Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 12/15 p. 21
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Yakubu Ya Tafi Haran
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yakubu Yana Da Babban Iyali
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 12/15 p. 21

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Mene ne Irmiya yake nufi sa’ad da ya ce Rahila tana kuka don ’ya’yanta?

Littafin Irmiya 31:15, ta ce: “Hakanan Ubangiji ya faɗi: ana jin murya cikin Ramah, makoki, da kuka mai-zafi, Rachel [Rahila] tana kuka domin ’ya’yanta: ta ƙi ta’azantuwa a kan ’ya’yanta, domin sun rasu.”

Rahila ta riga ’ya’yanta biyu mutuwa. Idan muka yi la’akari da hakan, za mu iya ce wataƙila abin da Irmiya ya rubuta shekaru 1,000 bayan rasuwar Rahila ba daidai ba ne.

Yusufu ne ɗan Rahila na fari. (Far. 30:22-24) Ɗanta na biyu shi ne Banyamin kuma ta mutu sa’ad da take haifan sa. Saboda haka, tambayar ita ce: Me ya sa Irmiya 31:15 ta ce Rahila tana kuka don ’ya’yanta “sun rasu”?

Babu shakka, Yusufu ɗanta na fari shi ne mahaifin Manassa da Ifraimu. (Far. 41:50-52; 48:13-20) Bayan haka, kabilar Ifraimu ta zama kabila mai tasiri a dukan kabilun da ke arewacin mulkin Isra’ila kuma ta wakilci dukan kabilu goma. Akasin haka, waɗanda suka fito daga kabilar Banyamin, ɗan Rahila na biyu, tare da ƙabilar Yahuda ne suka kafa mulkin kudancin ƙasar. Saboda haka, Rahila tana iya wakiltar dukan iyaye mata a Isra’ila, wato mulkin arewaci da kuma na kudancin Isra’ila.

A lokacin da aka rubuta littafin Irmiya, Assuriyawa sun riga sun ci kabilu goma na arewacin ƙasar da yaƙi kuma an riga an kai yawancin mutanen bauta. Amma, wataƙila wasu ’yan ƙabilar Ifraimu sun gudu zuwa yankin Yahuda. A shekara ta 607 kafin zamaninmu, Babiloniyawa sun ci masarautar ƙabilu biyu na kudancin Yahuda da yaƙi. Kamar dai an kawo waɗanda aka kama da yawa zuwa Ramah, wani birni mai nisan kilomita 8 daga arewacin Urushalima. (Irm. 40:1) Wataƙila a wannan yankin Banyamin inda aka binne Rahila ne aka kashe wasu. (1 Sam. 10:2) Saboda haka, kukar da Rahila ta yi zai iya wakiltar makokin da ’ya’yan Isra’ila suka yi a kan ’yan ƙabilar Banyamin gaba ɗaya ko kuma waɗanda suke birnin Ramah. Wataƙila hakan yana nufin cewa dukan matan da suka haifi bayin Allah, wato Isra’ilawa sun yi makoki don mutuwar ’ya’yansu ko kuma don an kai su bauta a Babila.

Ko ta yaya, abin da Irmiya ya fada game da makokin da Rahila ta yi annabci ne na abin da ya faru shekaru da yawa bayan haka. Hakan ya faru ne a lokacin da Hiridus yake so ya kashe Yesu da yake yaro. Saboda haka, ya ba da umurni cewa a kashe dukan ’ya’ya maza da suka kai shekara biyu a Bai’talami da ke kudancin Urushalima. A sakamakon haka, waɗannan ’ya’yan sun rasa rayukansu. Babu shakka, iyayen da aka kashe yaransu sun yi kuka sosai! Kamar dai an ji makokin da aka yi a Ramah da ke arewa da Urushalima.—Mat. 2:16-18.

Saboda haka, furucin nan, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta yana wakiltar makokin da iyaye mata suka yi lokacin da aka kashe ’ya’yansu a zamanin Irmiya da kuma a zamanin Yesu. Hakika, za a tayar da waɗanda suka je “ƙasar abokin gāba,” wato waɗanda suka mutu a lokacin tashin matattu.—Irm. 31:16; 1 Kor. 15:26.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba