Rahotannin Wa’azi
Muna farin cikin sanar da sabon ƙolin masu shela 330,316 da suka ba da rahoton wa’azi a watan Agusta. Wannan hanya ce mai kyau ta kammala shekarar hidimarmu ta 2011. Kowanne mai shela ya yi wa’azi na aƙalla abirejin sa’o’i 11.3 kuma ya gudanar aƙalla abirejin nazarin Littafi Mai Tsarki 1.5. Kuma mutane 12,687 ne suka yi baftisma a shekarar hidimar da ta gabata. Hanya ɗaya da za mu nuna godiya don albarkar da Jehobah ya yi wa ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu ita ce ta ci gaba da sanar wa mutane game da Mulkin Allah da kuma koma ziyara wurin masu son saƙonmu.—Zab. 116:12-14.