Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 5 p. 6
  • Akwai Mugayen Mala’iku Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwai Mugayen Mala’iku Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Shin Aljanu Suna Wanzuwa da Gaske?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 5 p. 6
Mugayen mala’iku ko kuma aljanu

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?

Akwai Mugayen Mala’iku Kuwa?

Ƙwarai kuwa. Daga ina suka fito? Ka tuna cewa Allah ya ba mala’iku ’yancin yin abin da suka ga dama. Bayan da aka halicci mace da namiji na farko, wato Adamu da Hauwa’u, sai wani mala’ika ya yi amfani da ’yancinsa a hanyar da ba ta dace ba kuma ya yaudari mutane. Ya yi nasarar sa Adamu da Hauwa’u su yi wa Allah rashin biyayya. (Farawa 3:​1-7; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Littafi Mai Tsarki bai gaya mana sunan mala’ikan ko kuma matsayin da yake da shi a sama kafin ya yi tawaye ba. Amma bayan da ya yi tawaye, sai Littafi Mai Tsarki ya kira shi Shaiɗan, wanda yake nufin “Mai tsayayya” da kuma Iblis wanda yake nufin “Maƙaryaci.”​—Matta 4:8-11.

Abin baƙin ciki shi ne, rashin biyayyar da suka yi bai ƙare a nan ba. Domin a zamanin Nuhu ma, mala’iku da yawa da ba a faɗi adadinsu ba sun “rabu da nasu wurin zama” a sama suka zo duniya. Sun ɗauki jiki irin na ’yan Adam don su riƙa yin lalata da mata. Mala’ikun sun yi watsi da ainihin dalilin da ya sa Allah ya halicce su.​—Yahuda 6; Farawa 6:1-4; 1 Bitrus 3:19, 20.

Mene ne ya faru da waɗannan miyagun mala’ikun? Sa’ad da Allah ya halaka mugaye da rigyawa, mala’ikun sun canza jikinsu zuwa na ruhu kuma suka koma sama. Amma Allah bai bar waɗannan mugayen mala’iku su koma “matsayi nasu ba.” A maimakon haka, ya saka su cikin “duhu” a alamance wanda ake kira Tartarus. (Yahuda 6; 2 Bitrus 2:4) Waɗannan mala’ikun sun koma ƙarƙashin ja-gorancin Shaiɗan Iblis, wato “sarkin aljanu” wanda “yakan mayar da kansa kamar mala’ika na haske.”​—Matta 12:24; 2 Korintiyawa 11:14.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu Kristi ya soma sarauta a Mulkin Allah a sama a shekara ta 1914.a Bayan Kristi ya soma mulki, sai aka kori Shaiɗan da mala’ikun da suke goyon bayansa zuwa duniya. A yau, Shaiɗan da kuma aljanu ne suke haddasa mugunta da lalata da muke gani a duniya.​—Ru’ya ta Yohanna 12:9-12.

Amma rashin ɗa’a da kuma yawan mugunta da muke gani a yau sun nuna cewa an kusan halaka mugayen mala’ikun. Nan ba da jimawa ba, za a ƙulle waɗannan mugayen mala’iku kuma ba za su ƙara haddasa mugunta ba. Bayan Mulkin Allah ya yi sarauta na shekara dubu, za a ba waɗannan mugayen mala’ikun dama ta ƙarshe don su gwada dukan mutane. A ƙarshe, za a halaka su gabaki ɗaya kuma ba za su sake wanzuwa ba.​—Matta 25:41; Ru’ya ta Yohanna 20:1-3, 7-10.

a Don ƙarin bayani game da Mulkin Allah, ka duba babi na 8 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi. Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba