Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 6 pp. 12-14
  • Littafi Mai Tsarki​—Me Ya Sa Akwai Juyi Dabam-Dabam?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki​—Me Ya Sa Akwai Juyi Dabam-Dabam?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AINIHIN LITTAFI MAI TSARKI
  • JUYIN SEPTUAGINT NA HELENANCI
  • JUYIN LATIN VULGATE
  • AN CI GABA DA FITAR DA SABABBIN JUYI
  • Jehobah, Allah Ne Mai Ma’amala da Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Wane Irin Littafi Ne Baibul?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • “Maganar Ubangiji Za ta Tsaya Har Abada”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 6 pp. 12-14
Littafi Mai Tsarki dabam-dabam

Littafi Mai Tsarki​—Me Ya Sa Akwai Juyi Dabam-Dabam?

Me ya sa ake da juyin Littafi Mai Tsarki da yawa a yau? Idan aka fitar da sabon juyi, kana ganin juyin zai taimaka maka ne ko zai hana ka fahimtar Littafi Mai Tsarki? Yin bincike a kan tarihin waɗannan juyin za su taimaka maka ka yi amfani da su yadda ya dace.

Amma wane ne ya rubuta ainihin Littafi Mai Tsarki kuma yaushe ya yi hakan?

AINIHIN LITTAFI MAI TSARKI

An raba Littafi Mai Tsarki zuwa kashi biyu. Kashi na ɗaya yana da littattafai guda 39 kuma yana ɗauke da “zantattukan Allah.” (Romawa 3:2) Allah ya ja-goranci wasu maza masu aminci da ruhu mai tsarki don su rubuta waɗannan littattafan. Sun yi hakan daga shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu zuwa 443, wato wajen shekaru 1,100 ke nan. Sun rubuta yawancin littattafan a Ibrananci, shi ya sa ake kiransa Nassosin Ibrananci ko kuma Tsohon Alkawari.

Kashi na biyu yana da littattafai guda 27 kuma shi ma yana ɗauke da “maganar Allah.” (1 Tasalonikawa 2:13) Allah ya ja-gorancin mabiyan Yesu Kristi su rubuta waɗannan littattafan daga shekara ta 41 bayan haihuwar Yesu zuwa 98, wato wajen shekaru 60 ke nan. Sun rubuta yawancin littattafan da Helenanci, shi ya sa ake kiransa Nassosin Helenanci ko kuma Sabon Alkawari.

Waɗannan littattafan guda 66 ne ainihin littattafan da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma saƙon da ke ciki daga Allah ne zuwa ga ’yan Adam. Amma me ya sa aka yi juyin Littafi Mai Tsarki dabam-dabam? Ga wasu dalilai uku da suka sa aka yi hakan.

  • Don mutane su iya karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu.

  • Don a cire kuskuren da masu kofan Littafi Mai Tsarki suka yi kuma a maido da ainihin saƙon da ke cikinsa.

  • Don a canja tsofaffin kalmomin da aka daina amfani da su a yaren.

Ka yi la’akari da yadda waɗannan dalilan suka sa aka fassara wasu juyin Littafi Mai Tsarki guda biyu.

JUYIN SEPTUAGINT NA HELENANCI

Shekaru 300 kafin a haifi Yesu, wasu malaman Yahudawa sun soma fassara Nassosin Ibrananci zuwa Helenanci. Ana kiran wannan juyin Septuagint na Helenanci. Me ya sa aka fitar da wannan juyin? A lokacin, Yahudawa da yawa suna jin Helenanci fiye da Ibrananci. Don haka, wannan juyin zai taimaka musu su san “littattafai masu-tsarki.”​—2 Timotawus 3:15.

Ban da haka ma, juyin Septuagint ya taimaka wa waɗanda ba Yahudawa ba su san koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Wani farfesa mai suna W. F. Howard ya ce: “Daga tsakiyar ƙarni na farko, yawancin Cocin Kiristoci suna amfani da wannan juyin, kuma da shi ne malamansu suke zuwa majami’u dabam-dabam don su ‘tabbatar wa mutane daga cikin nassosi cewa Yesu ne Almasihu.’ ” (Ayyukan Manzanni 17:​3, 4; 20:​20, Littafi Mai Tsarki) Wani mai binciken Littafi Mai Tsarki mai suna F. F. Bruce ya ce: “Wannan dalilin ne ya sa Yahudawa da yawa suka daina amfani da juyin Septuagint.”

Da almajiran Yesu suka ci gaba da rubuta sauran littattafan da ke Nassosin Helenanci, sun haɗa littattafan da juyin Septuagint na Ibrananci. Wannan ne ya zama cikakken Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau.

JUYIN LATIN VULGATE

Wajen shekara 300 da kammala Littafi Mai Tsarki, wani limamin addini mai suna Jerome ya fitar da juyin Littafi Mai Tsarki a yaren Latin kuma ana kiran juyin Latin Vulgate. Tun da yake da akwai juyin Latin da yawa, me ya sa ya fitar da wannan sabon juyin? Littafin nan The International Standard Bible Encyclopedia ya ce, Jerome yana so ne ya gyara “kuskuren da aka yi, ya kuma cire ƙarin bayanan da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki.”

Jerome ya gyara yawancin kuskuren da aka yi. Amma da shigewar lokaci, limaman coci sun kafa wata dokar da ba ta dace ba. Sun ce juyin Latin Vulgate ne kaɗai Littafi Mai Tsarkin da za a riƙa amfani da shi, kuma an yi shekaru da yawa ana bin wannan dokar! A lokacin, mutane da yawa ba su iya yaren Latin ba. Don haka, juyin Latin Vulgate bai taimaka wa mutane su fahimci Littafi Mai Tsarki ba.

