Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Afrilu-Yuni
“A yau duniya tana cike da matsaloli da yawa. A ganinka, menene kawai kake ganin zai iya magance waɗannan matsalolin? [Ka bari ya ba da amsa.] Dubi abin da Yesu ya ce a wannan Nassin. [Karanta Matta 6:9, 10.] Menene Mulkin zai yi a duniya? An amsa wannan tambayar a kan maganar da ke shafi na 9 na wannan mujallar.”
Mayu
“Kana ganin cewa tattalin arziki zai daɗa kyau a nan gaba kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa ba su san yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana a irin waɗannan lokatan wahala ba. [Ka karanta nassin da ke talifin.] Wannan talifin ya nuna yadda shawarar Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu jimre a lokacin da tattalin arziki yake taɓarɓarewa.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 18.
Afrilu-Yuni
“Babu wanda ya taɓa ganin Allah. Amma kana ganin za mu iya sanin kowanene Allah? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Luka 10:22.] Ɗansa, Yesu, ya yi shekaru masu ɗimbin yawa tare da Allah. Saboda haka, zai iya gaya mana abubuwa da yawa game da shi. An shirya wannan talifin da ya soma daga shafi na 6 ne don ya taimaka maka ka san abin da Yesu ya koyar game da Allah.”
Yuni
“Kamar dai rayuwa tana daɗa kasancewa da damuwa. Ka amince da haka kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa suna ganin cewa waɗannan kalmomin sun bayyana dalili ɗaya da ke jawo wannan damuwar. [Karanta 2 Timotawus 3:1.] Wannan mujallar ta tattauna yadda damuwa take shafarmu. Ta kuma ba da wasu shawarwari game da yadda za mu iya rage yin damuwa.”