“Za Ka Iya Zama Majagaba Mai Kyau!”
1. Yaya wata ’yar’uwa ta ji game da hidimarta ta majagaba?
1 “Babu wani aiki dabam da zai sa in sami gamsuwa ko albarka ta ruhaniya mai yawa kamar wannan.” In ji Kathe B. Palm. Ta yi shekaru da yawa tana hidimar majagaba daga ɓangare ɗaya na ƙasar Chile, Amirka ta Kudu, zuwa ɗayan ɓangaren. Domin ya yi tunani game da irin rayuwa mai gamsarwa ta waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci, wataƙila wani ya taɓa ce maka: “Za ka iya zama majagaba mai kyau!”
2. Ka bayyana dalilin da ya sa muke samun gamsuwa daga yin ayyukan ruhaniya.
2 Hanyar Rayuwa Mai Gamsarwa: Wanda muke bin misalinsa, Yesu, ya samu wartsakewa ta gaske wajen yin nufin Ubansa. (Yoh. 4:34) Saboda haka, da zuciya ɗaya ne Yesu ya koyar da mabiyinsa cewa ana samun gamsarwa ta ainihi daga yin ayyukan da suka shafi bautar Jehobah. Muna samun gamsuwa idan rayuwarmu tana cike da ayyukan da Jehobah ya amince da su. Ƙari ga hakan, yayin da muka ba da ƙarin lokaci, kuzari, da dukiya don taimaka wa wasu, muna daɗa farin cikinmu.—A. M. 20:31, 35.
3. Wane farin ciki ne za mu iya samu don yin amfani da ƙarin lokaci a hidima?
3 Idan muna ba da lokaci sosai a hidimar fage, za mu samu ƙarin zarafi na shaida farin cikin soma da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Har a inda masu gida ba sa son saƙonmu, za mu iya ganin cewa muna samun mutane sosai a yankinmu yayin da muka ƙware sosai a hidimar fage. Majagaba suna iya yin amfani da ilimi mai zurfi da suka samu daga Makarantar Hidima ta Majagaba da za su iya halarta bayan sun yi hidimar majagaba na shekara ɗaya. (2 Tim. 2:15) Yayin da muke aiki tuƙuru, za mu riƙa shuka iri na gaskiya da za ta yi ’ya’ya a nan gaba.—M. Wa. 11:6.
4. Ya kamata matasa da suka kusan sauke karatu su yi la’akari da me?
4 Matasa: Yayin da kake gab da sauke karatun sakandare, ka yi tunani sosai game da rayuwarka ta nan gaba kuwa? Har yanzu, ayyukan makarantarka ne ke nuna yadda za ka tsara ayyukanka. Yaya za ka yi amfani da wannan lokacin bayan ka kammala makaranta? Maimakon biɗar aiki, me zai hana ka yi tunani tare da addu’a game da zama majagaba na kullum? Gwanintar da za ka koya don yin wa’azi ga mutane daga al’adu dabam-dabam, tangarɗar da za ka sha kansu, samun horon kai, da kuma samun ingancin koyarwa zai amfane ka a rayuwarka gaba ɗaya.
5. Ta yaya iyaye da ikilisiya za su iya ƙarfafa yin hidimar majagaba?
5 Iyaye, kuna cika hakkinku na mai da hankalin yaranku ga biɗar hidima ta cikakken lokaci? Kalamanku da misalinku mai kyau za su taimake su su mai da abubuwan Mulki farko a rayuwarsu. (Mat. 6:33) Ray, wanda ya soma hidimar majagaba sa’ad da yake gab da gama makarantar sakandare, ya tuna: “Mahaifiyana takan ji cewa yin hidimar majagaba tana kai ga samun rayuwa mafi gamsarwa.” Kowa a cikin ikilisiya zai iya ƙarfafa yin hidimar majagaba ta hanyar furcinsu da kuma tallafinsu. Jose, daga ƙasar Spain, ya ce: “Ikilisiyarmu ta ɗauki aikin majagaba a matsayin aiki mafi kyau da matasa za su iya yi. Kalamansu da kuma godiyarsu ga hidimar majagaba tare da taimako mai amfani da suke ba da wa ya sa zama majagaba ya zo mini da sauƙi.”
