Tsarin Ayyuka na Makon 15 ga Oktoba
MAKON 15 GA OKTOBA
Waƙa ta 101 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 254 sakin layi na 9 zuwa shafi na 257 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Daniyel 10-12 (minti 10)
Na 1: Daniyel 11:15-27 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Kiristoci Ba Sa Ramako—Rom. 12:18-21 (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Yesu Ya Iya Fanshe Mu—td 17B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 106
Minti 10: Idan Wani Ya Ce: ‘Ba Ni da Marmari.’ Tattaunawa da aka ɗauko daga ƙasidar nan, Yadda Za a Soma Kuma Cigaba da Mahawwarai na Littafi Mai-Tsarki, shafi na 8 zuwa shafi na 9. Ka tattauna da masu sauraro bisa da gabatarwar da ke waɗannan shafuffukan da kuma wasu gabatarwa da ake amfani da su a yankin. Ka sa a yi ’yan gwaji guda biyu.
Minti 20: “Ku Yi Amfani da Warƙa a Yin Shelar Bishara.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 5, ka ɗan yi magana a kan warƙar da za a ba da a watan Nuwamba kuma ka sa a gwada yadda za a yi hakan. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 7, ka sa a gwada yadda za a yi amfani da warƙa wajen yin wa’azi a duk lokacin da aka samu zarafi.
Waƙa ta 97 da Addu’a