Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Nuwamba
“A ganin mutane da yawa a yau, Yesu jariri ne ko kuma mutumi ne da aka rataye a gungumen azaba shekaru dubu biyu da suka shige. Amma a ganinka, mene ne matsayin Yesu a yanzu? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka duba abin da aka ce a nan.” Ka ba mutumin Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba, kuma ku tattauna ƙaramin jigo na farko da ke shafi na 18 tare, sa’an nan ka karanta aƙalla nassi ɗaya. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Oktoba-Disamba
“Ga wani nassi mai ban sha’awa da za mu so mu tattauna da kai. [Karanta Irmiya 31:34.] Shin, wannan yana nufin cewa Allah Maɗaukakin Sarki ba zai iya tuna laifuffukan da ya yafe mana ba? Za ka sami amsar a shafi na 26 na wannan mujallar.”
Awake! Nuwamba
“Muna ziyarar ku ne domin muna son mu taimaka wa Iyali. Iyalan da mahaifi ko mahaifiya ce kaɗai ke kula da su sun zama ruwan dare a yau. Shin kana ganin suna fuskantar matsaloli ne fiye da iyalai waɗanda mahaifi da mahaifiyarsu na tare da su? [Ka bari ya ba da amsa.] Ƙa’idodi masu amfani da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun taimaka wa iyaye da yawa su jure waɗannan ƙalubalen. [Ka karanta 2 Timotawus 3:16.] Wannan mujallar tana ɗauke da wasu shawarwari da za su taimaka wa iyalan da mahaifi ko mahaifiya ce kaɗai ke kula da su.”