6. Menene za mu iya yi idan a yanzu ba mu da muradin yin hidimar majagaba?
6 Shawo Kan Tangarɗa: Amma idan fa ka ce, ‘Ba ni da marmarin yin hidimar majagaba.’ Idan yadda ka fara ji ke nan, ka yi addu’a ga Jehobah game da yadda kake ji kuma ka gaya masa, ‘Ban sani ba ko zan iya yin hidimar majagaba, amma ina so in yi abin da zai faranta maka rai.’ (Zab. 62:8; Mis. 23:26) Sai ka nemi ja-gorancinsa ta hanyar Kalmarsa da ƙungiyarsa. Majagaba da yawa sun fara “ɗanɗana” hidimar majagaba ta wajen somawa da hidimar majagaba na ɗan lokaci, kuma farin cikin da suka shaida ya motsa su su biɗi hidima ta cikakken lokaci.—Zab. 34:8.
7. Ta yaya za mu iya shawo kan shakkar cewa za mu iya samun awoyi 70 da ake bukata a kowane wata?
7 Idan ba ka da tabbacin cewa za ka iya samun awoyi 70 da ake bukata a kowane wata fa? Me zai hana ka tattauna da majagaban da suke cikin irin yanayin ka? (Mis. 15:22) Sai ka rubuta tsarin ayyuka masu yawa waɗanda za ka iya yi. Za ka iya ganin cewa samun lokaci daga wasu ayyuka marar amfani saboda hidima yana da sauƙi fiye da yadda kake tsammani.—Afis. 5:15, 16.
8. Me ya sa ya dace mu riƙa bincika yanayinmu a kai a kai?
8 Ka Sake Bincike Yanayin Ka: Yanayin mu yakan canjawa. Yana da kyau ka riƙa sake duba yanayin ka a kai a kai. Alal misali, ka kusan yin ritaya daga wajen aiki? Randy, wanda ya yi ritaya da daɗewa, ya ce: “Wannan zaɓin ya sa na soma hidimar majagaba na kullum tare da matata, kuma ya ba mu zarafin ƙaura zuwa inda ake da bukata sosai. Na samu albarka sosai don zaɓin da na yi, amma albarka mafi girma ita ce lamiri mai kyau.”
9. Ya kamata ma’aurata su yi tunani a kan me?
9 Bayan sun yi tunani sosai, wasu ma’aurata sun ga cewa su biyun ba sa bukatan su riƙa yin aiki na cikakken lokaci. Hakika, wataƙila hakan zai bukaci iyalin su sauƙaƙa salon rayuwarsu, amma kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu. John, wanda matarsa ta bar aikinta na cikakken lokaci kwanan nan don ta faɗaɗa hidimarta, ya ce: “Babu abin da ya fi ba ni farin ciki kamar sanin cewa matata tana yin ayyuka na ruhaniya.”
10. Me ke motsa Kiristoci su yi tunanin yin hidimar majagaba?
10 Alamar Ƙauna da Imani: Jehobah ya sa yin wa’azi ya zama aiki mafi muhimmanci da kowannenmu zai iya yi. Za a halaka wannan tsohon zamani ba da daɗewa ba, kuma waɗanda suke kiran sunan Jehobah ne kaɗai za su tsira. (Rom. 10:13) Zuciyar da ke cike da ƙauna ga Allah da kuma godiya don abin da ya yi mana zai motsa mu mu yi biyayya ga umurnin da Ɗansa ya ba mu na yin wa’azi da ƙwazo. (Mat. 28:19, 20; 1 Yoh. 5:3) Ƙari ga hakan, yin imani da cewa muna rayuwa a zamanin ƙarshe zai motsa mu mu yi iya ƙoƙarinmu a hidima yayin da muke da sauran lokaci, maimakon yin amfani da duniya sosai.—1 Kor. 7:29-31.
11. Idan wani ya ce za mu iya zama majagaba mai kyau, ya ya kamata mu ɗauki hakan?
11 Hidimar majagaba na kullum ta wuce bin tsarin ƙungiyar nan, alama ce ta ibadarmu ga Allah. Saboda haka, idan wani ya gaya maka cewa za ka iya zama majagaba mai kyau, ka ɗauki kalmarsa a matsayin yabo. Kuma ka yi tunani tare da addu’a sosai a kan yin hidima tare da waɗanda suke yin wannan aiki mai gamsarwa.
[Bayanin da ke shafi na 4]
Iyaye, kuna cika hakkinku na mai da hankalin yaranku ga hidima ta cikakken lokaci?
[Bayanin da ke shafi na 5]
Jehobah ya sa yin wa’azi ya zama aiki mafi muhimmanci da kowannenmu zai iya yi.