Taron Fita Wa’azi da Ke Cim ma Manufarsu
1. Don me ake shirya taron fita wa’azi?
1 Akwai wani lokaci da Yesu ya yi taro da almajiransa 70 kafin su fita wa’azi. (Luk. 10:1-11) Ya ƙarfafa su ta wajen tuna musu cewa “Ubangijin Girbi,” wato Jehobah zai kasance tare da su kuma zai yi musu ja-gora. Ya kuma ba su umurni da suka shirya su don wa’azin kuma ya aika su “biyu biyu.” Hakazalika, taron da muke yi a yau kafin mu fita wa’azi yana cim ma wannan manufar, wato yana ƙarfafa da tsara da kuma shirya mu don wa’azi.
2. Mintoci nawa ne ya kamata a yi taron fita wa’azi?
2 An saba amfani da minti 10 zuwa 15 ana gudanar da taron fita wa’azi kuma a cikin lokacin ne ake tsara ’yan’uwa, a ba su yankin da za su yi wa’azi kuma a yi addu’a. Yanzu muna so mu canja wannan tsarin. Daga watan Afrilu, taron fita wa’azi zai ɗauki minti 5 zuwa 7 kacal. Amma, kada tsawon wannan taron ya kai hakan idan zai biyo bayan taron ikilisiya tun da ’yan’uwa sun riga sun saurari jawaban Littafi Mai Tsarki. Yin gajeren taron fita wa’azi zai taimaki kowa ya yi wa’azi na sa’o’i da yawa. Ƙari ga haka, idan majagaba ko masu shela sun riga sun soma wa’azi kafin wannan taron, ba zai dace a katse musu wa’azi na tsawon lokaci ba.
3. A wace hanya ce za a iya shirya taron fita wa’azi don masu shela su amfana sosai?
3 Ya kamata a shirya taron fita wa’azi a hanyar da za ta taimaki masu shela sosai. A wasu ikilisiyoyi, zai fi dacewa kowane rukuni ya yi nasa taron fita wa’azi maimakon ikilisiyar ta haɗu a wuri ɗaya. Mai yiwuwa hakan zai kasance da sauƙi wa masu shela su isa wurin taron da kuma yankin da za su yi wa’azi. Hakan zai sa a tsara waɗanda za su fita wa’azi da sauri kuma zai yi wa dattijon da ke kula da rukunin sauƙi ya kula da ’yan rukuninsa. Rukunin dattawa su yi la’akari da yankinsu kuma su zaɓi abin da ya fi dacewa da su. Dukan masu shela su san yankin da za su yi wa’azi da ’yan’uwan da za su yi wa’azin tare kafin a rufe taron da addu’a.
4. Me ya sa bai kamata mu ɗauki taron ikilisiya da daraja fiye da taron fita wa’azi ba?
4 Muhimmancinsa Ɗaya Ne da Sauran Taron Ikilisiya: Ba dukan masu shela ne za su halarci taron fita wa’azi ba, tun da an shirya taron ne domin ’yan’uwan da suke so su fita wa’azi. Amma, hakan ba ya nufin cewa wannan taron bai kai sauran taron ikilisiya muhimmanci ba. Taron fita wa’azi da kuma sauran taron ikilisiya tanadi ne daga Jehobah don mu sami damar ƙarfafa juna. (Ibran. 10:24, 25) Saboda haka, mai gudanar da taron ya shirya sosai domin tattaunawar ta daraja Jehobah kuma ’yan’uwan da suka halarta su amfana. Idan zai yiwu, masu shela da za su fita wa’azi su yi ƙoƙari su halarci wannan taron.
Bai kamata mu ɗauka cewa taron fita wa’azi bai kai sauran taron ikilisiya muhimmanci ba
5. (a) Mene ne ya kamata mai kula da hidima ya yi a batun tsara taron fita wa’azi? (b) Yaya ya kamata ’yar’uwa ta gudanar da taron fita wa’azi?
