Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 3/11 p. 3
  • Kai Majagaba na Kullum Ne a Dā?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kai Majagaba na Kullum Ne a Dā?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • “Za Ka Iya Zama Majagaba Mai Kyau!”
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 3/11 p. 3

Kai Majagaba na Kullum Ne a Dā?

1. Wane gata ne mutane da yawa suka more, kuma mene ne yake da muhimmanci wasu ’yan’uwa su yi?

1 A cikin shekaru da yawa, dubban mutane sun more gata mai girma na “koyarwa da yin wa’azi” a matsayin masu hidima na cikakken lokaci. (A. M. 5:42) Amma dai, wasu ’yan’uwa sun daina yin hidimar majagaba don wasu dalilai dabam dabam. Idan kai majagaba na kullum ne a dā, ka bincike yanayinka na yanzu ka ga ko za ka iya sake yin hidimar majagaba na kullum?

2. Me ya sa ya kamata waɗanda majagaba ne a dā su bincike yanayinsu na yanzu?

2 Yanayi na Canjawa: Zai iya zama cewa yanayin da ya sa ka daina yin hidimar majagaba ya canja. Alal misali, idan ka daina yin hidimar majagaba ne don ba ka iya ba da awoyi 90 a wata ba, za ka iya somawa kuma tun da yake yanzu an rage awoyin zuwa 70? Aikinka ko kuma hakkokin iyalinka sun ragu ne tun lokacin da ka daina yin hidimar majagaba? Wata ’yar’uwa da ta daina yin hidimar majagaba don rashin lafiya ta sake somawa sa’ad da take da shekara 89. Ta fi shekara ɗaya da barin asibiti kuma ta ga cewa jikinta zai ƙyale ta ta sake yin hidimar majagaba!

3. Ta yaya waɗanda suke cikin iyali za su haɗa kai don su taimaki wani a cikin iyalinsu ya yi hidimar majagaba?

3 Wataƙila kai ba majagaba ba ne a dā, amma wani a iyalinka ya daina yin hidimar majagaba domin ya kula da wani a cikin iyalin, kamar iyaye tsofaffi. (1 Tim. 5:4, 8) Idan haka ne, shin kai ko wasu a cikin iyalinka za ku iya taimaka wa wani da ya daina yin hidimar majagaba? Zai yi kyau ku tattauna batutuwan tare. (Mis. 15:22) Sa’ad da iyali suka haɗa kai don ɗaya a cikinsu ya yi hidimar majagaba, dukansu za su ji cewa sun ɗauki hidimar da muhimmanci.

4. Me za ka iya yi idan ba ka iya sake yin hidimar majagaba a yanzu kuma ba?

4 Kada ka yi sanyin gwiwa idan yanayinka na yanzu bai ƙyale ka ka sake soma hidimar majagaba ba. Kasancewa a shirye ka yi hakan yana faranta wa Jehobah rai. (2 Kor. 8:12) Ka yi amfani da ilimin da ka samu sa’ad da kai majagaba na kullum ne a hidimarka yanzu. Ka sa muradinka cikin addu’a, kuma ka mai da hankali ga zarafi na daidaita yanayinka. (1 Yoh. 5:14) Wataƙila da shigewar lokaci, Jehobah zai buɗe maka “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” don ka sake moran farin ciki na yin hidimar majagaba!—1 Kor. 16:9.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba