Ba Za a Ƙara Tattauna Nassosin Yini a Taron Fita Hidimar Fage Kuma Ba
A dā, waɗanda suke gudanar da taron fita hidimar fage suna ɗan tattauna nassosin yini idan yana magana a kan hidima. An yi gyara a wannan. Ba za a ƙara yin amfani da ƙasidar nan Examining the Scriptures Daily [Bincika Nassosin Yini] don tattaunawa a tarurrukan fita hidimar fage ba. Kamar yadda ake yi a dā, masu gudanar da taron za su iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki, Hidimarmu Ta Mulki, littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, Reasoning From The Scriptures, da wasu littattafai da suka yi magana a kan hidima. Waɗanda aka sa su gudanar da taron su yi shirin ba da shawara mai kyau da za ta taimaki waɗanda za su fita hidima a ranar. Kamar yadda yake a dā, taron ba zai wuce minti 10 zuwa 15 ba, kuma za a gajertar da shi idan za a yi hakan bayan taron ikilisiya.