5 Shirin da Mai Gudanar da Taron Zai Yi: Idan ɗan’uwa yana da jawabi, ana sanar da shi da sauri domin ya shirya jawabin da kyau. Ya kamata a riƙa yin hakan ma a taron fita wa’azi. Idan kowane rukuni ne zai yi nasa taron fita wa’azi, dattijo mai kula da rukunin ko mataimakinsa ya gudanar da taron. Amma, idan ikilisiyar baƙi ɗaya za ta yi taron fita wa’azi tare, mai kula da hidima zai zaɓi ɗan’uwan da zai gudanar da taron. Wasu masu kula da hidima suna ba da tsarin ayyuka na wa’azi ga dukan ’yan’uwan da suke gudanar da taron kuma su manna shi a allon sanarwa. Ya kamata mai kula da hidima ya nuna sanin yakamata sa’ad da yake zaɓan ’yan’uwan da za su gudanar da taron kuma ya tuna cewa idan ya zaɓi ’yan’uwan da suke da tsari kuma sun iya koyarwa sosai, hakan zai shafi yadda za a gudanar da taron. Idan akwai ranar da babu wani dattijo ko bawa mai hidima ko ɗan’uwan da ya yi baftisma da zai fita wa’azi, mai kula da hidima ya zaɓi wata ’yar’uwa da ta yi baftisma kuma ta ƙware don ta gudanar da wannan taron.—Ka duba talifin nan “Idan Ya Zama Dole ’Yar’uwa Ta Gudanar da Taron.”
6. Me ya sa ya kamata ɗan’uwan da zai gudanar da taron ya yi shiri tun da wuri?
6 Sa’ad da aka ba mu aiki a Makarantar Hidima ta Allah ko Taron Hidima, muna ɗaukansa da muhimmanci kuma muna yin shiri sosai. Ba ma jira sai muna kan hanyar zuwa taro kafin mu soma shirya yadda za mu ba da jawabin. Hakan ma ya kamata masu gudanar da taron fita wa’azi su ɗauki taron. Yanzu da za a rage yawan lokacin da ake gudanar da taron, yin shiri sosai zai taimaka don kada a ci lokaci kuma taron ya kasance da ban ƙarfafa. Sanin yankin da za a yi wa’azi tun da wuri zai taimaka sosai.
7. Waɗanne irin batutuwa ne mai gudanar da taron zai iya tattaunawa?
7 Abin da Za A Iya Tattaunawa: Bawa mai-aminci, mai-hikima ba ya ba da awutlayin abin da za a tattauna a kowane taron fita wa’azi domin kowane yanki yana da nasa yanayin. Talifin nan mai jigo “Sa’ad da Kuke Taron Fita Wa’azi, Za Ku Iya Tattauna” yana ɗauke da jerin batutuwan da za mu iya tattaunawa. A yawancin lokatai, za a ba masu sauraro dama su yi magana sa’ad da ake gudanar da taron. Amma a wasu lokatai, za a yi gwaji ko kuma a nuna wani bidiyo game da wa’azi daga dandalin jw.org/ha. Idan mai gudanar da taron yana yin shiri, ya nemi batutuwan da za su ƙarfafa ’yan’uwa kuma sa su kasance a shirye don yin wa’azi a ranar.
Idan mai gudanar da taron yana yin shiri, ya nemi batutuwan da za su ƙarfafa ’yan’uwa kuma sa su kasance a shirye don yin wa’azi a ranar
8. Mene ne zai fi dacewa a tattauna a taron fita wa’azi a ranakun Asabar da Lahadi?
8 Yawancin masu shela suna ba da Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! a ranar Asabar. ’Yan’uwa da yawa da suke fita wa’azi a ranar Asabar ba sa fita a tsakiyar mako, a sakamakon hakan, zai iya zama musu da wuya su tuna gabatarwa da suka koya a lokacin Ibadarsu ta Iyali da yamma. Saboda haka, za su amfana idan mai gudanar da taron fita wa’azi ya maimaita gabatarwa da ke bayan Hidimarmu ta Mulki. Wani abu kuma da zai iya tattauna shi ne abin da za a gaya wa maigida don ya yi marmarin ziyararmu ta gaba, ko kuma yadda za a iya amfani da wani labari ko biki ko abin da ya faru a yankin wajen yin wa’azi. Idan wasu a rukunin sun riga sun soma amfani da mujallun da ake ba wa mutane a watan, mai gudanar da taron ya ce su faɗi gabatarwar da suka yi amfani da shi ko kuma su ba da wani labarin wa’azi. A ranar Lahadi ma mai gudanar da taron fita wa’azi zai iya bin wannan salon game da littattafan da muke ba mutane a watan. A kowane lokaci, za mu iya ba mutane littattafan da muke amfani da su wajen yin nazari, kamar su Albishiri Daga Allah! ko Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada ko kuma Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Mai gudanar da taron zai iya tattauna yadda za mu ba da waɗannan littattafan.