AN CI GABA DA FITAR DA SABABBIN JUYI

Da shigewar lokaci, mutane sun ci gaba da fitar da sababbin juyin Littafi Mai Tsarki kamar juyin Syriac Peshitta, wanda aka wallafa a kusan ƙarni na biyar bayan haihuwar Yesu. Amma sai a ƙarni na 14 ne aka soma fassara Littafi Mai Tsarki a yaruka dabam-dabam.

A ƙarshen ƙarni na 14 ne John Wycliffe da ke Ingila ya soma fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci. Ya yi hakan don mutanen ƙasar su iya fahimtar Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai Johannes Gutenberg ya ƙera wata na’urar buga littattafai. Da wannan na’urar, an buga sababbin juyin Littafi Mai Tsarki kuma an rarraba su a yaruka da yawa a Turai.

Da aka ci gaba da fitar da juyi na Turanci dabam-dabam, sai wasu suka ce bai kamata a riƙa fitar da juyi dabam-dabam a yare iri ɗaya ba. Wani limamin addini a ƙarni na 18 mai suna John Lewis ya rubuta cewa: “Akwai wasu kalmomi a yaruka da aka daina amfani da su, don haka, ana bukatar a canja juyin da ke ɗauke da tsofaffin kalmomin zuwa kalmomin da mutane suke amfani da su.”

A yau, akwai abubuwa da yawa da za su taimaka wa masu binciken Littafi Mai Tsarki su gyara tsofaffin fassarar da aka yi. Suna da cikakken bayanai a kan yarukan da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kuma suna da rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā da aka samo kwana-kwanan nan. Waɗannan bayanan suna taimaka musu su san ainihin saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Saboda haka, sababbin juyin Littafi Mai Tsarki da ake fitar da su suna da amfani sosai. Ko da yake akwai wasu juyin da muke bukatar mu yi hankali da su. Amma, idan mutanen da suke ƙaunar Allah ne suka fitar da sabon juyin Littafi Mai Tsarki, za mu amfana daga aikinsu sosai.

Idan kana so ka karanta Littafi Mai Tsarki a yarenku a intane ko kuma a wuyarka, ka shiga dandalin www.pr418.com. Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > LITTAFI MAI TSARKI, ko kuma ka yi scan ɗin wannan alamar

SUNAN ALLAH A LITTAFI MAI TSARKI

Sunan Allah a rubuce-rubuce na Septuagint a zamanin Yesu

Sunan Allah a juyin Septuagint da aka yi amfani da shi a zamanin Yesu.

A cikin juyin New World Translation of the Holy Scriptures, an saka sunan Allah, wato Jehobah a Nassosin Ibrananci da kuma Helenanci. Yawancin juyin Littafi Mai Tsarki a yau ba su yi hakan ba. Maimakon haka, sun yi amfani da kalmar nan “Ubangiji.” Wasu mafassaran sun ce sun yi hakan ne don ba a yi amfani da harufan nan huɗu na Ibrananci, wato YHWH da ke wakiltar sunan Allah a juyin Septuagint na Helenanci ba. Amma hakan gaskiya ne?

A tsakiyar ƙarni na 20, an samo wasu tsofaffin juyin Septuagint da aka yi amfani da su a zamanin Yesu. Littattafan suna ɗauke da suna Allah a baƙaƙen Ibrananci. Wataƙila bayan wasu shekaru ne masu kofan littafin suka cire wannan sunan kuma suka saka Kyʹri·os da ke nufin “Ubangiji” a Helenanci. Amma a juyin New World Translation, an saka sunan Allah yadda yake tun asali.

AN CANJA SAƘON DA KE LITTAFI MAI TSARKI NE?

Littafin Tekun Gishiri da ke dauke da littafin Ishaya

Littafin Tekun Gishiri da ya yi shekara 2,000. Yana ɗauke da littafin Ishaya. Bayanan da ke ciki kusan ɗaya ne da Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau

Hakika, mutanen da suka kofe Littafi Mai Tsarki sun yi kuskure. Amma kuskuren da suka yi bai canja saƙon Littafi Mai Tsarki ba. Littafin nan Our Bible and the Ancient Manuscripts ya ce: Waɗannan kurakuren ba su canja “ainihin koyarwar Kiristoci ba.”

Yahudawan da suka kofe Littafi Mai Tsarki ba su yi kuskure sosai ba. Littafin nan Second Thoughts on the Dead Sea Scrolls ya ce: “Marubuta Yahudawa a ƙarni na farko sun mai da hankali sosai wajen kofe Nassosin Ibrananci daidai yadda yake.”

Alal misali, an ga wani littafin Ishaya a cikin Littattafan Tekun Gishiri kuma wannan littafin ya girmi wanda muke da shi da shekara 1,000. Mene ne alaƙar da ke tsakaninsa da wanda muke da shi a yau? Littafin nan The Book. A History of the Bible ya ce: “A wasu wurare, an cire kalmomin da ba a bukata, amma an bar su a wasu wurare.”

Yanzu an gane yawancin kuskuren da masu kofe-kofe suka yi kuma an gyara su. Littafin nan The Books and the Parchments ya ce: “A cikin dukan littattafan dā, Sabon Alkawari ne za a iya ba da hujjojin da suka nuna cewa saƙon da ke cikinsa daidai ne.”

Littafin nan The Book. A History of the Bible ya ce: “Kiristoci suna bukatar su kasance da tabbaci cewa an fassara saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki daidai yadda yake duk da cewa an kofe shi kuma an buga shi sau da yawa.”

Shin, an canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne? A’a!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba