Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Yuli
“Kusan kowa yana so a yi zaman lafiya a duniya. Amma duk da haka, ana fama da yaƙe-yaƙe. Shin a ganinka, me ya sa aka kasa samun zaman lafiya a duniya?” Ka bari ya ba da amsa. Ka nuna masa talifin da ke bangon baya na Hasumiyar Tsaro na Yuli-Agusta. Ku tattauna sakin layi na ɗaya da kuma aƙalla nassi ɗaya daga cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba mutumin mujallun, kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna tambaya da ke biye.
Abin lura: A gwada wannan gabatarwa sa’ad da ake taron fita wa’azi a ranar 6 ga Yuli.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Agusta
“Muna ziyartar mutane a wannan unguwa don tattauna wata matsala da ta shafi kowa. Yawancin mutane sun taɓa fuskantar wani yanayi da aka nuna musu bambanci. Shin kana ganin akwai inda ba a nuna bambanci a duniya? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da yadda Allah yake ɗaukan mutane. [Ka karanta Ayyukan Manzanni 10:34.] Wannan mujallar ta tattauna yadda Allah zai kawo ƙarshen nuna bambanci gaba ɗaya.”
Awake! Yuli
“Muna ziyartar maƙwabtanmu don mu tattauna wata matsala da take ci wa mutane tuwo a ƙwarya, wato, rashin adalci. Wasu suna ƙoƙarin magance rashin adalci ta yin zanga-zanga. Kana ganin waɗanda suke zanga-zangar suna sa a sami canjin da ake bukata? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai tabbatar da ingantaccen canji a duniya. [Ka karanta Matta 6:9, 10.] Wannan mujallar ta ba da amsar tambayar nan, Yin zanga-zanga zai magance matsaloli ne?”
Albishiri Daga Allah!
“Muna ziyartar iyalai a unguwarku don mu tattauna wani abu mai ban ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki da su. Mutane da yawa da muka tattauna da su suna mamakin dalilin da ya sa Allah mai ƙauna ya ƙyale shan wahala sosai a duniya. Kana ganin Allah ya halicce mu don mu riƙa shan wahala kawai?” Ka bari ya ba da amsa. Ka buɗe darasi na 5 a ƙasidar, ka karanta kuma ka tattauna sakin layi na ɗaya da na biyu da kuma ayoyin da aka ce a karanta. Ka ba da mujallar, kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambaya ta gaba.