Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Agusta
“Mutane da yawa sun gaskata cewa duniya kasuwa ce. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batun.” Ka ba shi kofi ɗin Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba kuma ku tattauna talifin da ke ƙarƙashin tambaya ta farko a shafi na 16 da kuma aƙalla nassi guda da ke cikin mujallar. Ka ba da mujallar, kuma ka yi shirin koma ziyara don tattauna tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba
“Talauci yana cikin matsalolin da ’yan Adam suke fuskanta. Kana tsammani cewa lokaci na zuwa da talauci ba zai kasance kuma ba? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Luka 4:16-18.] Nassosi sun ba da bishara ga matalauta. Mene ne wannan bisharar? Wannan talifin da ya soma daga shafi na 7 ya amsa tambayar.”
Awake! Agusta
“Ina son na san ra’ayinka game da wannan ayar. [Karanta 1 Sama’ila 16:23.] Wannan ayar ta nuna cewa kiɗa tana da iko. Kana ganin zai yiwu wasu waƙoƙi su kasance da rinjaya marar kyau? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan mujallar ta tattauna yadda za mu iya yin zaɓi mai kyau game da kiɗa da kuma yadda za mu taimaka wa yaranmu su yi hakan.”