RAYUWAR KIRISTA
A Shirye Kake?
Idan bala’i ya abka ma yankinku, a shirye kake? Girgizar ƙasa ko mahaukaciyar guguwa ko wutar daji ko kuma ambaliyar ruwa za su iya aukowa ba zato ba tsammani kuma su yi ɓarna sosai. Ban da haka ma, hari daga ’yan ta’adda da yaƙi da kuma wasu cututtuka za su iya faruwa ba shiri. (M. Wa 9:11) Saboda haka, bai kamata mu ɗauka cewa irin waɗannan abubuwan ba za su faru a wurin da muke ba.
Zai dace kowannenmu ya kasance a shirye don bala’i. (K. Ma 22:3) Ko da yake ƙungiyar Jehobah tana taimakawa sa’ad da bala’i ya abko, kowannenmu yana da hakkin kasancewa a shirye.—Ga 6:5.
KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALA’I TA AUKU? SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Ta yaya dangantaka mai kyau da Jehobah za ta taimaka mana sa’ad da bala’i ya abku?
Me ya sa yake da muhimmanci mu . . .
• ba dattawa lambar wayarmu da adireshinmu kafin bala’i ya abko da kuma bayan hakan?
• kasance da jaka ko akwatin gaggawa?—g17.5-E 6
• bincika irin bala’in da za su iya aukuwa a yankinmu da matakan da ya kamata mu ɗauka?
A waɗanne hanyoyi uku ne za mu taimaka ma waɗanda bala’i ya abko musu?