DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 135-141
Ƙirarmu Abin Al’ajabi Ne
Dauda ya yi bimbini a kan halaye masu kyau na Allah da ke a bayyane a halittunsa. Ya yi amfani da rayuwarsa wajen bauta wa Jehobah da gaba gaɗi.
Yin tunani sosai a kan halittu ya motsa Dauda ya yabi Jehobah:
139:14
“Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa”
139:15
“Yanayina ba a ɓoye yake a gareka ba, sa’ad da aka yi ni a fakaice, sa’ad da aka sifanta ni da gwaninta daga cikin zurfafan duniya”
139:16
“Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu”