Ayyuka na Makon 5 ga Maris
MAKON 5 GA MARIS
Waƙa ta 103 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 145 zuwa 147 da akwati (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Irmiya 1-4 (minti 10)
Na 1: Irmiya 3:14-25 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Abin da Ya Sa Muke Ɗauke da Sunan Jehobah da Alfahari—Isha. 43:12 (minti 5)
Na 3: Ba Dukan Mutane Ba Ne Suke Bauta wa Allah Ɗaya—td 23D (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 94
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ka Amfana Daga Ƙasidar Examining the Scriptures Daily—2012. Ka ɗan ba da jawabi a kan gabatarwa na ƙasidar. Ka gayyaci masu sauraro su faɗi lokacin da suka keɓe don tattauna nassin yini da kuma yadda suka amfana. Ka kammala ta wajen tattauna jigon shekara ta 2012.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Maris. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don ka gabatar da wasu talifofi da mutane a yankinku za su so. Ta wajen yin amfani da talifin da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro, ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayar da za su yi da za ta sa mai-gidan ya so mujallar, kuma su faɗi nassin da za a iya karanta. Ka yi hakan da talifin bangon gaba na Awake! kuma idan da lokaci ka yi hakan da wani talifi da ke cikin mujallun. Ka sa a yi gwajin yadda za a gabatar da kowacce mujallar.
Waƙa ta 75 da Addu’a