Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Janairu-Maris
“Wasu mutane suna tunanin cewa dokokin Allah suna da wuyan bi. Menene ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Kubawar Shari’a 30:11, 16.] Wannan talifin zai taimaka maka ka fahimci cewa abubuwan da Allah yake bukata suna da amfani kuma za mu iya cika su.” Ka gabatar da talifin da ke shafi na 20.
Fabrairu
“Wasu sun amince da Mahalicci, wasu kuma suna jin cewa wannan imanin bai jitu da ilimin kimiyya ba kuma ba shi da kan gado. Yaya kake ji? [Ka bari ya ba da amsa.] Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, imani na gaske yana bisa tabbaci. [Karanta Ibraniyawa 11:1.] Wannan talifin ya bayyana wasu tabbacin da suka nuna cewa akwai Mahalicci.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 22.
Janairu-Maris
“Wasu ba sa samun farin ciki a aurensu. Menene kake tunanin cewa ya jawo hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Kamar dai mutane da yawa ba sa ɗaukan aure a matsayin gami mai tsarki. [Karanta Matta 19:4-6.] Wannan talifin da ya soma a shafi na 26 ya tattauna abin da zai iya taimaka wa iyalai su kasance da farin ciki.”
Maris
“Kamar mutane da yawa, babu shakka kana yin sha’awar kyaun halitta. Za ka amince cewa halitta yana bayyana hikima kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Zabura 104:24.] Wannan mujallar ta ba da misalai masu kyau game da zanen da ke cikin halitta kuma ta bayyana darassin da za mu iya koya.”