Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/11 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Yadda Za a Gabatar
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 6/11 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Yuli

“Ka taɓa tunanin dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta da wahala kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Zan so in nuna maka wani abu mai ban sha’awa a kan wannan batun. Ka karanta talifin da ke ƙarƙashin kan magana na farko a shafi na 16 na Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba da kuma ɗaya cikin nassosin da aka yi ƙaulinsa. Ka ba da mujallun, kuma ka shirya koma ziyara wurinsa don tattauna amsa ga tambaya ta gaba.”

Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba

“Da yawa cikinmu muna ƙoƙari don samun abin biyan bukata na yini kuma wasu mutane ba sa ma samu. Kana tsammani cewa za a taɓa yin lokaci da talauci ba zai kasance kuma ba? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Zabura 9:18.] Wannan mujallar ta bayyana dalilin da ya sa ake talauci da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda za a yi maganin wannan matsalar.”

Awake! Yuli

Ka ambata wani bala’in da ya faru kwanan nan. Sai ka ce: “Me kake tsammani ne ya sa Allah yake ƙyale irin waɗannan abubuwan su faru? [Ka bari ya ba da amsa.] Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, Allah yana da juyayi ga waɗanda suke shan wahala. [Karanta Fitowa 3:7.] Littafi Mai Tsarki ya kuma gaya mana dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala kuma ya ce ba da daɗewa ba Zai sa wahala ta daina har abada. Wannan mujallar ta ba da waɗannan bayanan.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba