Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Mayu p. 9
  • Ku Kasance a Shirye a Ƙarshen “Kwanakin Ƙarshe”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Kasance a Shirye a Ƙarshen “Kwanakin Ƙarshe”
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • A Shirye Kake?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Kana Shirye don Lokacin Tashin Hankali?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Kun Yi Shiri don Aukuwar Bala’i?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Mayu p. 9
Wata iyali tana shirya abinci da ruwa da kuma wasu abubuwa da za su yi amfani da su idan yanayin gaggawa ya taso.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance a Shirye a Ƙarshen “Kwanakin Ƙarshe”

Abubuwa za su yi muni sosai yayin da muke rayuwa a ƙarshen “kwanakin ƙarshe.” (2Ti 3:1; Mt 24:8) A lokacin da bala’i ya abko, bayin Jehobah suna samun umurnin da zai ceci rayukansu a kan lokaci. Za mu iya ceton rayukanmu idan mun kasance da shiri tun yanzu.​—Lu 16:10.

  • Ka yi kusa da Allah: Ka riƙa karanta da kuma nazarin Littafin Mai Tsarki. Ka koyi hanyoyin yin wa’azi dabam-dabam. Kada ka ji tsoro idan an ware ka na ɗan lokaci daga ’yan ikilisiyarku. (Ish 30:15) Ka tuna cewa ba za a iya ware ka daga Jehobah da kuma Yesu ba.​—od-E 176 sakin layi na 15-17

  • Ka shirya kanka: Ban da jaka ko akwatin gaggawa, kowannenmu zai iya ajiye abinci da ruwa da magani da dai sauransu saboda yanayin gaggawa da zai iya bukaci mutum ya yi zama a wani wuri na ɗan lokaci.​—K. Ma 22:3; g17.5-E 4, 6

KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALA’I TA AUKU? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘A Shirye Kake Idan Bala’i ta Auku?’ Wani dan’uwa yana karanta Littafi Mai Tsarki.

    Ta yaya dangantaka mai kyau da Jehobah za ta taimaka mana sa’ad da bala’i ya abku?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘A Shirye Kake Idan Bala’i ta Auku?’ Wani hoto da ya nuna jakar gaggawa da lambar waya da adireshi da kuma inda wata iyali za su hadu idan yanayin gaggawa ya taso.

    Me ya sa yake da muhimmanci mu . . .

    • ba dattawa lambar wayarmu da adireshinmu?

    • kasance da jaka ko akwatin gaggawa?

    • bincika irin bala’in da za su iya aukuwa a yankinmu da matakan da ya kamata mu ɗauka?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘A Shirye Kake Idan Bala’i ta Auku?’ Hotunan da ke nuna hanyoyin da za mu taimaka ma wadanda bala’i ya shafa. Na 1. Wani dan’uwa yana addu’a a madadin su. Na 2. Wasu ’yan’uwa suna taimakawa da kayan agaji. Na 3. Wani dan’uwa yana ba da gudummawa don tallafa wa aikin da ake yi a fadin duniya.

    A waɗanne hanyoyi uku ne za mu taimaka ma waɗanda bala’i ya abka musu?

KA TAMBAYI KANKA, ‘Waɗanne darussa ne annobar korona bairus ta koya mana game da kasancewa da shiri?’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba