Kun Yi Shiri don Aukuwar Bala’i?
1. Me ya sa yana da kyau mu kasance a shirye don aukuwar bala’i?
1 A Kowace shekara, girgizar ƙasa da ambaliyar ruwa da tashe-tashen hankula da bala’i iri-iri suna shafan miliyoyin mutane a faɗin duniya har da ’yan’uwanmu Shaidun Jehobah. Ta’addanci da faɗa da makamai abubuwa ne da za su iya faruwa a ko’ina.
2. Wane alkawari mai ban ƙarfafa ne Jehobah ya yi wa bayinsa?
2 Ko da yake yanayin duniya yana ƙara taɓarɓarewa, bayin Allah ba sa razana, kuma ba sa tsoro. Mun san abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa kuma mun san cewa muna ƙarshen kwanaki domin mu ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne. (2 Tim. 3:1, 13) Allahnmu Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai kāre bayinsa daga duk wani abin da zai ɓata dagantakarmu da shi. Alal misali, zai taimaka mana mu tsira daga bala’i mai tsanani da zai shafi dukan duniya ba da daɗewa ba, wato, ƙunci mai girma. Daga baya, waɗanda suka tsira daga wannan bala’in za su ji daɗin rayuwa a ƙarƙashin Mulkin Allah har abada. (Isa. 14:7) Amma a yanzu, dole ne mu riƙa fama da bala’i. Zai dace mu kasance a shirye tun da bala’i, da masifun da ’yan Adam suke haddasawa za su iya shafanmu ba zato.—Mis. 21:5.
3. Idan yanayi yana daɗa muni, wane ne zai yanke shawara ko a ƙaura ko a’a?
3 Tun da Wuri: A wani lokaci hukuma tana iya faɗakar da mutane game da bala’in da ke tafe. Zai dace a mai da hankali ga wannan faɗakarwar. (Mis. 22:3) A irin wannan yanayin, dattawa za su yi ƙoƙari su tuntuɓi dukan ’yan’uwan da ke cikin ikilisiya kuma su taimaka musu a yin shirye-shiryen da ake bukata. Wajibi ne dattawa su yi hattara game da abubuwan da ke faruwa a yanki don hakan zai sa su ba masu shela shawara mai kyau. Amma ba dattawa ne za su tsai da shawara wa ’yan’uwa ba kuma ba wani dattijon da zai tilasta wa ’yan’uwa su bi ra’ayinsa a kan wannan batun. Saboda haka, kada kowanne ɗan’uwa ya jira sai dattawa na yankin sun ba da izini cewa ya ƙaura ko kuma ya jira sai an samu ja-gora daga ofishin reshe kafin ya ɗauki mataki sa’ad alamu sun nuna cewa bala’i zai auku ko kuma za a yi tashin hankali. Idan yanayi ya yi muni, kowa yana da ’yancin yanke wa kansa shawara ko zai ƙaura ko a’a. Kada a matsa wa wani ya ci gaba da zama a inda yake, kuma kada a matsa wa wani ya ƙaura zuwa wani wuri sa’ad da bai shirya yin haka ba.—Gal. 6:5.
4. Mene ne ya dace mu yi sa’ad da aka yi tashin hankali ko kuma ta’addanci a yankinmu?
4 Tashin hankali da kuma ta’addanci suna iya aukuwa ba zato ba tsammani. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawara cewa mu riƙa nuna basira kuma mu yi hattara a kowane lokaci. (Mis. 27:12) Saboda haka, ya kamata mu riƙa lura da abubuwan da ke faruwa a yankinmu. Muna son kowane ɗan’uwa ya ɗauki mataki don ceton rayuka idan bukata ta kama. Yin hakan zai bukaci ƙaura daga inda ake tashin hankali ko kuma wurare masu haɗari zuwa wani wuri idan hakan zai yiwu, sai bayan abubuwa sun lafa. Wasu sun riga sun ɗauki wannan matakin duk da cewa sun yi hasarar dukiyoyinsu, kuma muna yaba musu. Ya kamata mu tuna cewa rai ya fi dukiya tamani. (Luk 12:15) Idan saboda abin duniya ɗan’uwa ya ƙi tashi daga inda akwai haɗari, ya yi ɓatan basira.
5. Ta yaya za mu ba wa dattawa haɗin kai idan muna zama a wurin da aka cika tashin hankali?
5 Idan ’yan ikilisiya suna zama a inda ake yawan tashin hankali, ko kuma idan ana ganin cewa da alama za a yi tashin hankali ko hargitsi, dattawa za su iya gaya wa masu shela su ba da suna da kuma lambar wayar danginsu ko kuma abokinsu da yake zama a wani wuri wanda za a iya tuntuɓa a lokacin gaggawa. Hakan zai taimaka wa dattawa su san inda waɗanda suka bar yankin saboda tashin hankali suke. Dattawa za su iya shirya wa ’yan ikilisiya abubuwa kamar sunayen abubuwan da za a bukata a lokacin gaggawa waɗanda ya kamata a kasance da su, shirin yadda za a tsere sa’ad da bala’i ya auku da kuma yadda za a taimaka wa marasa lafiya da naƙasassu. Yana da muhimmanci a ba wa dattawa haɗin kai sa’ad da suke waɗannan shirye-shiryen.—Ibr 13:17.
