Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 pp. 27-31
  • Hidimar Majagaba Tana Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hidimar Majagaba Tana Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA HIDIMAR MAJAGABA TAKE ƘARFAFA DANGANTAKARMU DA ALLAH
  • YADDA ZA KA CI GABA DA YIN HIDIMAR MAJAGABA
  • SHIN ZA KA IYA SOMA HIDIMAR MAJAGABA?
  • “Za Ka Iya Zama Majagaba Mai Kyau!”
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Wane Ne Majagaba?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 pp. 27-31

Hidimar Majagaba Tana Ƙarfafa Dangantakarmu Da Allah

“Ya yi kyau a raira yabbai ga Allahnmu.”—ZAB. 147:1.

TAMBAYOYI DON BIMBINI

  • Ta yaya hidimar majagaba za ta iya ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

  • Idan kai majagaba ne, mene ne zai taimaka maka ka ci gaba da hidimar?

  • Idan kuma kai ba majagaba ba ne tukun, me zai taimake ka ka soma hidimar?

1, 2. (a) Mene ne sakamakon yin tunani da kuma magana game da wani da muke ƙauna? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

YIN tunani da kuma magana game da wani da muke ƙauna zai sa dangantakarmu da shi ta daɗa danƙo. Hakan ma dangantakarmu da Jehobah take. Da yake Dauda makiyayi ne, ya kasance a waje daddare sau da yawa, kuma ya rifta wannan zarafin don ya kalli taurari kuma ya yi bimbini a kan ikon Mahaliccinsu. Ya ce: “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; Wane abu ne mutum, da kake tuna da shi? Ɗan Adam kuma da kake ziyartarsa?” (Zab. 8:3, 4) Kuma sa’ad da manzo Bulus ya lura da yadda Jehobah yake cika nufinsa game da Kiristoci shafaffu, ya ce: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!”—Rom. 11:17-26, 33.

2 Muna tunani da kuma magana game da Jehobah sa’ad da muka yi wa’azi kuma hakan yana ƙarfafa dangantakarmu da shi. Majagaba da yawa sun lura cewa sun daɗa ƙaunar Allah domin sun ƙara ƙwazo a wa’azin Mulkin Allah da suke yi. Wannan talifin zai taimaka wa majagaba da kuma waɗanda suke so su soma wannan hidimar su yi bimbini a kan waɗannan tambayoyin: Ta yaya hidimar majagaba za ta iya ƙarfafa dangantakarka da Jehobah? Idan kai majagaba ne, mene ne zai taimaka maka ka ci gaba da hidimar? Idan kuma kai ba majagaba ba ne tukun, me zai taimake ka ka soma hidimar? Bari mu fara tattauna yadda hidimar majagaba za ta iya ƙarfafa dangantakarmu da Allah.

YADDA HIDIMAR MAJAGABA TAKE ƘARFAFA DANGANTAKARMU DA ALLAH

3. Ta yaya tattauna da mutane game da abin da Mulkin Allah zai yi a nan gaba zai iya taimaka mana?

3 Za mu kusaci Jehobah idan muka yi shelar abubuwan da Mulkinsa zai yi a nan gaba. Wane nassi ne ka fi amfani da shi sa’ad da kake wa’azi gida-gida? Wataƙila littafin Zabura 37:10, 11 ko Daniyel 2:44 ko Yohanna 5:28, 29 ko kuma Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 ne. A duk sa’ad da muka tattauna da mutane game da waɗannan alkawuran, muna tuna wa kanmu cewa “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta” daga Allahnmu mai karimci ne, wato Jehobah. Kuma hakan zai sa mu kusaci shi sosai.—Yaƙ. 1:17.

4. Me ya sa muke ƙara fahimtar nagartar Allah sa’ad da muka yi wa mutane wa’azi?

4 Ganin irin yanayin da mutanen da ba su san Allah ba suke ciki zai sa mu daɗa daraja gaskiyar da muka koya. Babu abin da ke taimaka wa mutanen duniya su yi nasara da kuma farin ciki na gaske. Yawancinsu suna alhini a kan abin da zai faru a nan gaba kuma ba su da bege. Ba su san dalilin da ya sa muke raye ba. Yawancin mutane masu ibada ma ba su san Littafi Mai Tsarki sosai ba. Suna kamar mutanen birnin Nineba na dā. (Karanta Yunana 4:11.) Idan muka kwashi sa’o’i da yawa muna yi wa mutane wa’azi, za mu daɗa fahimtar cewa Jehobah yana kula da mu sosai. (Isha. 65:13) Jehobah yana tanadar da bukatun bayinsa, kuma yana ba kowa zarafin samun wartsakewa da kuma bege na gaske. Hakan ya tuna mana cewa Jehobah nagari ne sosai.—R. Yoh. 22:17.

