Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp19 Na 3 pp. 12-13
  • Me Za Ka Yi Don Ka Ji Dadin Rayuwa a Nan Gaba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Za Ka Yi Don Ka Ji Dadin Rayuwa a Nan Gaba?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ALLAH YA CE ZAI MAYAR DA RAYUWA TA ZAMA YADDA YA KAMATA
  • YESU YA NUNA MISALIN ABUBUWAN DA ZAI YI WA MASU ADALCI
  • YADDA ZA KA SAMI HANYAR RAI MAFI INGANCI
  • ABU NA FARKO DA YA KAMATA KA YI
  • Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Abubuwan da Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ku Ci-gaba da Saurarar Sa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Bauta da Allah Ya Amince da Ita
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
wp19 Na 3 pp. 12-13
Daya daga cikin ’yan kimiyya da aka yi maganarsu a baya yana karanta Littafi Mai Tsarki

Me Za Ka Yi Don Ka More Rayuwa A Nan Gaba?

RAYUWA a yau ba yadda Allah yake so ta zama ba ne. Ya kamata masu yin koyi da Mahaliccinmu, da masu bin ja-gorancinsa, da masu son mulkinsa ne kaɗai su kasance a duniya. Allah ya so ’yan Adam su haɗa kai su yi zaman tare a matsayin iyalai, su koyi sabbin abubuwa kuma su sa duniya ta zama aljanna.

ALLAH YA CE ZAI MAYAR DA RAYUWA TA ZAMA YADDA YA KAMATA

  • ‘Zai tsai da yaƙe-yaƙe a dukan duniya.’​—Zabura 46:9.

  • ‘Lokaci ya yi da za a hallaka masu hallaka duniya!’​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18.

  • “Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’”​—Ishaya 33:24.

  • “Mutanena da na zaɓa za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”​—Ishaya 65:22.

Ta yaya Allah zai cika waɗannan alkawuran? Allah ya naɗa Ɗansa, Yesu ya yi sarauta daga sama bisa duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce wannan gwamnatin, ita ce Mulkin Allah. (Daniyel 2:44) Game da Yesu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah zai ba shi kujerar mulkin. . . . Zai yi mulki.”​—Luka 1:​32, 33.

A lokacin da Yesu yake duniya, ya yi ayyuka masu ban mamaki da yawa da suka nuna cewa idan ya zama Sarki, zai inganta rayuwarmu sosai.

YESU YA NUNA MISALIN ABUBUWAN DA ZAI YI WA MASU ADALCI

  • Ya warkar da cututtuka iri-iri, kuma hakan ya nuna cewa zai kawar da ciwo daga duniya.​—Matiyu 9:35.

  • Ya dakatar da guguwa a teku, kuma hakan ya nuna cewa zai kāre mutane daga bala’o’i kamar ambaliya da guguwar iska mai ƙarfi da dai sauransu.​—Markus 4:​36-39.

  • Ya ciyar da dubban mutane, kuma hakan ya nuna cewa zai biya wa mutane bukatunsu.​—Markus 6:​41-44.

  • Ya juya ruwa ya zama ruwan anab a wurin bikin aure, kuma hakan ya nuna cewa yana so mutane su riƙa shaƙatawa.​—Yohanna 2:​7-11.

Me za ka yi don ka more irin rayuwar da Allah yake shirya ma waɗanda suke ƙaunarsa? Littafi Mai Tsarki ya ce dole ne ka bi “hanyar” rai, kuma ya ce “masu binta . . . ba su da yawa.”​—Matiyu 7:14.

YADDA ZA KA SAMI HANYAR RAI MAFI INGANCI

Mene ne ake nufi da hanyar rai? Hanyar rai tana nufin dukan umurnin da Allah yake ba mu. Allah ya ce: “Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya[ke] koya muku domin amfanin kanku, wanda ya[ke] nuna muku hanyar da za ku bi.” (Ishaya 48:17) Idan mun bi wannan hanyar, za mu sami rayuwa mafi inganci.

Yesu ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai.” (Yohanna 14:6) Sai ta wurin yin imani da abubuwan da Yesu ya koyar, da kuma bin misalinsa ne za mu iya kusantar Allah kuma mu amfani kanmu.

Ta yaya za ka sami hanyar rai? Akwai addinai da yawa, amma Yesu ya ja mana kunne da cewa: “Ba duk mai ce mini ‘Ubangiji, Ubangiji’ ne zai shiga mulkin sama ba. Sai dai wanda ya yi abin da Ubana wanda yake cikin sama yake so.” (Matiyu 7:21) Ƙari ga haka, ya ce: “Za ku gane su ta irin aikinsu.” (Matiyu 7:16) Littafi Mai Tsarki zai iya taimakonka ka gane ko su waye ne suke yin ibada ta gaskiya.​—Yohanna 17:17.

Me zai taimaka maka ka sami hanyar rai? Wajibi ne ka koya game da Wanda ya ba mu rai. Ya kamata ka san ko shi waye ne. Me ne sunansa? Yaya halinsa yake? Me yake yi wa ’yan Adam yanzu? Mene ne yake so mu yi?a

Ba yin aiki, da cin abinci, da wasa, da kuma haihuwa ne kaɗai Allah ya halicci ’yan Adam su riƙa yi ba. An yi mu yadda za mu iya sanin Mahaliccinmu kuma mu zama aminansa. Za mu iya nuna masa cewa muna ƙaunarsa ta wurin yin abin da yake so. Yesu ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya.”​—Yohanna 17:3.

ALLAH YANA KOYA MAKA DON KA ‘AMFANI KANKA’ TA WURIN LITTAFI MAI TSARKI.​—ISHAYA 48:17

ABU NA FARKO DA YA KAMATA KA YI

Mai yiwuwa za mu ga cewa muna bukatar mu yi wasu canje-canje bayan mun koyi abin da Allah yake so. Hakan zai iya zama mana da wuya. Amma a gaskiya, za mu daɗa jin daɗin rayuwa idan muka yi canje-canjen nan. Idan kana so ka sami amsoshi ga wasu tambayoyi game da Allah, Shaidun Jehobah za su iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai a lokaci da kuma wurin da kake so. Ka tuntuɓe mu ta intane a adireshin nan: www.pr418.com/ha.

a See Ka duba Hasumiyar Tsaro, Na 1 2019..

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba