Gabatarwa
Don Soma Nazari da Mutane a Asabar ta Farko a Watan Yuli
“Muna ziyarar mutane ne don mu ɗan tattauna wata tambaya. [Ka nuna masa tambaya ta farko a shafin ƙarshe na Hasumiyar Tsaro ta Yuli–Agusta.] Mece ce amsarka?” Ka bari ya ba da amsa. Ku tattauna bayanin da ke ƙarƙashin tambayar da kuma aƙalla ɗaya daga cikin nassosin. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli–Agusta
“Mun kawo muku ziyara ne don mun lura cewa mutane da yawa suna so su san yadda nan gaba zai kasance. Yaya kake ji sa’ad da ka yi tunanin yadda abubuwa za su kasance nan gaba? Kana kasancewa da gaba gaɗi ne ko kuma kana damuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sa’an nan ka karanta ɗaya daga cikin nassosin da ke akwatin nan “Abin da Allah Ya Bayyana Game da Nan Gaba” da ke shafi na 7.] Wannan mujallar ta lissafa wasu abubuwan da Allah ya ce za su faru kuma ta bayyana dalilan da za su taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa za su faru.”
Awake! Yuli
“Ko ba jima ko ba daɗe, kowane mutum yana iya fuskantar matsaloli kamar su bala’i ko rashin lafiya mai tsanani ko kuma mutuwar wani danginsa. Sa’ad da hakan ya faru, kana ganin yana da muhimmanci mutum ya kasance da ra’ayi mai kyau kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa sun gano cewa Littafi Mai Tsarki yana da ban taimako sa’ad da mutum yake cikin mawuyacin hali. [Karanta Romawa 15:4.] Wannan mujallar ta bayyana yadda Kalmar Allah za ta iya taimaka mana sa’ad da muke cikin mawuyacin hali.”