Tsarin Ayyuka na Makon ga 8 Maris
MAKON 8 GA MARIS
Waƙa ta 91
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 1 sakin layi na 6-13
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sama’ila 1 zuwa 4
Na 1: 1 Sama’ila 2:18-29
Na 2: Menene Cocin Kirista? (td 13A)
Na 3: Nassosi Sun Bayyana Ƙaunar Jehobah ga Yara
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 105
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ana Jin Saƙon Littafi Mai Tsarki da Kake Gabatarwa Kuwa? Jawabi daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, daga shafi na 109, sakin layi na 2, zuwa ƙarshen babin.
Minti 20: “Nuna Godiya Domin Kyauta Mafi Girma da Allah Ya Ba Mu.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Bayan sakin layi na 3, ka tattauna shirye-shiryen da ikilisiya ta yi na hidimar fage don rarraba takardar gayyata ta musamman don Tuna Mutuwar Yesu. Ka sa majagaba na ɗan lokaci ya gwada yadda zai gabatar da takardar gayyata. Bayan haka, ka sa ya ambata yadda ya keɓe lokaci don zama majagaba na ɗan lokaci da kuma yadda ya amfana.
Waƙa ta 87