6. (a) Mene ne ya kamata mu yi idan bala’i ta auku a yankinmu? (b) Me ya sa ya kamata mu ba wa dattawa ainihin adireshinmu da lambar wayarmu?
6 Bayan Aukuwar Bala’i: Me ya kamata ku yi idan bala’i ya auku ko kuma an yi tashin hankali a yankinku? Ku tabbata cewa kun tanadar da abubuwan da iyalinku za su bukata nan da nan. Ku taimaka wa waɗanda abin ya shafa, daidai ƙarfinku. Ku yi ƙoƙarin tuntuɓar mai kula da hidima a rukuninku ko kuma wani dattijo ba tare da ɓata lokaci ba. Yin hakan yana da muhimmanci ko da a ce kuna lafiya kuma ba ku bukatar taimako. Idan kuna bukatar wani taimako, ku tabbata cewa ’yan’uwanku za su yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka maku. (1Ko 13:4, 7) Ku tuna cewa Jehobah yana sane da yanayinku; ku dogara da shi don ya taimake ku. (Za 37:39; 62:8) Ku riƙa lura da yanayin mutane saboda ku ƙarfafa su da magana mai daɗi da kuma saƙon da ke Littafi Mai Tsarki. (2Ko 1:3, 4) Dattawa za su yi ƙoƙari su tuntuɓi duka waɗanda ke cikin ikilisiya don su tabbata ko suna lafiya kuma domin su ba da taimako idan da bukata. Idan dattawa ba su da ainihin lambar waya ko kuma adireshin ’yan ikilisiya, ba za su iya tanadar da taimako da wuri ba. Saboda haka, yana da kyau ku ba wa sakatare da kuma mai kula da hidima a rukuninku ainihin adireshinku da lambar wayarku.
7. Ta yaya za mu ƙarfafa dagantakarmu da Jehobah a inda muka fake?
7 Sa’ad da Muka Nemi Mafaka: Yana da muhimmanci mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma mu kasance da bangaskiya sosai a duk inda muka fake sa’ad da ake tashin hankali. Idan halartar taro a Majami’ar Mulki a irin wannan yanayin zai kasance da haɗari, masu shela za su iya yin taro a ƙananan rukuni, wataƙila a rukuninsu na wa’azi kuma su tattauna abin da za a tattauna a taron ikilisiya a makon. Idan hakan ba zai yiwu ba, za ku iya tattauna batun sa’ad da kuke Bauta ta Iyali da yamma, bayan abubuwa sun lafa, sai a koma halartar taro kamar yadda aka saba. A wannan lokacin, dukan ’yan’uwa su ci gaba da yin wa’azi ga waɗanda za su so su saurari saƙon “bishara ta alheri” amma su yi hankali sa’ad da suke yin haka. (Ish 52:7) A ƙarshen wata, kowane mai shela ya nemi yadda zai aika rahotonsa kai tsaye zuwa ga sakatare ko kuma mai kula da rukuninsu na wa’azi ko mataimakinsa. Alal misali, za ku iya aika rahotonku ta waya ko ta saƙon waya. Ta hakan, muna cika aikinmu na ‘yin wa’azin kalmar ko da dama, ko ba dama.’—2 Tim. 4:2.
8. Ta yaya aukuwar bala’i da kuma tashin hankali suke shafanmu?
8 Duk da cewa aukuwar bala’i da kuma tashin hankali yakan sa mu damuwa sosai, muna da tabbaci cewa za a samu kwanciyar hankali a nan gaba. Duka bala’i za su shuɗe. (R. Yoh 21:4) Kafin wannan lokacin, muna bukata mu ɗauki matakai da suka dace kuma mu kasance da shiri domin lokacin masifa yayin da muke yi wa mutane wa’azin bishara da himma.
[Akwati a shafi na 6]
Matakan da Za Mu Ɗauka Saboda Bala’i:
• Ku tattara takardu masu muhimmanci wuri ɗaya don ku iya guduwa da su idan bala’i ya auku.
• Ku harhaɗa abubuwan da za ku bukata a lokacin gaggawa na tsawon kwana uku zuwa biyar. Waɗannan abubuwa sun haɗa da abinci da magani da ruwan sha kuma ku ajiye su da kyau don ku iya ɗaukawa sa’ad da kuke guduwa.
• Ku kasance da shiri don tsere wa bala’i kuma ku san inda za ku fake.
• Ku bi umurnin dattawa da na hukuma.