5. Yaya koya wa mutane Kalmar Allah take sa mu ɗauki matsalolinmu?

5 Ba za mu riƙa damuwa da matsalolinmu ba sa’ad da muke koya wa wasu Littafi Mai Tsarki. Wata majagaba mai suna Trisha ta ce ta yi baƙin ciki sosai sa’ad da iyayenta suka kashe aurensu. Ta ce: “Babu abin da ya taɓa sa ni baƙin ciki haka.” Wata rana da take baƙin ciki sosai kuma ta ji kamar ta zauna a gida, sai ta yi ƙoƙari ta je yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu yara uku da suke fuskantar matsaloli a gida. Mahaifinsu ya yasar da su kuma yayansu ya ci zarafinsu. Trisha ta ce: “Ba za a iya gwada matsalolin da nake fuskanta da nasu ba. Yayin da muke nazarin, sun fahimci abin da muka tattauna kuma sun yi farin ciki sosai. Waɗannan yaran baiwa ne daga Jehobah, musamman ma a wannan ranar.”

6, 7. (a) Ta yaya koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki take ƙarfafa bangaskiyarmu? (b) Yaya muke ji sa’ad da muka ga yadda ɗalibanmu suke amfana daga bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

6 Koyar da Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa bangaskiyarmu. Manzo Bulus ya yi magana game da wasu Yahudawa a zamaninsa da suka ƙi yin abin da suke wa’azinsa. Ya ce: “Kai fa mai-koya wa wani, ba ka koya wa kanka ba?” (Rom. 2:21) Majagaba a yau suna samun zarafi da yawa na koya wa mutane gaskiya da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Idan suna son su yi hakan sosai, ya kamata su fara koyar da kansu. Wajibi ne su shirya kowane nazarin da za su yi kuma su nemi amsoshin tambayoyin. Wata majagaba mai suna Janeen ta ce: “A duk lokacin da na sami zarafin koya wa mutane Kalmar Allah, bangaskiyata tana daɗa ƙarfi.”

7 Za mu daraja hikimar Allah sosai sa’ad da muka ga cewa ɗalibanmu suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Isha. 48:17, 18) Hakan yana sa mu so yin amfani da ƙa’idodin a rayuwarmu. Wata majagaba kuma mai suna Adrianna ta ce: “Idan mutane suka dogara ga hikimarsu, ba za su yi nasara ba. Amma idan suka dogara ga hikimar Allah, za su shaida amfaninta nan da nan.” Hakazalika, wani majagaba mai suna Phil ya ce: “Ina mamaki sosai yadda Jehobah yake taimaka wa mutane su canja salon rayuwarsu.”

8. Ta yaya yin wa’azi tare da ’yan’uwanmu yake taimaka mana?

8 Yin wa’azi tare da ’yan’uwanmu yana ƙarfafa mu. (Mis. 13:20) Yawancin majagaba suna wa’azi na sa’o’i da yawa tare da ’yan’uwansu. Hakan yana ba su ƙarin zarafin ‘ƙarfafa’ juna. (Rom. 1:12; karanta Misalai 27:17.) Wata majagaba mai suna Lisa ta ce: “Mutane suna yawan gasa da kuma kishin juna a wurin aiki. Suna gulma da kuma zagi kullum. Kowa dai ya fi so ya fi wani samun matsayi. A wasu lokatai ma, mutane suna yi maka ba’a da kuma dariya saboda imaninka. Amma dai, yin wa’azi tare da ’yan’uwanka yana kawo kwanciyar rai ainun. Ko da na gaji tikis don na yi wa’azi, ina dawowa gida cike da farin ciki.”

9. Ta yaya yin hidimar majagaba tare yake taimaka wa ma’aurata?

9 Yin hidimar majagaba a matsayin ma’aurata yana ƙarfafa aure. (M. Wa. 4:12) Wata mai suna Madeline da take hidimar majagaba tare da mijinta ta ce: “Ni da maigidana muna samun isashen lokacin tattauna abubuwan da suka faru sa’ad da muke wa’azi ko kuma wani abu da muka koya a karatun Littafi Mai Tsarki da za mu iya amfani da shi a wa’azi. Muna kusantar juna sosai a duk shekarar da muka yi hidimar majagaba tare.” Hakazalika, Trisha wadda aka ambata ɗazun, ta ce: “Ni da maigidana mun tsai da shawara cewa ba za mu ci bashi ba.” Mene ne sakamakon haka? Ta ce: “Ba ma faɗa a kan kuɗi. Muna ziyarar mutanen da muka yi wa wa’azi kuma muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Hakan yana sa dangantakarmu ta daɗa ƙarfi sosai.”

