Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Nuwamba: Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? Ku ba da sabuwar mujallar tare da waɗannan mujallun: Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Za Ka Iya Zama Abokin Allah! Disamba: Littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived. Idan akwai yara a gidan, ku ba da littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami. Janairu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! A inda masu gida suke son saƙon, ku ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, kuma ku ƙudurta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani. Fabrairu: Za ku iya ba da littafin nan Asirin Farinciki na Iyali ko Ka Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya.