Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp19 Na 2 pp. 4-5
  • Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA YANA SA MU KASANCE DA BEGE
  • A Shirye Kake?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Maza da Suke Yawan Damuwa
    Karin Batutuwa
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
wp19 Na 2 pp. 4-5
Wasu mutane biyu suna zaune a tarkacen wani gida da ya rushe

Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana

Andrew, daga ƙasar Saliyo ya ce: “Da farko mun yi baƙin ciki sosai domin zaftarewar ƙasa da ambaliyar ruwa ta hallaka dukiyarmu gaba ɗaya.”

David daga Virgin Islands ya ce: “Bayan da aka yi wata guguwa da iska, mun koma gida kuma muka tarar da cewa ba abin da ya rage. Mun yi baƙin ciki sosai kuma ’yata ta sunkuya tana ta kuka.”

IDAN bala’i ya taɓa abko maka, wataƙila hakan ya sa ka rikice, ka damu kuma ka kasa yin barci kamar yadda ya faru da mutane da yawa. Yawancin mutanen da bala’i ya abko musu sukan ƙaraya kuma su gaji da rayuwa.

Idan kai ma ka rasa dukiyarka sanadiyar wani bala’i, hakan zai iya sa ka ji cewa ka gaji da jimrewa ko kuma ka ji cewa rayuwa ba ta da wani amfani. Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa rayuwa tana da amfani kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA YANA SA MU KASANCE DA BEGE

Littafin Mai-Wa’azi 7:8 ya ce: “Gwamma ƙarshen abu da farawarsa.” Idan bai jima da bala’i ya same ka ba, za ka iya jin cewa rayuwarka ta taɓarɓare. Amma idan ka jimre kuma ka yi aiki da ƙwazo, za ka iya kyautata rayuwarka kuma abubuwa za su yi kyau kamar yadda suke a dā.

Littafi Mai Tsarki ya ce lokaci yana zuwa da “ba za a sake jin muryar kuka . . . ko ƙarar kukan azaba” ba. (Ishaya 65:19) Hakan zai faru a lokacin da aka mai da duniya aljanna a ƙarƙashin Mulkin Allah. (Zabura 37:​11, 29) Bala’i ba zai sake abko ma kowa ba. Duk wani baƙin ciki ko ɓarnar da bala’i ya janyo mana za su shuɗe domin Allah Mai Iko Duka ya yi alkawari cewa: “Ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba, tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.”​—Ishaya 65:17.

Ka yi la’akari da wannan: Mahaliccinmu yana shirin ba mu “bege mai kyau a ƙarshe,” wato begen yin rayuwa mai kyau a Mulkin Allah. (Irmiya 29:11) Shin sanin wannan gaskiyar za ta sa ka ɗauki rayuwa da muhimmancin kuwa? Matar da muka yi maganar ta a talifi na farko mai suna Sally, ta ce, “Yin tunani a kan abubuwan da Mulkin Allah zai yi mana a nan gaba zai taimaka mana mu manta da matsalolinmu kuma mu mai da hankali a kan abubuwan da suke faruwa a yanzu.”

Muna ƙarfafa ka ka koyi wasu abubuwan da Mulkin Allah zai yi wa ’yan Adam. Yin hakan zai ba ka tabbaci cewa duk da bala’in da ya abko maka, rayuwa za ta ci gaba da kasance da muhimmanci a gare ka yayin da kake jiran lokacin da bala’i ba zai sake abko maka ba. Ko a yanzu ma, Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarwari masu amfani da za su taimaka maka ka jimre a lokacin da bala’i ya abko maka. Bari mu ga kaɗan daga cikin shawarwarin.

Nassosin da Za Su Iya Taimakawa

Ka riƙa hutawa da kyau.

“Gwamma kaɗan a hannu ɗaya cike da kwanciyar rai, da mai yawa a hannu biyu cike da famar aiki, wannan ma ƙoƙarin kamun iska ne.”​—Mai-Wa’azi 4:6.

Masu bincike sun gano cewa “idan mutum baya samun isashen barci a lokacin da yake fama da baƙin ciki, hakan zai iya ƙara masa damuwa kuma zai shafi lafiyar jikinsa.” Saboda haka, isashen barci yana da muhimmanci.

Ka bayyana yadda kake ji.

“Damuwa a zuciya takan hana mutum sakewa, amma kalmar ƙarfafawa takan faranta rai.”​—Karin Magana 12:25.

Ka gaya ma ɗan’uwa ko abokin arziki abin da yake damun ka. Za su saurare ka su kuma ƙarfafa ka. Ƙari ga haka, za su ba ka shawarwari da za su taimaka maka.a

Ka yi tunani a kan lokacin da kome zai yi kyau.

“Amma bisa ga alkawarin Allah, muna marmarin sabon sammai da sabuwar ƙasa, inda adalci zai kasance kullum.”​—2 Bitrus 3:13.

a Mutumin da ya daɗe yana fama da baƙin ciki zai iya bukaci ganin likita don taimako.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba