Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Mayu p. 5
  • Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • A Shirye Kake?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Ku Kasance a Shirye a Ƙarshen “Kwanakin Ƙarshe”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Kana Shirye don Lokacin Tashin Hankali?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Mayu p. 5

RAYUWAR KIRISTA

Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?

Ba ma mamaki saꞌad da abubuwan da ke faruwa a duniya suka taɓarɓare tattalin arziki. Me ya sa? Domin muna rayuwa a ƙarshen kwanaki na ƙarshe kuma Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu kada mu dogara ga “arziki marar tabbata.” (1Ti 6:17; 2Ti 3:1) Mene ne abin da ya faru da Sarki Jehoshafat ya koya mana game da kasancewa a shirye don faɗuwar tattalin arziki?

Jehoshafat ya dogara ga Jehobah saꞌad da maƙiyansa suka yi barazanar yaƙi da shi. (2Tar 20:​9-12) Ƙari ga haka, ya yi shirye-shirye ta wajen gina katanga da kuma kafa barikin sojoji da yawa. (2Tar 17:​1, 2, 12, 13) Kamar Jehoshafat, zai dace mu dogara ga Jehobah kuma mu yi shirye-shiryen fuskantar yanayoyi masu wuya.

ABIN DA ZA MU IYA YI A LOKACIN FAƊUWAR TATTALIN ARZIKI

Ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah: Ku gamsu da abin da kuke da shi kuma ku dogara ga Jehobah cewa zai biya bukatunku na yau da kullum. (Mt 6:26; 1Ti 6:8) Ku kudiri niyya cewa ba za ku daina bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba don ku biya waɗannan bukatun. (Ro 2:21) Ku shirya yadda za ku ci gaba da samu da kuma karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu idan aka ɗauke wuta ko kuma Intane. Ku ajiye wasu littattafai kuma idan zai yiwu ku saukar da littattafai a naꞌurorinku tun da wuri.

Ku shirya abin biyan bukatunku: Ku yi ƙoƙari ku biya bashin da kuka ci kuma ku rage yawan kashe kuɗi kafin faɗuwar tattalin arziki. (K. Ma 22:7) Idan zai yiwu ku tara abinci da wasu kayayyaki. Wasu suna iya shuka kayan lambu don su rage kashe kuɗi.

KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALAꞌI TA AUKU? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

Hotuna daga bidiyon “A Shirye Kake Idan Balaꞌi Ta Auku?” An nuna Littafi Mai Tsarki, jakar gaggawa da babbar waya da kuma masu gine-gine.
  • Mene ne za mu iya yi don mu yi shiri kafin balaꞌi ta auku?

Hotuna daga bidiyon “A Shirye Kake Idan Balaꞌi Ta Auku?” ꞌYanꞌuwa sua taimakawa a wajen da aka yi balaꞌi. suna gini da kuma sauke kaya daga wani tirela.
  • Ta yaya za mu kasance a shirye don mu taimaka wa mutane?

MAƘASUDI

A lokacin da kuke ibada ta iyali, ku tattauna abin da ke Awake! Na 1 2022. Kuma ku tattauna ƙarin abubuwan da za ku iya yi don ku kasance a shirye kafin balaꞌi ta auku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba