Tsarin Ayyuka na Makon 30 ga Maris
MAKON 30 GA MARIS
Waƙa ta 57 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 22 sakin layi na 9-17 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sama’ila 14-15 (minti 8)
Na 1: 1 Sama’ila 14:36-45 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Koyon Harshe Mai Tsarki da Kuma Yinsa Ya Ƙunsa?—Zaf. 3:9 (minti 5)
Na 3: Yadda Annabcin Littafi Mai Tsarki Game da Kwanaki na Ƙarshe Yake Cika—igw 13 sakin layi na 1 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: ‘Ku Zama Shiryayyu don Kowane Kyakkyawan Aiki.’—Tit. 3:1.
Waƙa ta 37
Minti 15: Ƙarin Bidiyoyi a Dandalinmu don Wa’azi. Tattaunawa. Ka soma da nuna bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? Bayan haka, ka tattauna yadda za a yi amfani da wannan bidiyon a wa’azi. Ka yi hakan ma da bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? Ka sa a yi gwaji.
Minti 15: “Ku Yi Amfani da ‘Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah’ don Soma Tattaunawa da Mutane.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka ba masu sauraro dama su faɗi wasu hanyoyi da za a iya yin amfani da “Abubuwa da Za Mu Iya Koya Daga Kalmar Allah” a wa’azi. Ka sa a yi gwaji.
Waƙa ta 114 da Addu’a