10. Ta yaya saka al’amuran Mulkin Allah farko da kuma shaida taimakon Jehobah suke sa mu dogara gare shi?

10 Za mu ƙara dogara ga Jehobah sa’ad da muka saka hidimarsa farko, muka samu taimakonsa kuma ya amsa addu’o’inmu. Gaskiya ne cewa dukan Kiristoci amintattu suna dogara ga Jehobah. Amma majagaba sun san cewa dogara ga Jehobah ne kawai zai taimaka musu su ci gaba da wannan hidimar. (Karanta Matta 6:30-34.) Wani majagaba wanda wakilin mai kula da da’ira ne mai suna Curt, ya yarda ya ziyarci wata ikilisiyar da ake yin tafiyar sa’o’i biyu da minti talatin kafin a kai ta. Shi da matarsa wadda ita ma majagaba ce ba su da isashen māi a motar da za su tuƙa zuwa wurin, kuma sauran mako guda kafin a biya su albashi. Curt ya ce: “Na soma tunani ko na tsai da shawara mai kyau.” Bayan sun yi addu’a, sai suka amince cewa za su je wurin kuma sun yi imani cewa Jehobah zai kula da su. Sa’ad da suke gab da barin gida, wata ’yar’uwa ta ce tana da kyautar da take son ta ba su. Daidai kuɗin da suke bukata su yi tafiya da shi ne ta ba su. Curt ya ce: “Sa’ad da ka shaida irin wannan yanayin sau da yawa, za ka fahimci cewa Jehobah yana biyan bukatun bayinsa.”

11. Waɗanne albarka ne masu yin hidimar majagaba suke samu?

11 Majagaba suna yawan cewa idan sun kusaci Allah kuma sun daɗa ƙwazo a hidimarsa, suna samun albarka sosai. (K. Sha 28:2) Amma, hidimar majagaba ba cin tuwo ba ne domin tana ɗauke da nata ƙalubale. Babu ɗan Adam da ba ya shan wahala saboda ajizancinmu da kuma muguwar duniyar nan. A wasu lokatai, matsaloli suna sa majagaba ya daina hidimarsa na ɗan lokaci. Amma, za a iya magance ko kuma hana matsalolin faruwa. Mene ne zai iya taimaka wa majagaba ya ci gaba da yin hidimarsa?

YADDA ZA KA CI GABA DA YIN HIDIMAR MAJAGABA

12, 13. (a) Me ya kamata majagaban da ba ya iya samun sa’o’in da ake bukata a gare shi ya yi? (b) Me ya sa keɓe lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki kullum da yin nazari mu kaɗai da kuma bimbini suke da muhimmanci?

12 Yawancin majagaba suna shagala da ayyuka dabam-dabam. A sakamako, yana kasance musu da wuya su yi dukan abubuwan da suke so. Saboda haka, ya kamata su kasance da tsari. (1 Kor. 14:33, 40) Idan ba ya kasance wa wani majagaba da sauƙi ya cika sa’o’in da ake bukata a gare shi, ya kamata ya yi tunani a kan yadda yake amfani da lokacinsa. (Afis. 5:15, 16) Zai iya tambayar kansa: ‘Shin nishaɗi ne yake cinye lokacina? Zan iya canja tsarin ayyukana kuwa? Shin abubuwan da ba su da amfani suna cinye lokacina?’ Majagaba suna bukatar su yi wa kansu waɗannan tambayoyin a kai a kai kuma su yi gyara idan da bukata.

13 Wajibi ne majagaba ya keɓe lokacin da zai riƙa karanta Littafi Mai Tsarki, ya yi nazari shi kaɗai kuma ya yi bimbini a kai a kai. Ya kamata ya tabbata cewa abubuwa da ba su da muhimmanci sosai ba su cinye lokacinsa ba. (Filib. 1:10) Alal misali, a ce majagaba ya dawo gida bayan ya yi sa’o’i da yawa yana wa’azi kuma yana so ya yi shiri don taron da za a yi a makon. Amma da farko, ya karanta saƙon da aka aika masa. Bayan haka, sai ya kunna kwamfutarsa kuma ya karanta da amsa saƙon imel ɗinsa. Bayan ya gama aika saƙon, sai ya shiga Intane don ya binciko farashin wani abin da yake son ya saya. Kafin ya ankara, sa’o’i biyu sun riga sun wuce kuma bai soma shirya abubuwan da za a tattauna a taro ba tukun. Me ya sa hakan matsala ce sosai? Idan ɗan wasa yana son ya cim ma burinsa sosai, wajibi ne ya riƙa cin abinci mai gina jiki. Hakazalika, majagaba yana bukatar ya riƙa yin nazari shi kaɗai a kai a kai don ya kyautata ibadarsa kuma ya ci gaba da yin hidimarsa.—1 Tim. 4:16.

