Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp19 Na 2 p. 3
  • Idan Matsaloli Sun Sa Ka Gaji da Rayuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Idan Matsaloli Sun Sa Ka Gaji da Rayuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Me Za Ka Yi Idan Ka Gaji da Rayuwa?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Sa’ad da Aka Mana Rasuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Hakika Rayuwa Tana da Amfani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
wp19 Na 2 p. 3
Wata mata tana kuka a wurin aiki

Idan Matsaloli Sun Sa Ka Gaji da Rayuwa

RAYUWA akwai daɗi idan kome yana tafiya daidai. Amma, a wasu lokuta matsaloli sukan sa rayuwa ta yi wuya.

Alal misali, wata mai suna Sallya a ƙasar Amirka, wadda ta rasa mafi yawa daga cikin kayayyakinta sanadiyyar wata guguwa da aka yi, ta ce: “Na ga kamar matsalar ta fi ƙarfina kuma ba zan iya jimrewa ba.”

Wani abin da yake sa mu baƙin ciki kuma shi ne sa’ad da aka yi mana rasuwa. Wata mai suna Janice a Ostareliya, ta bayyana cewa: “Sa’ad da ’ya’yana biyu suka mutu, na yi baƙin ciki sosai. Na yi addu’a ga Allah cewa: ‘Ya Allah, na gaji da rayuwa ba zan iya jimrewa kuma ba! Gwamma in mutu.’”

Wani kuma mai suna Daniel, ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da matarsa ta ci amanarsa. Ya bayyana cewa: “Sa’ad da matata ta ci amanata, na ji zafi sosai kamar dai an soka min wuka a zuciyata. Abin da ta yi ya sa na daɗe ina baƙin ciki.”

Wannan Hasumiyar Tsaro za ta bayyana amfanin rayuwa ko a lokacin da

  • Bala’i ya abko mana

  • Aka yi mana rasuwa

  • Aka ci amanarmu

  • Muke fama da rashin lafiya

  • Matsaloli suka sa ka rasa na yi

Da farko, ta yaya za mu jimre sa’ad da bala’i ya abko mana?

a An canja wasu sunayen a talifofin nan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba