Sanarwa
◼ Littattafan da za a ba da a watan Oktoba: Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da kuke koma ziyara, ku gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, idan sun dace da mutumin, kuma ku ƙoƙarta ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Nuwamba da Disamba: Ku yi amfani da warƙoƙi da kuke da su a cikin ikilisiya. Idan mutumin yana son saƙon da ya ji daga Littafi Mai Tsarki, ku nuna masa yadda muke nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada. Janairu: Ku yi amfani da ɗaya daga cikin waɗannan ƙasidun da ke gaba: Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada ko kuma Za Ka Iya Zama Abokin Allah! kuma ku ƙoƙarta ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Sa’ad da kuke koma ziyara, ku gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun da ya dace da mutumin.