Yadda Za a Gabatar
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Mayu
“Ka taɓa tunani ko wane ne Yesu Kristi? [Ka bari ya ba da amsa.] Zan so na nuna maka wani abu mai burgewa a kan wannan batun.” Ku karanta talifin da ke ƙarƙashin kan magana na farko da ke shafi na 22 a talifin Hasumiyar Tsaro ta Afrilu-Yuni da kuma nassi guda da aka yi ƙaulinsa. Ka gabatar da mujallar, kuma ka shirya don ka dawo ka ba da amsa ga tambayar da ke gaba.
Afrilu-Yuni
“Ka taɓa tunani ko wane ne Yesu Kristi? [Ka bari ya ba da amsa.] Zan so na nuna maka wani abu mai burgewa a kan wannan batun.” Ku karanta talifin da ke ƙarƙashin kan magana na farko da ke shafi na 24 a talifin Hasumiyar Tsaro ta Afrilu-Yuni da kuma nassi guda da aka yi ƙaulinsa. Ka gabatar da mujallar, kuma ka shirya don ka dawo ka ba da amsa ga tambayar da ke gaba.
Mayu
“Wasu mutane sun ce ’yan Adam dabbobi ne da suka rikiɗa. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Zabura 139:14.] Hakika, marubucin zabura bai da cikakken ilimi game da abin ban mamaki na jikin ’yan Adam. Wannan mujallar ta tattauna abin da muka sani, haɗe da abin da ya bambanta mu da dabbobi.”