Ku Yi Amfani da “Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah” don Soma Tattaunawa da Mutane
1. Wace sabuwar ƙasida ce za ta iya taimaka mana a wa’azi?
1 Yaya za mu iya yin amfani da sabuwar ƙasidar nan Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah sa’ad da muke shirin fita wa’azi? Tun da yake ƙasidar tana da nassosi dabam-dabam da ke bayyana kowane batu a Littafi Mai Tsarki, za ta taimaka sosai don soma tattaunawa da mutane.
2. Yaya za mu iya yin amfani da sabuwar ƙasidar nan a wa’azi?
2 Za ka iya amfani da tambaya ta 8 kuma ka ce: “Muna yi wa maƙwabtanmu wannan tambayar, ‘Kana ganin Allah ne yake jawo wa ’yan Adam wahala?’ [A wasu yankuna, zai dace a nuna wa maigidan tambayar.] Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa mai gamsarwa ga wannan tambayar.” Ka karanta kuma ka tattauna nassi ɗaya ko fiye da haka da aka rubuta a wurin. Idan maigidan ya saurara, za ka iya nuna masa tambayoyi 20 da ke cikin ƙasidar kuma ka ce ya zaɓi ɗaya da zai so ku tattauna idan ka sake dawowa. Ko kuma ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari da mutane da ke ɗauke da abin da kuka tattauna.
3. Yaya za mu yi amfani da sabuwar ƙasidar nan don soma tattaunawa a yankunan da mutane ba Kiristoci ba ne?
3 Tambayoyi na 4 da 13 zuwa 17 za su taimaka sa’ad da muke wa’azi a yankunan da mutanen ba Kiristoci ba ne. Alal misali, za ka iya yin amfani da tambaya ta 17 kuma ka ce: “Muna tattaunawa da iyalai. Ka yarda cewa iyalai suna fuskantar matsaloli da yawa a yau? [Ka bari ya ba da amsa.] Iyalai da yawa sun amfana daga wannan shawara cewa: “Matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” [Ba ka bukatar ka ambata cewa ka ɗauko shawarar daga Afisawa 5:33. Idan kana magana da mace ce, za ka iya maimaita Afisawa 5:28.] Kana gani iyalai za su amfana idan suka bi wannan shawara?
4. Mene ne za ka iya yi sa’ad da ka gama tattaunawa da mutumin da ba Kirista ba ne?
4 Sa’ad da kuka kammala tattaunawar, ka gaya wa maigidan cewa za ka sake dawowa don ku ci gaba da tattaunawa. Za ka iya gaya masa cewa in ka dawo za ku tattauna ɗayan nassin da ke ƙarƙashin tambayar. A lokacin da ya dace, ka gaya wa maigidan cewa abubuwan da kuke tattaunawa daga cikin Littafi Mai Tsarki ne. Za ka iya ba shi mujallar da kake ganin ta dace da shi bisa ga abin da kuka tattauna ko kuma ra’ayin mutumin game da Littafi Mai Tsarki.—Ka duba ’yar ciki na Hidimarmu ta Mulki ta Disamba, 2013.