14, 15. (a) Me ya sa ya kamata majagaba su sauƙaƙa salon rayuwarsu? (b) Me ya kamata majagaba ya yi sa’ad da yake fuskantar matsaloli?

14 Ya kamata majagaban da suke son su yi nasara a hidimarsu su sauƙaƙa salon rayuwarsu. Abin da Yesu ya ƙarfafa almajiransa su yi ke nan. (Mat. 6:22) Yesu ya kasance da salon rayuwa mai sauƙi don kada kome ya raba hankalinsa daga hidimarsa. Shi ya sa ya ce: “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sama kuma suna da sheƙuna; amma Ɗan mutum ba shi da wurin da za ya kwanta.” (Mat. 8:20) Majagaban da suke yin koyi da Yesu ba sa manta cewa idan suna da abubuwan mallaka da yawa, za su bukaci ƙarin lokaci don su adana da kuma gyara su.

15 Majagaba sun san cewa suna hidima ta musamman, amma hakan ba ya nufin cewa sun fi wasu ’yan’uwa muhimmanci. Maimakon haka, suna ɗaukan hidimar a matsayin baiwa daga Jehobah. Saboda haka, wajibi ne su dogara ga Jehobah don su yi nasara a hidimarsu. (Filib. 4:13, Littafi Mai Tsarki) Za su riƙa fuskantar matsaloli da kuma ƙalubale. (Zab. 34:19) Amma sa’ad da hakan ya faru, za su iya neman taimakon Jehobah kuma su bi ja-gorarsa, maimakon yin hanzarin daina hidimar da suke yi. (Karanta Zabura 37:5.) Yayin da suke ganin yadda Jehobah yake kula da su kuma yake ƙaunarsu, dangantakarsu da shi za ta daɗa danƙo.—Isha. 41:10.

SHIN ZA KA IYA SOMA HIDIMAR MAJAGABA?

16. Mene ne ya kamata ka yi idan kana so ka soma hidimar majagaba?

16 Idan kana son ka yi hidimar majagaba kuma ka sami albarka da wasu majagaba suke samu, ka yi addu’a ga Jehobah game da batun. (1 Yoh. 5:14, 15) Ka tattauna da waɗanda suke hidimar majagaba. Ka kafa wa kanka maƙasudan da za su taimaka maka ka soma hidimar majagaba. Abin da Keith da Erika suka yi ke nan. Kamar sauran ma’aurata, Keith da Erika suna aiki tuƙuru kuma sun sayi sabon gida da kuma mota bayan sun yi aure. Sun ce: “Mun yi zato cewa waɗannan abubuwan za su sa mu farin ciki. Amma ba abin da ya faru ke nan ba.” Sa’ad da aka kore shi daga aiki, sai ya soma hidimar majagaba na ɗan lokaci. Ya ce: “Yin hidimar majagaba ya tuna mini irin farin cikin da mutum yake yi don yin wa’azi.” Sun zama abokan wasu ma’aurata da suke hidimar majagaba, kuma sun taimaka musu su san cewa idan sun sauƙaƙa salon rayuwarsu kuma sun soma hidimar majagaba, za su yi farin ciki sosai. Wace shawara ce Keith da Erika suka yanke? Sun rubuta jerin maƙasudan da suke son su cim ma kuma sun manna takardar a jikin firijinsu. Idan suka cim ma wani maƙasudin, sai su sa alama a kai. Hakan ya sa daga baya, suka soma hidimar majagaba.

17. Me ya sa ya dace mu yi tunani sosai ko zai yiwu mu soma hidimar majagaba?

17 Shin za ka iya zama majagaba kuwa? Idan hakan ba zai yiwu ba a wannan lokacin, ka yi iya ƙoƙarinka don ka kusaci Jehobah ta wajen yin ƙwazo sosai a hidima. Idan ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka yi la’akari sosai da yanayinka, za ka iya ganin cewa kana bukatar ka yi wasu canje-canje a salon rayuwarka don ka yi hidimar majagaba. Idan ka soma hidimar majagaba, ba za ka riƙa damuwa don sadaukarwa da ka yi ba, amma za ka yi farin ciki sosai. Za ka yi farin ciki domin kana saka Mulkin Allah farko a rayuwarka kuma kana saka bukatun wasu gaba da naka. (Mat. 6:33) Za ka sami ƙarin zarafin yin tunani da kuma tattauna da mutane game da Jehobah. A sakamako, za ka daɗa ƙaunar Jehobah kuma ka faranta masa rai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba