Mene ne wataƙila ya sa Dauda sanyin gwiwa?

16 A wasu lokatai, yanayi masu sa sanyin gwiwa za su iya sa mu rasa gaba gaɗinmu. Wataƙila, hakan ya faru da Dauda na ɗan lokaci, domin ya rera: “Ku ’yan adam, har yaushe za a juyar da darajata ta koma ƙasƙanci? Har yaushe za ku ƙaunaci banza, ku biɗi ƙarya?” (Zab. 4:2) Furucin nan “’yan adam,” yana nufin ’yan Adam a yanayi marar kyau. Maƙiyan Dauda ‘sun ƙaunaci banza.’ Ga yadda juyin New International Version ya fassara wannan ayar: “Har yaushe za ku ƙaunaci ƙarya ku kuma biɗi allolin ƙarya?” Ko da abin da mutane suka yi ya sa mu sanyin gwiwa, bari mu ci gaba da yin addu’a da dukan zuciya kuma mu nuna cewa mun dogara gabaki ɗaya ga Allah makaɗaici na gaskiya.

17. Ka bayyana yadda za mu iya aikatawa bisa Zabura 4:3.

17 Kalaman nan sun nuna cewa Dauda yana da cikakkiyar dogara ga Allah: “Amma ku sani Ubangiji ya ware wa kansa mai-ibada: Ubangiji za ya ji lokacin da na yi kira gareshi.” (Zab. 4:3) Muna bukatar gaba gaɗi da cikakkiyar dogara ga Jehobah don mu kasance da aminci. Alal misali, iyalan Kirista suna bukatar wannan halin sa’ad da aka yi wa danginsu da bai tuba ba yankan zumunci. Allah yana yi wa waɗanda suke da aminci gare shi da hanyoyinsa albarka. Kuma, aminci da cikakkiyar dogara ga Jehobah suna kawo farin ciki tsakanin mutanensa.—Zab. 84:11, 12.

18. Bisa ga Zabura 4:4, me ya kamata mu yi idan wani ya faɗi ko ya yi mana abu marar kyau?

18 Idan wani ya yi ko kuma ya ce abin da ya ɓata mana rai kuma fa? Za mu iya ci gaba da yin farin ciki idan mun yi abin da Dauda ya ce: “Ku ji tsoro, kada kuwa ku yi zunubi: ku yi shawara da zuciyarku a bisa shimfiɗarku, ku yi shuru.” (Zab. 4:4) Idan wani ya ce ko kuma ya yi abin da ya ɓata mana rai, bai kamata mu yi zunubi ta ramawa ba. (Rom. 12:17-19) Za mu iya furta wa Allah yadda muke ji a addu’a sa’ad da muka kwanta a kan gado. Ra’ayinmu zai iya canjawa idan mun yi addu’a game da batun kuma hakan zai motsa mu mu gafarta saboda ƙauna. (1 Bit. 4:8) Abu na musamman game da wannan shi ne gargaɗin manzo Bulus, wanda wataƙila ya ɗauko ne daga Zabura 4:4: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.”—Afis. 4:26, 27.

19. Ta yaya Zabura 4:5 za ta iya taimaka mana a bautarmu?

19 Da yake furta amfanin yin dogara ga Allah, Dauda ya rera waƙa: “Ku bada hadayu na adalci, ku sa danganarku ga Ubangiji.” (Zab. 4:5) Hadayar da Isra’ilawa suke bayarwa za ta kasance da amfani ne kawai idan suna da muradi mai kyau. (Isha. 1:11-17) Mu ma muna bukatar kasancewa da muradi mai kyau da kuma cikakkiyar dogara ga Jehobah idan muna son ya amince da bautarmu.—Karanta Misalai 3:5, 6; Ibraniyawa 13:15, 16.

20. Mene ne ‘hasken fuskar Jehobah’ yake nufi?

20 Dauda ya ci gaba: “Waɗansu da yawa suna cewa, Wa za ya nuna mana nagarta? Ya Ubangiji, ka tada hasken fuskarka bisa garemu.” (Zab. 4:6) ‘Hasken fuskar Jehobah’ yana wakiltar amincewar Allah. (Zab. 89:15) Saboda haka, sa’ad da Dauda ya yi addu’a cewa: “Ka tada hasken fuskarka bisa garemu,” yana nufin ‘ka yi mana tagomashi.’ Domin muna dogara ga Jehobah, muna da tagomashinsa da kuma farin ciki sosai yayin da muke yin nufinsa da gaba gaɗi.

21. Wane tabbaci ne muke da shi idan muna saka hannu sosai a aikin wa’azi a yau?

21 Da yake jiran farin cikin da Allah yake ba da wa da ya fi wanda ake yi a lokacin girbi, Dauda ya rera waƙa ga Jehobah: “Ka sa murna a cikin zuciyata, Gaba da tasu lokacin da hatsinsu da ruwan anab nasu sun yawaita.” (Zab. 4:7) Za mu samu tabbacin yin farin ciki idan muna saka hannu a aikin wa’azi. (Luk 10:2) Da yake ‘al’umma mai yawa’ na shafaffu suna yin ja-gora, yanzu muna farin ciki yayin da masu aikin ‘girbi’ suke ƙaruwa. (Isha. 9:3) Shin kana saka hannu sosai a wannan aikin girbi mai sa farin ciki?

Ka Ci Gaba da Yin Cikakkiyar Dogara ga Allah

22. Bisa ga Zabura 4:8, mene ne ya faru da Isra’ilawa sa’ad da suka yi biyayya ga Dokar Allah?

22 Dauda ya kammala wannan zabura da waɗannan kalamai: “Zan kwanta in yi barci da rai a kwance: Gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kana zamshe ni cikin natsuwa.” (Zab. 4:8) Isra’ilawa suna kasancewa da salama da kuma kāriya idan suka kiyaye Dokar Jehobah. Alal misali, ‘Yahuda da Isra’ila sun zauna lafiya’ a lokacin sarautar Sulemanu. (1 Sar. 4:25) Waɗanda suke dogara ga Allah sun shaida salama ko da ƙasashen da ke kusa da su suna gāba da su. Kamar Dauda, muna kwance cikin salama domin Allah yana kāre mu.

23. Me za mu shaida idan muka kasance da cikakkiyar dogara ga Allah?

23 Bari mu ci gaba da yin ƙwazo a hidimar Jehobah. Bari mu kuma yi addu’a da imani kuma mu shaida “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.” (Filib. 4:6, 7) Hakan yana sa mu farin ciki sosai! Za mu kuma fuskanci nan gaba da gaba gaɗi idan muka kasance da cikakkiyar dogara ga Jehobah.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne matsaloli ne Dauda ya fuskanta saboda Absalom?

• Ta yaya Zabura ta uku ta sa mu gaba gaɗi?

• A waɗanne hanyoyi ce Zabura ta huɗu za ta iya ƙarfafa dogararmu ga Jehobah?

• Ta yaya za mu iya amfana don kasancewa da cikakkiyar dogara ga Allah?

[Hoton da ke shafi na 29]

Dauda ya kasance da gaba gaɗi ga Jehobah, har sa’ad da ya gudu don Absalom

[Hotuna da ke shafi na 32]

Kana kasancewa da cikakkiyar dogara ga Jehobah kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba