Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Agusta
“Kana ganin addini yana sa mutane su kasance da ƙauna kuma su yi zaman lafiya, ko kuwa yana haddasa ƙiyayya da tashin hankali? [Ka bari ya ba da amsa.] Bari in nuna maka wani abu mai ƙayatarwa game da wannan batun.” Ka ba shi Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba sai ku tattauna tambaya ta farko da ke shafi na 24 da kuma aƙalla nassi ɗaya a kan batun. Ka ba da mujallar, kuma ka yi shirin koma ziyara don ku tattauna tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba
“Muna tattaunawa ne da mutane game da wani hali da zai sa mutane su ƙaunace ka, wato, tawali’u. Abin baƙin ciki shi ne, mutane da yawa a yau ba su da tawali’u. Kana ganin Jehobah Allah ne mai tawali’u? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. [Ka karanta Zabura 18:35, NW.] Talifin da ke shafi na 22 a wannan mujallar ya tattauna yadda za mu amfana idan muka yi koyi da halin Jehobah na tawali’u.”
Awake! Agusta
“A yau mutane suna tsoron fita yawo su kaɗai, musamman ma da dare saboda rashin imani da ya zama ruwan dare. Kana ganin akwai abin da za a yi don a rage nuna rashin imani a wannan duniya? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan mujallar ta tattauna wasu abubuwan da kowannenmu zai iya yi don mu yi zaman lafiya da juna. Ta kuma tattauna yadda wannan annabci mai ban ƙarfafa zai cika.” Ka karanta Zabura 72:7.