Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/12 pp. 5-6
  • Yadda Za Ku Amfana Daga Rukuninku na Wa’azi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ku Amfana Daga Rukuninku na Wa’azi
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Taron Fita Wa’azi da Ke Cim ma Manufarsu
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 10/12 pp. 5-6

Yadda Za Ku Amfana Daga Rukuninku na Wa’azi

1. Waɗanne abubuwa ne aka mora a Taron Nazarin Littafi na Ikilisiya da har yanzu ana tanadarwa ta Rukuninmu na fita wa’azi?

1 Kuna kewar wasu sassa na Taron Nazarin Littafi na Ikilisiya da ake yi dā can? ’Yan’uwa da ke rukunin a lokacin ba su da yawa kuma suna jin daɗin kasancewa tare. Hakan ya sa mun ƙulla abuta da ’yan’uwa kuma mun ƙarfafa imaninmu. (Mis. 18:24) Kari ga haka, hakan ya ba mai kula da rukunin zarafin sanin yanayin kowannenmu da kuma ƙarfafamu yadda ya dace. (Mis. 27:23; 1 Bit. 5:2, 3) Ko da yake, an daina gudanar da Nazarin Littafi na Ikilisiya, muna morar waɗannan abubuwan a Rukuninmu na fita wa’azi.

2. Da yake muna samun ƙarfafa daga rukuninmu na wa’azi, wane mataki za mu ɗauka don mu ƙulla abuta da ’yan’uwa da ke rukunin?

2 Ku Ɗauki Mataki: An tsara ’yan’uwa cikin ƙananan rukunoni na fita wa’azi kamar yadda aka tsara rukunonin nazarin littafi na ikilisiya a dā. Ta wajen yin wa’azi “tare” da ’yan’uwa dabam-dabam da ke cikin rukuninmu, za mu ƙulla abota mai kyau da su. (Filib. 1:27, Littafi Mai Tsarki) Mutane nawa ne cikin rukuninku ka taɓa yin wa’azi tare da su? To, idan ba ka taɓa yin hakan ba, ka yi ƙoƙari ka ‘buɗe zuciyarka’ ta wajen yin wa’azi tare da ’yan’uwa dabam-dabam. (2 Kor. 6:13) Ƙari ga haka, a lokaci-lokaci, za mu iya gayyatar wani daga rukuninmu zuwa gidanmu don mu yi Bauta ta Iyali ko kuma mu ci abinci tare don mu ƙarfafa juna. Kuma, a duk lokacin da aka gayyaci wani ɗan’uwa ya zo ya ba da jawabi a cikin ikilisiyarmu, rukunin fita wa’azi da suka ba da kai za su iya ɗaukan nauyin tanadar da abinci wa ɗan’uwan. A makon da baƙon ya ziyarci ikilisiyar, rukunin za su taru don su ci abinci tare kuma su ƙarfafa juna ko da baƙon ya zo cin abincin ko a’a.

3. Wace dama ce kuke da ita na samun ziyarar ƙarfafa a rukuninku na fita wa’azi?

3 Ko da yake a yanzu, ikilisiyoyi suna taro sau biyu ne kawai a mako, hakan ba ya nufin cewa ba za a yi wa masu shela ziyarar ƙarfafa da ya kamata ba. An naɗa masu kula da rukunoni don su riƙa ƙarfafa kowanne ɗan’uwa a cikin rukuninsu kuma su horar da su a yin wa’azi. Idan ba ka taɓa yin wa’azi tare da mai kula da rukuninku ba, kana iya tambayarsa ko za ku iya hakan tare. Ƙari ga haka, mai kula da hidima yana bin rukuni-rukuni don ya fita wa’azi tare da su sau ɗaya a wata a ƙarshen mako. A ƙananan ikilisiyoyi da babu rukunin fita wa’azi da yawa, yana iya fita wa’azi da kowanne rukuni sau biyu a shekara. Shin, kana tsara ayyukanka yadda za ka sami zarafi don ka fita wa’azi tare da shi sa’ad da ya ziyarci rukuninku?

4. (a) Yaya ake tsara taron fita wa’azi? (b) Me ya sa zai dace mu yarda a yi amfani da gidanmu don a riƙa gudanar da taron fita wa’azi a ciki?

4 Yana da kyau duka rukunonin fita wa’azi su haɗu a wurare dabam-dabam sa’ad da suke fita wa’azi a ƙarshen mako. Idan kowane rukuni yana da wurin taron fita wa’azi, hakan zai taimaka wa ’yan’uwa su hallara da wuri kuma su tafi yankin da za a yi wa’azin ba tare da wata matsala ba. Ƙari ga haka, yin hakan zai taimaka a tsara masu shela da ke rukunin da sauri don su kama hanya zuwa yankin ba tare da ɓata lokaci ba. Kuma zai yi wa mai kula da rukunin sauƙi ya kula da waɗanda suke cikin rukuninsa. Amma a wani lokaci, zai fi dacewa rukunoni biyu ko sama da hakan su yi taron fita wa’azi tare saboda wani yanayi. Idan dukan masu shela sun haɗu don su yi taron fita wa’azi tare a Asabar ta farko a wata, ko kuma bayan Nazarin Hasumiyar Tsaro, zai dace kowane rukuni su zauna tare kuma a ba wa mai kula da rukunin ɗan lokaci don ya rarraba ’yan’uwa da ke rukuninsa don wa’azi kafin a kammala.—Ku duba akwatin nan “Za Ka Yarda a Yi Amfani da Gidanka?”

5. Ko da yake an daina tsarin Nazarin Littafi na Ikilisiya, wane tabbaci ne muke da shi?

5 Ko da yake an daina taron Nazarin Littafi na Ikilisiya, Jehobah zai ci gaba da yi mana tanadin dukan abubuwan da muke bukata don mu ƙarfafa imaninmu. (Ibran. 13:20, 21) Ba za mu rasa kome ba domin Jehobah yana kula da mu. (Zab. 23:1) Muna samun albarka da yawa daga rukuninmu na fita wa’azi. Idan muka ɗauki mataki don mu “shuka da yalwa,” za mu girbe “da yalwa.”—2 Kor. 9:6.

[Akwati a shafi na 6]

Za Ka Yarda a Yi Amfani da Gidanka?

Wasu rukunoni da dama suna yin taron fita wa’azi tare a ƙarshen mako don babu gidaje da yawa da za a yi taron a ciki. Taron fita wa’azi sashen bautarmu ne, saboda haka, gata ne mai girma mu ba da gidajenmu don a yi taro a ciki. Za ku iya yin hakan? Kada ku yi jinkirin yin hakan don kuna ganin cewa gidanku ba zai dace a gudanar da taron fita wa’azi ciki ba. Dattawa za su iya duba wurin da gidanka yake da wasu abubuwa da suka yi la’akari da su a dā can da suke zaɓan gidajen aka gudanar da taron nazarin littafi a cikinsu. Idan kana so a yi amfani da gidanka, ka gaya wa mai kula da rukuninku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba