Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Janairu-Maris
“Mutane suna fuskantar matsaloli da yawa a yau. Kana tsammani cewa akwai wanda ya fahimci yadda muke ji sosai? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da aka bayyana a nan. [Karanta 2 Labarbaru 6:30.] Waɗannan kalaman suna da ban ƙarfafa! Wannan talifin ya tattauna yadda za mu iya samun ƙarfafa daga wannan Nassin.” Ka gabatar da talifin da ke shafi na 11.
Maris
Idan ka sadu da matashi, ka nuna talifin da ya soma daga shafi na 26. Ka nuna masa kan magana na farko sai kuma ka tambaye shi, “Kana ganin waɗannan kalaman gaskiya ne ko ƙarya? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta 2 Korintiyawa 7:1.] Wannan talifin ya tattauna abubuwan da muke bukata mu sani game da shan sigari, haɗe da yadda za mu daina yin hakan.”
Afrilu-Yuni
“Kana tsammani cewa zai yiwu a san yadda Allah yake kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ina da abu mai kyau a kan wannan batun.” Ka karanta kuma ka tattauna batun da ke ƙarƙashin tambaya na biyu a shafi na 16 da kuma ɗaya daga cikin nassosi da aka yi ƙaulinsa. Ka gabatar da mujallun, kuma ka shirya ka koma don tattauna batun da ke ƙarƙashin tambaya ta 3.
Afrilu
“Shin ka amince cewa rashin wani ƙaunatacce a mutuwa ɗaya daga cikin abubuwa mafi wuya da ’yan Adam za su iya fuskanta ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa sun amfana daga wannan shawarar. [Karanta Zabura 55:22.] Wannan Mujallar ta tattauna hanyoyi masu amfani da za mu iya jimre da baƙin ciki, haɗe da yadda za mu miƙa nawayarmu ga Allah.”