9. Mene ne za a iya tattauna a ƙarshen mako idan ana wani kamfen na musamman?
9 Idan ikilisiyar tana yin wani kamfen a ƙarshen mako, mai gudanar da taron zai iya tattauna yadda za a ba da warƙar ko takardar gayyata tare da sababbin mujallu, ko kuma ya faɗi abin da za a yi idan maigida yana so a tattauna da shi. Ban da wannan, zai iya ba da wani labarin da zai nuna muhimmancin kamfen ɗin.
10, 11. Wane sakamako ne za a samu idan ’yan’uwa suka yi shiri sosai don taron fita wa’azi?
10 Yadda Masu Shela Za Su Shirya: Masu shela ma za su iya sa taron fita wa’azi ya zama da ban ƙarfafa sosai. Idan suka yi shiri da kyau mai yiwuwa sa’ad da suke ibada ta iyali, za su san abin da za su faɗa da zai ƙarfafa ’yan’uwa. Karɓan littattafan da za mu yi amfani da su tun kafin mu je wajen taron zai sa mu soma wa’azi da wuri ba tare da ɓata lokaci ba.
11 Yana da kyau mu shirya yadda za mu isa wurin taron kafin a soma. Hakika, ya kamata mu riƙa halartan dukan taron ikilisiya da wuri. Amma yana da muhimmanci sosai mu isa taron fita wa’azi da wuri don kome ya tafi sumul. Me ya sa muka ce hakan? Ɗan’uwan da ke gudanar da taron yana la’akari da abubuwa da dama kafin ya tsara rukunin. Idan masu shela da suke wurin ba su da yawa, yana iya ce kowa ya je ya yi wa’azi a yankin da an soma amma ba a gama ba. Idan wasu sun taka ne zuwa wurin taron kuma inda za a yi wa’azi yana da nisa, yana iya ce su tafi tare da masu shela da suke da mota. Idan babu tsaro sosai a yankin da za su yi wa’azi, zai iya ce ’yan’uwa maza su yi wa’azi tare da ’yan’uwa mata ko kuma su kasance a rukuni ɗaya. Za a iya sa tsofaffi ko naƙasassu su yi wa’azi a yankin da babu tuddai ko kuma gidajen da babu hawa sosai. Masu shela da ba su daɗe da soma wa’azi ba za su iya tafiya da waɗanda suka ƙware. Amma idan masu shela sun makara, mai gudanar da taron zai sake yin gyara ga shirin da ya riga ya yi. Akwai wasu lokuta da za mu makara don wata ƙwaƙƙwarar dalili, amma idan hakan ya zama jikinmu, zai dace mu tambayi kanmu ko muna yin hakan ne domin ba mu daraja taron fita wa’azi ba ko kuma ba mu da tsari sosai.
12. Me ya kamata ka yi la’akari da shi idan ka saba yin naka shirin fita wa’azi?
12 Masu shela da suka halarci taron fita wa’azi za su iya zaɓan ’yan’uwan da suke so su fita wa’azi tare ko kuma mai gudanar da taron zai ba su. Idan kai ne kake yawan zaɓan wanda za ku fita wa’azi tare, zai dace ka zaɓi masu shela dabam-dabam maimakon abokanka kawai a kowane lokaci. (2 Kor. 6:11-13) A wasu lokuta, za ka iya yin wa’azi tare da wani mai shela da bai daɗe da soma wa’azi ba don ka taimaka masa ya ƙware. (1 Kor. 10:24; 1 Tim. 4:13, 15) Ka saurara da kyau sa’ad da mai gudanar da taron yake ba da umurni haɗe da umurni game da inda za ku yi wa’azin. Sa’ad da aka kammala taron, kada ka soma yin wasu canje-canje kuma ka nufi yankin ba tare da ɓata lokaci ba.
13. Wane amfani ne za mu samu idan kowane ɗan’uwa yana da ƙwazo kuma ya cika hakkinsa?
13 Bayan almajirai 70 da Yesu ya tura yin wa’azi sun kammala, sun “komo da farin zuciya.” (Luk. 10:17) Babu shakka, taron da Yesu ya yi da su kafin su fita wa’azi ya taimaka musu su sami sakamako mai kyau. A yau ma, taron fita wa’azi zai iya sa a sami irin wannan sakamakon. Idan kowane ɗan’uwa yana da ƙwazo kuma ya cika hakkinsa, taron fita wa’azi zai kasance da ban ƙarfafa, zai tsara mu kuma ya shirya mu don mu ba da “shaida ga dukan al’ummai.”—Mat. 24:14.