Abubuwa Biyar da Za Su Taimaka Mana Mu Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane
1. Idan muna samun matsala wajen soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a yankinmu, mene ne ya kamata mu yi, kuma me ya sa?
1 Yana muku wuya ne ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane? Idan haka ne, kada ku karaya. Jehobah yana yi wa waɗanda suka ci gaba da yin nufinsa albarka. (Gal. 6:9) Ga wasu abubuwa biyar da za su taimaka muku ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.
2. Wace tambaya ce za mu iya yi kai tsaye don mu soma nazari da mutane?
2 Ku Tambayi Mutane Kai Tsaye: Mutane da yawa sun san cewa muna rarraba Hasumiyar Tsaro da Awake!, amma ba su san ko muna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ba. Saboda haka, zai dace ku tambayi mutane kai tsaye. Za ku iya tambayar waɗanda kuka yi musu wa’azi ko za su so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Idan ba su yarda ba, kada ku karaya. Ku ci gaba da ba su mujallu kuma ku riƙa ƙarfafa su ko wata rana za su amince a yi nazari da su. Wani ɗan’uwa ya yi shekaru yana ba wasu ma’aurata mujallunmu. Wata rana, sa’ad da ya kai musu mujallun kuma ya juya zai tafi sai ya tambaye su: “Za ku so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ku?” Suka ce e. Abin ya ba shi mamaki don bai yi tsammani cewa za su yarda ba. A yanzu haka, su Shaidun Jehobah ne.
3. Dukan mutane da suke halartar taronmu ne ake nazarin Littafi Mai Tsarki da su? Ka bayyana.
3 Ku Tambayi Waɗanda Suke Halartan Taro: Kada ku aza cewa ana nazarin Littafi Mai Tsarki da dukan waɗanda suke son saƙonmu da suke zuwa taronmu. Wani ɗan’uwa ya ce: “Yawancin mutanen da nake nazari da su na same su ne a taronmu, sa’an nan na tambaye su ko za su so a yi nazari da su kuma suka amince.” A ƙarshen taro a wani ikilisiya, wata ’yar’uwa ta tambayi wata mata da ta halarci taron ko za ta so a yi nazari da ita. Wannan matar tana da yara huɗu da suka yi baftisma kuma suna ikilisiyar. Ƙari ga haka, ta yi shekara 15 tana halartar taro. Matar takan shiga Majami’ar Mulki da zarar an fara taro kuma idan an gama taro, sai ta tafi ba tare da ɓata lokaci ba. Matar ta amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma yanzu ita Mashaidiyar Jehobah ce. ’Yar’uwar ta ce: “Ina baƙin ciki cewa na jira sai bayan shekara 15 kafin na tambaye ta ko za ta so in yi nazari da ita.”
4. Ta yaya ɗalibanmu ko waɗanda muke ba wa mujallu za su iya taimaka mana mu sami wani da za mu yi nazari da shi?
4 Ku Nemi Bayani Daga Wasu: Wata ’yar’uwa takan bi wasu sa’ad da suke zuwa nazarin littafi tsarki da ɗalibansu. Da izinin mai nazarin, sai ta tambayi ɗalibar ko ta san wata da za ta so a yi nazari da ita. Sa’ad da kake ziyartar wani da kuke tattaunawa da shi kuma kana son ka gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, za ka iya tambayarsa: “Ka san wani da zai so ya karanta irin wannan littafin?” A wani lokaci, majagaba da masu shela ba sa iya yin nazari da wani da suka yi wa wa’azi don wasu dalilai. Saboda haka, zai dace ku gaya wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya cewa kuna neman waɗanda za ku soma nazari da su.
5. Me ya sa zai dace mu tambayi mutanen da matarsu ko mijinsu mashaidi ne ko za su so a yi nazari da su?
5 ’Yan’uwa da Matarsu Ko Mijinsu Ba Mashaidi Ba Ne: Akwai ’yan’uwa a cikin ikilisiyarku da matar ko mijin ba Mashaidi ba? Alal misali, idan wani yana da mata wadda Mashaidiya ce, ba zai so ya tattauna batun Littafi Mai Tsarki da ita ba, amma zai iya yarda ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wani ɗan’uwa. Saboda haka, zai dace ku tattauna da Mashaidiyar kafin ku yi magana da maigidanta, don ku san yadda za ku soma tattaunawa da shi.
6. Mene ne muhimmancin yin addu’a sa’ad da kuke neman ɗalibin da za ku yi nazari da shi?
6 Addu’a: Kada ku manta cewa yin addu’a game da wannan batun yana da muhimmanci sosai. (Yaƙ. 5:16) Jehobah ya yi alkawari cewa zai amsa addu’o’inmu idan sun jitu da nufinsa. (1 Yoh. 5:14) Wani ɗan’uwa da ba ya da ɗalibin da zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi saboda cewa aiki ya yi masa yawa, ya yi addu’a Allah ya ba shi wanda zai yi nazari da shi. Matarsa kuma ta damu don tana ganin cewa ba zai sami zarafi na gudanar da nazari da mutane ba, musamman ma idan ɗalibin yana da matsaloli da yawa. Saboda haka, ta yi addu’a game da yanayin maigidanta kuma ta roƙi Jehobah ya ba wa maigidan ɗalibin da zai iya yin nazari da shi. Makonni biyu bayan haka, wata majagaba a ikilisiyarsu ta sami wani mutumin da yake son ya yi nazari sai ta ce maigidan matar ya soma nazari da mutumin. Hakika, Jehobah ya amsa addu’arta. Matar ta rubuta cewa: “Ga abin da nake son in gaya wa duk wani wanda yana ganin ba zai iya yin nazari da wasu ba: Ku faɗi ainihin abin da kuke so sa’ad da kuke yin addu’a kuma kada ku fasa yin addu’a sai Jehobah ya amsa addu’ar. Jehobah ya amsa addu’armu fiye da yadda muka yi zato.” Idan kun dāge, ku ma za ku iya samun ɗalibai da za ku yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma ku more farin cikin da ke tattare da taimaka wa mutane su shiga ‘hanya wadda ta nufa wajen rai.’—Mat. 7:13, 14.